Abu huɗu da suka jawo guguwar fasa ɗakunan kayan abinci a Najeriya

Asalin hoton, OTHERS
- Marubuci, Imam Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- An wallafa
Jim kadan bayan kawo ƙarshen zanga-zangar nuna adawa da zaluncin da ake zargin jami'an 'yan sanda na yi a Najeriya, wani batu da ya sake kunno kai shi ne yadda wasu matasa ke kutsa wa ɗakunan ajiyar abinci na gwamnati suna wawashe abubuwan da aka jibge a ciki.
Yayin da gwamnatocin jihohin da lamarin ya faru ke cewa sun adana kayayyakin ne, jama'ar gari na cewa boye su aka yi, dalilin kenan da ya sanya suka fusata domin karbar abin da suke ganin hakkinsu ne a matsayinsu na ;yan kasar.
Rahotanni sun ambato yadda irin wannan al'amari ya faru a jihohi da dama, kama daga kan na kudanci da zanga-zangar End SARS da kuma wadanda ba'a yi ba, dalilin kenan da yasa hukumomi daukar matakai daban-daban domin shawo kan lamarin.
Ana danganta abubuwan da ke faruwa da tunzurar da jama'a suka yi sakamakon zanga-zangar da aka kwashe tsawon makwanni ana yi a wasu jihohi.
Wasu daga cikin irin kayayyakin da aka jibge a irin waɗannan gidaje sun haɗar da nau'ukan abinci iri-iri da aka tanada don raba wa mutanen da annobar korona ta fi shafa, wasu na gwamnatin tarayya ne da ta raba wa jihohi, wasu kuwa jihohin ne suka tara ta hanyar karɓar gudummawa daga masu hannu da shuni da masu sha'awar taimaka wa jama'a.

Asalin hoton, Matasa yayin da suke kwashe kayan abinci
Abin da yawancin matasan da ke irin wannan ƙundumbala ta wawashe kayan da aka tanada a gidajen ajiyar abinci na gwamnati ke cewa shi ne me yasa za a boye abinci alhalin na jama'a ne?
Ga shi kuma an yi nisa a cikin wannan annoba da aka tanadi kayan dominta, sannan an ƙi raba wa mutane har yanzu?
Ita dai gwamnati a nata ɓangaren na kallon hakan a matsayin laifi, sai dai wasu na ganin cewa al'amarin na ƙara fito da halin ƙunci da takura da jama'a ke ciki, lamarin da a yanzu ya fara muni har ta kai sun fara ɗaukar wannan mataki domin su ci su rayu.
Fargabar da ake da ita a yanzu ita ce idan ba a ɗauki mataki ba, watakila masu irin wannan ɗabi'a za su koma kan kayan jama'a da zarar sun gama da na gwamnati.
Ga dai wasu dalilai huɗu da masu sharhi ke ganin sun taka rawa wajen guguwar da ta kawo fasa ɗakunan kayan abinci a Najeriyar.

Talauci
Talauci ya ƙaru a Najeriya kamar yadda rahotanni daban-daban suka nunar, ita kanta gwamnatin kasar ta amince da haka, ta sha neman afuwar jama'a tare da yin alƙawarin cewa abubuwa za su daidaita nan da ɗan wani lokaci.
Karuwar farashin kayan masarufi da kara farashin litar man fetur ta janyo sauye sauye da dama, wasu na ganin cewa wannan hali da ake ciki ya taimaka matuka gaya wajen faruwar irin wannan al'amari
Kwamared Kabiru Sa'idu Dakata wani ɗan gwagwarmaya ne, kana mai sharhi kan al'amuran da suka shafi al'umma, ya ce ba dai-dai ba ne gwamnati ta ɓoye abincin da aka raba wa jama'a musamman lokacin da aka shiga kulle, amma a ajiye su alhalin ga halin da mutane ke ciki na buƙata, kuma an san jama'a ba za su kasa sanin cewa akwai su ba.
''Gwamnatin tarayya ta sanar a hukumance, cewa ta bada wannan tallafi, wasu ma kungiyoyin kasashen duniya ne suka bayar, jama'a sun samu labari, amma sai aka yi shiru ba'a raba su ba''in ji Comrade Kabiru Dakata, dan gwagwarmaya mai sharhi kan al'amuran yau da kullum.
Ya ce matsawar mutane na ganin cewa gwamnati ta ɓoye tare da hana su haƙƙinsu alhalin cin yau da na gobe na gagararsu babu abin da zai hana su daukar wannan mataki, duk da cewa hakan ba dai-dai ba ne.

Rashin yarda tsakanin al'umma da gwamnati
Wasu rahotanni sun nuna cewa kayan abincin sun jima a ajiye, wasu jihohin ma sun ce suna fargabar cewa mutanen da suka kwashe suna iya gamuwa da cututtuka domin har lokacin amfaninsu ya wuce.
Irin wannan na iya kawo rashin yarda tsakanin jama'a da kuma hukumomi, domin zargin da mutum zai iya shi a nan shi ne me yasa ba a raba su ba har aka bari suka lalace?
''Ɓoye kayan abinci da wasu jihohi suka yi, ya nuna cewa ba mahaifina ne ke da laifi a taɓarɓarewar al'amura ba'' in ji Zahra Buhari, ɗiyar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Wasu mutane a shafukan sada zumunta na kallon kalaman a matsayin ƙoƙarin wanke kai daga zargin da ka iya biyo baya, sai dai wasu na ganin cewa rijiya ce ta bayar da ruwa guga ya hana.

Ɓata gari
Hukumomi na cewa matasan da ke wawushe kayan ɓata gari ne, sai dai wasu rahotanni sun nuna cewa yawancinsu jama'ar gari ne da ke rayuwa a inda rumbunan ajiyar suke.
Hotunan yadda lamarin ya faru a wasu wurare sun nuna yawancin mutanen masu iyali ne, da kuma yara ƙanana da ma dattawa, baya ga hoton wani mai lalurar naƙasa da aka dasawa ƙafa da shi ma ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta.
Ba abin mamaki ba ne idan gwamnati na danganta su da ɓata gari, duba da cewa lamarin na zuwa ne jim kadan bayan kammala lalata gine-ginen gwamnati da kuma kwashe kayan jama'a a wasu jihohi da zanga-zangar End SARS ta rikiɗe ta zama tashin hankali a cikinsu.
Sannan ba abin mamaki ba ne idan zanga-zangar ta taimaka wajen fusata jama'a domin ƙwatar abin da suke ganin cewa hakkinsu ne duk da cewa a baya ba a ga hakan ta faru ba

Taɓarbarewar tsaro
Wasu masu sharhi na cewa matsalar rashin tsaron da ake fama da shi a wasu sassan ƙasar da ya jefa mutane cikin halin ha'ula'i na raba su bda muhallansu da mayar da su ƴan gudun hijira, ya taka rawa wajen sa wasu su zama cikin masu rububin abincin.
A hannu guda kuma ga duk wanda ya ji irin abubuwan da ke faruwa a baya-bayan na abin da zai zo masa shi ne ina jami'an tsaron da aka ajiye domin gadin irin wadannan wurare?
Bayanai sun nuna cewa ba shakka a kan ajiye jami'an tsaro domin kula da waɗannan kayayyakin abinci amma a wasu wurare da dama da irin hakan ta faru yawan mutanen da ke wawashe kayan abincin ya kai intaha har ya sa jami'an tsaron suka dinga roƙon jama'a da su yi a hankali ban da turereniya, kamar yadda aka gani a wasu bidiyon.
Ga kuma fargabar kada garin hana mutane ɗibar kayayyakin a samu asarar rai, irin abin da ya faru a baya na zanga-zanga ya sake maimaita kansa.
To sai dai duk da haka, jami'an tsaron na cewa suna daukar matakan sake tsaurara tsaro a gidajen domin tabbatar da kare kayayyakin gwamnati
Jihohi da dama sun lashi takobin gano mutanen da suka wawashe kayayyakin tare da daukar mataki a kansu.
Jihohin da lamarin ya auku

Asalin hoton, OTHERS
Kaduna
A jihar Kaduna an samu rahoton cewa wasu matasa sun kunna kai wani gidan ajiyar abinci da ke Barnawa, tare da kwashe kayan abincin da aka ajiye.
Sai dai gwamnatin jihar ta ce wasu daga cikin kayan da aka kwashe an ɗebe su ne a wani wuri da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa NAFDAC ke ajiye abincin da ya lalace.
Taraba
A ranar Asabar 24 ga watan Satumba ne dandazon jama'a suka yi wa wani gidan ajiyar kayan abinci da ke birnin Jalingo ƙawanya duk da jami'an tsaron da ke gadinsa, tare da kwashe dukkanin kayan abincin da aka ajiye.
Wannan al'amari ya sa gwamnatin jihar ta ɗauki matakin sanya dokar hana fita ta tsawon sa'a 36 domin daƙile lamarin.
Adamawa
A jihar Adamawa, gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita ta tsawon awa 24, bayan samun wasu matasa da kwashe kayan da aka ajiye don tallafa wa waɗanda annobar korona ta janyowa shiga garari.
Gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri ya ce an riga an raba kashi hudu na kayan, kashi daya ne kawai ya rage ba a bai wa jama'a ba, kuma su ma ɗin za a bayar da su ne ranar Litinin ɗin nan.
Filato
Mutane sun shiga wani gidan ajiyar abinci da ke Buruku, a Jos Ta Kudu.
Sai dai gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwa, in da ta ce ba ta ɓoye komai ba, hasalima ta gama raba waɗanda ta karɓa daga ma'aikatar jin ƙai tun a ranar 16 ga watan Octoba.
Bauchi
Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya ce wasu mutane sun yi yunƙurin shiga wani gidan ajiyar abinci na gwamnatin jihar da zummar kwashe kayayyakin da ake ciki, amma ba u tarar da komai ba, domin tuni gwamnati ta raba su ga mutane.
Legas
A jihar Legas ranar Alhamis ne wasu matasa suka kwashe kayan abinci a inda aka ajiye su a unguwar Maza-Maza, tare da kwashe komai a ciki.
Hakan na zuwa ne bayan da rikici ya ɓarke a jihar sakamakon zanga-zangar End SARS wadda ta rikiɗe ta zama rikici.
Ekiti
A nan ma an kwashe kayan abinci a inda ake ajiye da su a birnin Ado Ekiti, amma gwamnatin jihar ta ce suna ɗauke da sinadarai.
Sanarwar gwamnatin jihar ta ce an kwashe abincin ne a wani wuri da hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar wato SEMA ke ajiye taki, amma sai mutane suka yi zaton garin kwaki ne.
Kogi
Mutane sun fasa wani gidan ajiyar abinci da ke birnin Lokoja, amma gwamnatin jihar ta ce tuni ta raba tallafin na cutar korona.
Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ta gode wa mutanen, bisa yadda suka je suka debi nasu kason.
Osun
Mutane sun shiga gidan Cocoa da aka jibge tarin kayan abinci tare da kwashe su.
A cewar gwamnatin jihar, kayan na hannun kwamitin raba kayan tallafi na fadar shugaban kasa har yanzu, don haka ba su zama nata ba tukunna.











