Shugabannin Afrika da suka fi dadewa a mulki

Asalin hoton,
An wallafa
Jami'ai sun fitar da sakamakon zaben raba gardama a kasar Congo-Brazzaville, wanda ya nuna cewa sama da kaso 92 cikin dari na masu zabe sun amince da sauya kudun tsarin mulkin kasar da zai bai wa shugaban kasar damar sake takarar mulki a karo na uku.
A yanzu dai kudun tsarin mulkin kasar bai yadda Shugaba Denis Sassou Nguesso ya sake shiga takara ba, saboda shekarun sa sun wuce 70, kuma ya riga ya yi mulki sau biyu.
Sassou Nguesso ya hau mulki a shekarar 1979, inda face wasu shekaru biyar da ya yi ba a kan karargar ba, ya ke mulkin kasar.
Ga shugabannin da suka dade a kan mulki:
- <image id="d5e343"/> <paragraph>Shekaru 35 a kan mulki: Robert Mugabe, shugaban kasar Zimbabwe. Shi ne kadai shugaban kasa a nahiyar Afrika da ya ke mulki tun lokacin da kasar sa ta samu 'yancin kanta, inda Mugabe ya zama Firayi Ministan a watan Afrilun shekarar 1980 daga bisani kuma ya zama shugaban kasar a shekarar 1967.</paragraph>
- <image id="d5e353"/> <paragraph>Shekaru 32 a kan mulki: Paul Biya, shugaban kasar Kamaru. Ya hau karagar mulki a ranar 6 ga watan Nuwambar shekarar 1982.</paragraph>
- <image id="d5e369"/> <paragraph>Shekaru 26 a kan mulki: Omar al-Bashir, shugaban kasar Sudan. Yana kan karaga tun bayan da ya kwace mulki a watan Yunin shekarar 1989.</paragraph>
- <image id="d5e379"/> Shekaru 25 a kan mulki: Idriss Deby, shugaban kasar Chadi. Ya soma mulkin kasar a watan Disambar shekakar 1990, bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar, Hissein Habre. <paragraph>Ga kuma shugabannin Afrika da suka fi dadewa a mulki a kasashen da aka yi wa mulkin mallaka a tarihin Afrika.</paragraph>







