Arsenal na son Guimaraes, yayin da Chelsea ke harin Lacroix

Bruno Guimaraes

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal na son ɗauko ɗan wasan Brazil Bruno Guimaraes daga Newcastle a wannan kaka. (Mail)

Tottenham ta sake yin wasi da tayin ɗan wasan Newcastle Sandro Tolani, inda Totthenham din ke son siyar da ɗan wasan kan Euro miliyan ɗari. (Mail)

RB Leipzig taƙi amincewa da tayin da Liverpool ta yi na baya-bayan nan, na fam miliyan 100, kan ɗan wasan Ivory Coast Yan Diomande. (Teamtalk)

Mai tsaron ragar Mancester United da Kamaru Andre Onana, na shirin rattaba hannu kan kwantaragi a kaka ta biyu a mastyin dan wasan aro a Trabzonspor da ke Turkiya. (Mail)

Crystal Palace na son siyar da ɗan wasan Faransa Maxence Lacroix, kan fam miliyan 50, inda ƙungiyoyin ingila ke son daukar sa ciki har da Chelsea. (Football Insider)

Bournemouth ta shiga jerin ƙungiyoyin da ke son ɗaukar ɗan wasan Benfica da Colombia Richard Rois. (Sportwitness)

Inter Milan za ta iya yunƙurin ɗaukar dan wasan Chelsea da Ingila Trevoh Chalobah, idan har suka gaza siyen dan wasan bayan Faransa Oumar Solet, daga Udinese. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Borussia Dortmund ba zata siyar da ɗan wasanta na ƙasar Jamus Felix Nmecha, kan ƙasa da fam miliyan 86, (euro miliyan 100). (Kicker - in German)

Wolves ta sanya farashin Fam miliyan 15 kan ɗan wasanta Huge Bueno, yayin da Fiorentina ke nuna shawa'arta na son ɗaukar ɗan wasan. (Football Insider)