Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda wasannin Premier mako na 16 suka gudana

Muna kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. GOAL ' 48, Everton 2-0 Chelsea

    Calvert-Lewin ya ska ta biyu a ragar Chelsea.

  2. An dawo hutun rabin lokaci, Everton 1-0 Chelsea

    Minti 45 din karshe kamar dai na farko da alamun ranar yau ta Everton ce. Chelsea na bukatar kara kaimi.

    An ci gaba da wasa babu wanda ya yi canji.

  3. An tafi hutun rabin lokaci, Everton 1-0 Chelsea

    Goodison Park ta dauki harama ba don komai ba saboda tawagarsu na ci. Magoya bayan ba za su taba manta abin kunyar da kungiayr ta aikata ba ranar Laraba da ta gabata, inda Liverpool ta ragargaje ta da ci 5-2 a wasa irin na hamayyar birnin Liverpool.

    Na tabbata za su so su tashi da maki uku a karshen wannan wasa musamman ma yanzu da suke jan ragamar wasan.

    Kazalika mai horarwa Duncan Ferguson ba zai so ya fara da rashimn nasara ba a wasansa na farko a matsayin koci bayan sallamar Marco Silva a ranar Alhamis.

  4. An kara minti '2, Everton 1-0 Chelsea

  5. Richarlison, Everton 1-0 Chelsea

    Kwallo ta biyar kenan ga Richarlison dan kasar Brazil mai shekara 22 a Premier ta bana.

    Ko zai ci ta biyu?

  6. Katin gargadi, Everton 1-0 Chelsea

    An bai wa Richarlison katin gargadi sakamakon keta da ya yi wa Kovacic.

  7. Everton 1-0 Chelsea, Everton 1-0 Chelsea

    Chelsea ta bude wuta amma Everton ta dage ta ki yarda kwallon ta rika karasawa wajen mai tsaron gida Jordan Pickford.

  8. Theo Walcott, Everton 1-0 Chelsea

    Walcott na ci gaba da matsa wa bayan Chelsea - kwallo ta biyu kenan da ya kai kofar gidan Chelsea.

    Babu mamaki tsohon dan wasan Arsenal din ya amfana da ta uku.

  9. Richarlison, Everton 1-0 Chelsea

    Richarlison na da kwallo hudu kafin ta yau, har wadda ya ci yau kwallo biyar kenan, shi ne wanda ya fi ci wa Everton kwallo a wannan shekarar>

  10. Abraham, Everton 1-0 Chelsea

    Abraham ya sake kai hari, inda ya saka wa kwallo kai sai dai ya yi satar gida, in ji mataimakin alkalin wasa.

  11. Tammy Abraham, Everton 1-0 Chelsea

    Tammy Abraham na da Kwallo 11 a Premier ko zai iya kara wa kwallon nasa yawa?

  12. Rawar da ake takawa, Everton 1-0 Chelsea

    Chelsea tana buga wasa ne a tsakiyar fili da shafa ta daya bayan daya amma har yanzu ba ta kai hari na-ci ba.

  13. Everton 1-0 Chelsea, Everton 1-0 Chelsea

    Ba karamin kokari Everton take ba, amma abin tambayar shi ne, za ta iya wannan kokarin har karshen lokaci?

  14. Everton 1-0 Chelsea, Everton 1-0 Chelsea

    Kokarin da Everton take shi ne ta ga ta samu nasarar wannan wasa. Har yanzu Chelsea ba ta kai wa Jordan Pickford hari ba.

  15. Chelsea ta kusa farkewa, Everton 1-0 Chelsea

    Willian ya kai hari a ragar Everton bayan 'yan bayan Everton sun yi kuskure.

    Sai dai ya buga kwallo waje. Babu hadari ga Everton.

  16. Kante ya yi keta, Everton 1-0 Chelsea

    Kante ya yi wa Walcot keta.

  17. Everton 1-0 Chelsea

    Richarlison ya ci wa Everton kwallon farko.