Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda wasannin Premier mako na 16 suka gudana

Muna kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Wasa ya kare, Aston Villa 1-4 Leicester

  2. An kara minti '6, Norwich 1-2 Sheffield United

  3. GOAL '87, Newcastle 2-1 Southampton

    Fernendez ya ci wa Newcastle kwallo ta biyu⚽

  4. Jamie Vardy, Aston Villa 1-4 Leicester

    Jamie Vardy ya ci kwallo 11 a wasa 8 na baya-bayan nan.

    vs Burnley ⚽

    vs Southampton ⚽⚽⚽

    vs Crystal Palace ⚽

    vs Arsenal ⚽

    vs. Brighton ⚽

    vs Everton ⚽

    vs Watford ⚽

    vs Aston Villa ⚽⚽

    Kwallo 16 ya ci baki daya a kakar bana.

  5. Cantwell, Norwich 1-2 Sheffield United

    Cantwell ya kai mummunan hari na-ci, inda ya dada wa mai tsaron ragar Sheffield kwallo. Sai dai golan ya tura ta kwana.

  6. Vardyyy GOAL '75, Aston Villa 1-4 Leicester

    Jamie Vardy ya ci gaba da yin abin da ya saba. Kwallo ta biyu kenan da ya ci a wannan wasa kuma ta 16 a kakar bana.

    Ya ci kwallo 25 a wasa 24 na baya-bayan nan ga Leicester City.

  7. An kori dan wasan Sheffield United, Norwich 1-2 Sheffield United

    An bai wa Chris Basham jan kati, bayan wata keta da ya yi.

  8. Norwich City ta yi canji biyu a jere, Norwich City 1-2 Sheffield United

    An cire Sam Byram, Jamal Lewis ya maye gurbinsa.

    Onel Hernandez ya fita, An sako Todd Cantwell.

  9. Iheanacho, Aston Villa 1-3 Leicester

    Iheanacho ya ci kwallo a dukkanin wasa hudu da ya buga wa Leicseter City a kakar bana - kwallo hudu.

  10. GOAL '67, Newcastle 1-1 Southampton

    Jonjo Shelvey

  11. Leicester ta yi canji, Aston Villa 1-3 Leicester

    An cire Kelechi Iheanacho an sako Harvey Barnes.

  12. Katin gargadi, Aston Villa 1-3 Leicester

    An bai wa John McGinn katin gargadi.

  13. Danny Ings, Newcastle 0-1 Southampton

    Danny Ings ne dan wasan Southampton na farko da ya ci kwallo a wasa biyar a jere a Premier tun bayan James Beattie wanda ya yi hakan a 2003.

  14. GOAL, Newcastle 0-1 Southampton

    Danny Ings ya jefa kwallo ta farko a ragar Newcastle. Kwallonsa ta 8 kenan a bana.

  15. GOAL '50, Norwich City 1-2 Sheffield United

    George Baldock

  16. GOAL '48, Aston Villa 1-3 Leicester

    Evans ya kara ta uku. Kwallonsa ta farko kenan a Premier bana.

  17. Aston Villa 1-2 Leicester, Aston Villa 1-2 Leicester

    Aston Villa ta dawo da karfinta don haka idon Leicester ba ta kara dagewa ba tsaf za a zare kwallon da take da.

  18. GOAL '48, Norwich 1-1 Sheffield United

    Stevens ya farke wa Sheffield United kwallonta.

  19. An dawo wasa

    • Aston Villa 1-2 Leicester
    • Norwich 1-0 Sheffield United
    • Newcastle 0-0 Southampton
  20. An tafi hutun rabin lokaci, Newcastle 0-0 Southampton