An dawo hutun rabin lokaci
- Bournemouth 0-2 Liverpool
- Tottenham 3-0 Burnley
- Watford 0-0 Crystal Palace
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muna kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Rigima na neman kaurewa tsakanin 'yan wasa yayin da Cahill ke yi wa alkalin wasa korafi kan wata dama da ya hana su.
Dele Alli ya taimaka kai-tsaye wurin cin kwallo shida a cikin wasa biyar da ya buga karkashin Mourinho a dukkanin gasanni (ya ci 4, ya bayar an ci 2), rabin haka ya samu a wasannin da ya buga karkashin Pochettino (kwallo 2, taimako 1 a wasa 10).
Sarr na kara nuna kwarewa da kuruciya a wannan wasa.
Dejan Lovren ya fita, yayin da Trent Alexander-Arnold ya karbe shi.
Kaita ne ya ci wa Liverpool.
Alex Oxlade-Chamberlain shi ne dan wasa na 15 da ya ci wa Liverpool kwallo a wannan kakar, wanda wannann shi ne lokacin da aka samu 'yan wasan da yawa suka ci kwallo sama da kowanne lokaci.
An bai wa Abdoulaye Doucoure da Wilfried Zaha katin gargadi
Alex Oxlade-Chamberlain
Wannan wacce irin kwallo ce!
Son ne ya dauki kwallon tun daga baya ya rika yanka har sai da ya zira ta a zaren Burnley.
Babu shakka wannan kwallon za ta iya zama daya daga cikin kwallon Premier ta wannan shekarar.
Tottenham ta rike wasan ta yadda ba ta bai wa Burnley damar taka rawar gani a wasan.
Harry Wilson na neman bugun tazara, alkalin wasa ya ce ya tashi babu komi.
Mummunan hari da Brady ya kai, amma ta daki turke kuma Wood ya kara, sai dai Sánchez ya fitar da kwallon waje.
Liverpool ta mamaye wasan sai dai har yanzu babu wani kwakkwaran hari da zai nuna tana bukatar kwallo.
Kwallon ba ta kayatarwa zuwa yanzu.
Bayan wata doguwar turka-turka Lucas ya samu nasarar jefa kwallo ta biyu.
Harry Kane ne ya dada kwallon daga waje. Kwallo ta farko ga Tottenham. Kwallo ta 8 ga Harry Kane a Premier ta bana.
Wasannin uku za mu kawo muku
Bournemouth v Liverpool
Tottenham v Burnley
Watford v crystal Palace