Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda wasannin Premier mako na 16 suka gudana
Muna kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
An kara minti '4, Watford 0-0 Crystal Palace
An kara minti '3, Tottenham 5-0 Burnley
Liverpool ta yi canjn karshe, Bournemouth 0-3 Liverpool
An cire Alex Oxlade-Chamberlain an sako Xherdan Shaqiri.
Katin gargadi, Watford 0-0 Crystal Palace
An bai wa Kiko Femenia katin gargadi bayan doke Zaha da ya yi.
Ismaila Sarr, Watford 0-0 Crystal Palace
Ismaila Sarr yana kokari, amma ya tada hankalinsa a wasan.
Mohamed Salah, Bournemouth 0-3 Liverpool
Mohamed Salah ya ci kwallo 63 a wasa 100 na Premier.
'Yan wasa uku ne kacal suka fi dan kasar Masar din zira kwallaye a wasansu 100 na farko - Alan Shearer (79), Ruud van Nistelrooy (68) da kuma Sergio Aguero (64).
Watford na neman Finareti, Watford 0-0 Crystal Palace
bayan wani mummunan hari da Watford ta kai, yanzu tana neman bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Zaha, Watford 0-0 Crystal Palace
Zaha ba ya komi a wannan wasa, sai dai kuma dan wasa ne da cire shi ka iya zama koma baya ga Palace.
Liverpool ta yi canji, Bournemouth 0-3 Liverpool
Andy Robertson ya fita, Curtis Jones ya shigo kuma wannan ne wasan farko na matashin dan wasan.
GOAL '74, Tottenham 5-0 Burnley
Sissoko ya ci ta biyar.
Burnley ta yi canji, Bournemouth 0-3 Liverpool
Aaron Lennon tsohon dan wasan Tottenham ya shigo ya maye gurbin Robbie Brady.
Watford 0-0 Crystal Palace, Watford 0-0 Crystal Palace
Hankali ya dawo kan wannan wasan domin ganin wainar da ake toyawa.
Sauran wasannin biyu a iya cewa an kammala su.
, Tottenham 5-0 Burnley
Chris Wood ya fita, Matej Vydra ya shigo - wasansa na farko kenan cikin sama da wata guda.
Bournemouth ta ci kwallon satar gida, Bournemouth 0-3 Liverpool
Bournemouth ta yi canji, Bournemouth 0-3 Liverpool
Callum Wilson ya fita Dan Gosling ya maye gurbinsa.
GOAL '54, Bournemouth 0-3 Liverpool
Salah ya jefa ta shi. Da ma ya kwana biyu ba a ji duriyarsa ba.
Kwallo ta bakwai kenan da ya ci a bana a Premier.
Kaaaaaane GOAL '53, Tottenham 4-0 Burnley
Wannan kafar damar ta Harry Kane azaba ce! Ya kara ta biyu!
Ko Kane zai iya cin kwallo uku a yau?
Da ma a baya ya taba cin Burnley uku shi kadai.
Kwallo ta tara kenan da Kane ya ci a Premier ta bana.
Sau 14 ya taba cin kwallo uku rigis a wasa daya tun sanda ya fara buga tamaula a matsayin kwararre.
Liverpool na neman ta uku, Bournemouth 0-2 Liverpool
Liverpool ta matsu ta kara ta uku yayin da Salah ya bai wa Keita kwallo, wanda shi kuma ya yi kokarin neman Alexander-Arnold amma dan wasan bayan bai iya buga kwallon ba.
, Watford 0-0 Crystal Palace
Riedewald ya canji Jeffrey Schlupp
Da alama tsoorn jin rauni ne ya sa aka maye gurbin dan wasan.