Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda wasannin Premier mako na 16 suka gudana

Muna kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Tawagar Tottenham

    Jose Mourinhpo ya yi canji daya a tawagar da ya yi wasan Manchester United da ita, Eric Dier ya maye gurbin Harry Winks.

  2. Tawagar Burnley

  3. Tawagar Watford

    Yan wasa:Foster, Kabasele, Femenía, Cathcart, Masina, Sarr, Doucouré, Capoue, Pereya, Deulofeu, Deeney.

    Yan canji :Gomes, Chalobah, Mariappa, Foulquier, Gray, Success, Hughes.

  4. Tawagar Crystal Palace

    An maye gurbin Mamadou Sakho da aka bai wa jan kati a wasan da ya gabata, sai Jeffrey Schlupp da ya ci kwallo a wasan da ya gabata wanda ya maye gurbin Patrick van Aanholt.

    Yan wasa: Guaita, Kelly, Cahill, Tomkins, Schlupp, McArthur, Kouyate, Milivojevic, Townsend, Zaha, Ayew.

    Yan canji:Hennessey, Riedewald, Dann, Camarasa, McCarthy, Wickham, Benteke.

  5. Liverpool ta yi canji bakwai

    Liverpool ta yi canji bakwai cikin tawagar da ta ci Everton 5-2 a wasan da ya gabata. Roberto Firmino da sun dawo amma an aje Mane a benci.

    'Yan wasa :Alisson, Gomez, Lovren, Van Dijk, Robertson, Henderson, Milner, Keita, Oxlade-Chamberlain, Salah, Firmino.

    'Yan canji:Adrian, Mane, Shaqiri, Origi, Jones, Alexander-Arnold, Elliott.

  6. Tawagar Bournemouth

    Canji biyu ne aka yi a Bournemouth na Simon Francis da Ryan Fraser da za su shigo.

    An aje Adam Smith saboda rauni, yayin da Harry Wilson ya shirya tsaf domin tunkarar kulob din iyayensa.

    'Yan wasa: Ramsdale, Francis, Mepham, Ake, Rico, Fraser, Lerma, Billing, Danjuma, Solanke, Callum Wilson.

    'Yan canji: Boruc, Gosling, Surman, Ibe, Lewis Cook, Stacey, Simpson.

  7. Shi ke nan, Everton 3-1 Chelsea

    Wasa ya kare! An cinye Chelsea! An cinye Lampard! Sakamako maras dadi ga masu ziyara - rashin nasara a karo na biyar a bana ga Chelsea.

    Masu masaukin baki bakinsu har kunne.

  8. Liverpool ta yi canji bakwai

    Liverpool ta yi canji bakwai cikin tawagar da ta ci Everton 5-2 a wasan da ya gabata. Roberto Firmino da sun dawo amma an aje Mane a benci.

    Za mu kawo muku sharhin wasannin nan kai tsaye.

    Bournemouth da Liverpool

    Tottenham da Burnley

    Watford da Crystal Palace

  9. Duncan Ferguson, Everton 3-1 Chelsea

    Mai horarwa Duncan Ferguson bakinsa har kunne yau din nan. Wa ya sani ma ko zai iya barci!

    Wasansa na farko kenan a matsayin koci amma ya saka wa Chelsea kwallo uku a raga.

  10. GOAL '83, Everton 3-1 Chelsea

    Wannan wasa yana kyau ga Everton!

    Calvert-Lewin ya ci kwallo ta biyu bayan an yi tataburza da kwallon da Davies ya shigo da ita har gaba Kepa.

    Ana tsaka da damadamar ne kuma Lewin ya zungura ta raga.

    Koci Duncan Ferguson baki har kunne.

  11. , Everton 2-1 Chelsea

    Azpilicueta ya buga shot a kusa da yadi na bakwai, mai tsraon raga Pickford ya yi tsalle ya yi mata gada zuwa bugun kwana.

  12. , Everton 2-1 Chelsea

    Christensen ya buga shot daga wajen yadi na 18, sai dai ta yi fadi zuwa wajen fili.

  13. Abraham a kasa, Everton 2-1 Chelsea

    Abraham a kasa bayan mai tsaron raga da dan wasan bayan Everton sun matse shi a tsakiya.

    An duba shi kuma ya ci gaba da wasa. Da alama ba babbar matsala ba ce.

  14. Chelsea ta yi canji, Everton 2-1 Chelsea

    Callum Hudson-Odoi ya karbi Willian.

  15. Chelsea ta yi canji '70

    Davies ya karbi Richarlison

  16. , Everton 2-1 Chelsea

    Pulisic ya yi wa Sidibe keta - Sidibe ya kankane bayan Everton ya bayar da tsaro sosai, abin da bai yi wa Pulisisc dadi ba, shi ya sa ya bige shi kawai.

  17. Mount ya kai hari, Everton 2-1 Chelsea

    Mason Mount ya buga kwallo a cikin yadi na 18 amma ta yi fadi, babu wani hadari ga Pickford.

  18. Walcott, Everton 2-1 Chelsea

    Theo Walcott ya dada kwallo ga Kepa a cikin yadi na 18, golan ya bige ta.

    Amma da Walcott ya bai wa Richarlison kwallon ina ganin da ta zama ta uku a ragar Chelsea.

  19. Everton 2-1 Chelsea, Everton 2-1 Chelsea

    Duncan Ferguson na bukatar kara dagewa saboda har yanzu babu tabbas din samun nasara a wasan.

  20. GOAL '52, Everton 2-1 Chelsea

    Kovacic ne ya farke wa Chelsea kwallo daya tun daga kusan yadi na 25.

    Kwallo ce mai kyau kuma ko murna 'yan wasan ba su zauna yi ba saboda gaggawa.

    Mai tsaron raga Pickford bai yi azama ba gaskiya.