Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fafata a wasannin Premier mako na 13

Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Harry Kane, West Ham United 0-3 Tottenham

    Harry Kane ya shiga jerin 'yan wasan da suka fi ci wa Tottenham kwallo, yanzu yana da kwallo 175 da ya ci, inda yake bin bayan Jimmy Greaves da ke da kwallo 266 da kuma Bobby Smith me 208.

  2. Babu wani katabus daga West Ham United, West Ham United 0-3 Tottenham

    Irin fushi da kuma kwazo da West Ham ke nuna wa a baya saboda buga wasa da Tottenham da suke birnin daya yanzu duk babu shi.

  3. Harry Kane ya kusa ci, West Ham United 0-3 Tottenham

    An bai wa Harry kane kwallon kuma ya tsinke a guje zuwa ragar West Ham, sai dai Diop ya yunkura ya hana shi cin kwallo ta hudu a wasan.

  4. West Ham United ta yi canji, West Ham United 0-3 Tottenham

    Felipe Anderson ya fita, Michail Antonio ya shiga.

  5. Jose Mourinho, West Ham United 0-3 Tottenham

    Jose Mourinho ya ci dukkanin wasanni 36 da ya buga wadanda a cikinsu ya fara zira kwallo biyu ko fiye da haka a raga.

    Da alama dai yau zai ci na 37 domin kuwa West Ham ba su nuna suna da wani hadari ga Tottenham ba tun daga farkon wasa.

  6. Satar gida, West Ham United 0-3 Tottenham

    Antonio ya yi satar gida..

  7. Harry Kane, West Ham United 0-3 Tottenham

    Kwallo ta 7 kenan da Harry Kane ya ci a Premier bana.

    Kwallo ta uku ga Mourinho kuma ta uku ga Tottenham a wasan yau.

  8. GOAL '49, West Ham United 0-3 Tottenham

    Harry Kane ya zira kwallo ta uku a ragar West Ham United.

  9. Lucas Mouraaaa, West Ham United 0-2 Tottenham

    Moura ya barar da kwallo mai hadarin gaske a gaban ragar West Ham.

  10. An dawo wasa, West Ham United 0-2 Tottenham

  11. Hutun rabin lokaci., West Ham United 0-2 Tottenham

    Da wahala ka furta wani abu na sauyi a kwallon Tottenham, ko kuma wani sauyi da Mourinho ya samar a kungiyar ya zuwa yanzu.

    Dele Alli does look engaged, though. And they have dealt with pretty much everything the Hammers have thrown at them, although that is less the kitchen sink and more the pathetic, sad little cloth you use to clean it.

    Dele Alli yana kokari, haka zalika Son da Moura sai dai Kane ne kamar babu shi a wasan.

  12. Hutun rabin lokaci., West Ham United 0-2 Tottenham

    ka iya cewa Tottenham ba waniu kokarin azo a gani take ba, amma ta yi amfani da boiyu daga cikin damar da ta samu ta jefa kwallaye biyu.

    Babu alamun nasara ga West Ham United, har yanzu barci take, babu wani kwarin gwiwa a tare da 'yan wasanta, ko sun karaya ne da wasan.

  13. An tafi hutun rabin lokaci., West Ham United 0-2 Tottenham

    Son Heung-Min da Lucas Moura ne suka jefa kwallayen da Tottenham ta ci.

  14. West Ham United 0-2 Tottenham, Mourinho

    Mourinho ya fice daga filin wasa kafin a juya hutun rabin lokaci.

  15. Karin lokaci, West Ham United 0-2 Tottenham

    An kara minti 2 kafin tafiya hutun rabin lokaci.

  16. GOAL '43, West Ham United 0-2 Tottenham

    Kwallo ta biyu a ragar West Ham United.

    Lucas Moura ya jefa kwallo ta biyu, bayan Son ya kwaso masa ita.

    Nasara na neman tabbata a bangaren koci Mourinho.

  17. West Ham United 0-1 Tottenham, Mourinho

    Kwallo ta Musamman ga Mourinho.

    ya ta shi daga kujerarsa don nuna farin ciki da aikin Son.

  18. Katin gargadi, West Ham United 0-0 Tottenham

    An bai wa Frediricks na West Ham katin gargadi bisa ketar da ya yi wa Son.

  19. GOAL '36, West Ham United 0-1 Tottenham

    Son ya jefa kwallo ta farko a ragar West Ham United.

    Kwallo ta Farko ga sabon koci Mourinho, kuma kwallo ta shida ga dan wasan a cikin wasa shida.

  20. West Ham United 0-0 Tottenham, West Ham United 0-0 Tottenham

    Har yanzu babu wani abun birgewa a wasan daga duka kungiyoyin biyu,kamar kwallon tsoron tsoro suke bugawa.