Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fafata a wasannin Premier mako na 13

Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Man City 2-1 Chelsea, Man City 2-1 Chelsea

    kiris ya hana City kara kwallo, amma ina wani dan baya ya cire ta.

  2. Man City 2-1 Chelsea, Man City 2-1 Chelsea

    Ko waye ya jefa kwallo ta gaba za ta zama mai mahimmanci kwarai, in City ce za ta bata damar jin nasara a wasan, in ko Chelsea ce za ta samu karfin gwiwar kara kwallo domin samun nasara a karshen wasa.

  3. Man City ta yi chanji, Man City 2-1 Chelsea

    Rodri ya fita Gündogan ya shigo.

  4. An dawo zagaye na biyu, Man City 2-1 Chelsea

    Bakin rai bakin fama City na son ta ga ta tsira da wannan maki. Sai dai ita ma Chelsea ba za ta so ta ga ta yi rashin nasara ba ko dan saboda matsayinta a teburin Premier.

  5. Man City 2-1 Chelsea, Man City 2-1 Chelsea

    Kun san kuwa duk wanda yake gida a wasannin Premier yau bai ci wasa ba, watakila City za ta iya kai bantenta.

  6. An tafi hutun rabin lokaci, Man City 2-1 Chelsea

  7. Ngolo Kante, Man City 2-1 Chelsea

    Kante ya ci kwallo uku a shot uku na-ci da ya buga a Premier ta bana.

  8. Agueroooo '44, Man City 2-1 Chelsea

    Aguero ya shimfida kwallo da kyau amma ta bugi tirke ta dawo.

    An samu damar ne bayan mai tsaron ragar Chelsea Kepa ya yi kuskuren buga kwallon gare shi a tsakiyar fili.

  9. GOAL '36 Mahrez, Man City 2-1 Chelsea

    Ba za ku so ku daukje idonku daga wasan nan ba.

    Riyad Mahrez ne ya kara kwallo ta biyu bayan ya yi kwance-kwance ya dada wa Kepa kwallon a cikin yadi na 18.

  10. GOAL '29, Man City 1-1 Chelsea

    De Bruyne ya fake wa Man City kwallon ne bayan fasin din da David Silva ya ba shi an toshe shi, bai yi wata-wata ba ya zuga kwallon inda ta daki jiki Zouma kafin ta fada cikin raga.

  11. GOAL '21, Man City 0-1 Chelsea

    Ngolo Kante ne ya kantara wa Man City kwallo bayan Mateo Kvacic ya bugo masa kwallon a sama, shi kuma ya take ta ya shiga tsakar yadi na 18 din City kuma ya buga ta raga bayan ya yi arba da Ederson.

    Duk da matsin da Mendy ya saka masa hakan bai hana shi cin kwallon ba a wasansa na 150 a Chelsea.

  12. Man City 0-0 Chelsea, Man City 0-0 Chelsea

    Tomori ya kusa jefa kwallo. Chelsea na nuna hankalinta kwance yake.

  13. Man City 0-0 Chelsea, Man City 0-0 Chelsea

    Wasan ya fara daukar zafi, duka kungiyoyin biyu suna iya kokarinsu.

  14. Man City 0-0 Chelsea, Man City 0-0 Chelsea

    Abraham amma ina ta yi waje

  15. Man City 0-0 Chelsea, Man City 0-0 Chelsea

    Willian ya kai irin harin da De Bruyne ya kai wa Chelsea.

    Da yanzu kowa ya samu kwallo cikinsu.

  16. Man City 0-0 Chelsea, Man City 0-0 Chelsea

    De Bruyne ya kai wani hari na kin karawa.

  17. Man City 0-0 Chelsea, Man City 0-0 Chelsea

    Da alamun City a shirye ta fito don buga wannan wasa, saboda kashin da ta sha a hannun Liverpool a wasan mako na 12 da ya gabata.

  18. Man City 0-0 Chelsea, Man City 0-0 Chelsea

    Kocin Ingila Gareth Southgate ya na filin wasa na Etihad in da ya nemi wuri ya zauna daram.

  19. An fara wasa, Man City v Chelsea

  20. Liverpool ta lallasa Crystal Palace har gida, Crystal Palace 1-2 Liverpool

    Har yanzu tawagar Jurgon Klopp na ci gaba da bai wa kungiyoyi kashi a Premier bayan ta lallasa Crystal Palace har gida da ci 1-2 a wasan mako na 13.

    Palace ta bai wa Liverpool wuya sosai domin kuwa ta fi ta taka rawar gani a wasan, inda Liverpool din ta fi shan wahala sama da wasanta da Aston Villa a wasan mako na 11.

    Sadio Mane ne ya fara jefa kwallo a ragar masu masaukin bakin a minti na 49 - shi ne dan wasa na uku da ya ci kwallo a wasan Premier biyar a jere a tarihin Liverpool.

    Sai ana saura minti takwas a tashi daga wasa Wilfred Zaha ya farke kwallon amma Roberto Firmino bai bari an tashi ba sai da ya kara ta biyu a minti na 85.

    Kwallon da Zaha ya ci ita ce ta farko a cikin wasa 14 na Premier da ya buga.

    Liverpool ta ci gaba da zamanta a saman teburi da maki 37, maki takwas kenan tsakaninta da Leicester City a matsayi na biyu.