Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fafata a wasannin Premier mako na 13

Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. An dawo hutun rabin lokaci, Sheffield United 1-0 Man United

    Sheffield United ta fi Man United taka rawa a kowane fanni.

    Yadda wasan nan ke tafiya Man United na da aiki a gabanta musamman 'yan wasan bayanta.

    Mun ga yadda Phil Jones ya yi ta fama a tsakiyar bayan.

  2. Ya kuka ji wannan?, Sheffield United 1-0 Man United

    An saka wa Man United kwallo a raga a kowanne wasa 12 na baya-bayan nan da ta buga a manyan gasanni - mafi muni a tarihin kungiyar kenan tun a shekarar 1985/86 da hakan ta faru a wasa 15 a jere.

    Ba mu sani ba ko za ta farfado daga wannan kwallon da ta sha a yau.

  3. An tafi hutun rabin lokaci, Sheffield United 1-0 Man United

  4. Manchester United, Sheffield United 1-0 Man United

    Man United na bayar da kwallo a sadaka.

    Cikin minti kusan 41 sau daya ta kai wa mai tsaron raga Simon Moore hari, wanda ya fara buga wasan na Premier a yau.

    Dole ne Ole Gunnar Solskjaer ya yi wani abu da zai canza wasan saboda alamu na nuna Sheffield ce za ta iya cin kwallo ta gaba.

  5. Ya kuka ji wannan?, Sheffield United 1-0 Man United

    An saka wa Man United kwallo a raga a kowanne wasa 12 na baya-bayan nan da ta buga a manyan gasanni - mafi muni a tarihin kungiyar kenan tun a shekarar 1985/86 da hakan ta faru a wasa 15 a jere.

    Ba mu sani ba ko za ta farfado daga wannan kwallon da ta sha a yau.

  6. Lys Mousset, Sheffield United 1-0 Man United

    Wani bayani kan Lys Mousset: Makonnin baya Chris Wilder ya ce:

    "Dan wasan gaban bai gama warwarewa daga rashin buga wasa ba ne, yana kalubalantar cewa da ya warke zai shiga jerin yara masu kokari.

    Amma ya zuwa yanzu ya tabbatar da hakan a wasan yau.

  7. Martial, Sheffield United 1-0 Man United

    Martial ya kai harin farko a wasan, kuma na farko ga United.

  8. Sheffield United ta kankane wasa, Sheffield United 1-0 Man United

    Har yanzu Man United ba ta kai hari ba kowane iri - babu shot babu wani yunkuri.

    Sheffield dai na ci gaba da nuna cewa a gidanta ake wasa.

  9. Sheff Utd 1-0 Man Utd, Sheff Utd 1-0 Man Utd

    Sheffield United na buga kwallo babu tsoro, ta fito da duka yan wasanta, ta kwace wasan duka.

  10. Sheffield United 1-0 Man United, Sheffield United 1-0 Man United

    Man United na shan wuta daga Sheffield, babu kuma wata alamar cewa United a filin wasan.

  11. GOAL '18, Sheffield United 1-0 Man United

    Bayan wani zubar gado da aka yi tsakanin Mousset da Jones, an buga kwallon De Gea ya buge ta amma Fleck ya kara ta cikin ragar United.

    Man United fa sai ta yi da gaske idan ba haka ba Sheffield za ta ci wasanta na shida kenan a jere.

  12. De Gea ya fara abin da ya saba, Sheffield United 0-0 Man United

    Mummunan hari ga Man United, Sheffield na nuna kwarewa da cikakken shirin samun maki uku a wasan nan.

    Sai dai mai tsaron ragar Man United David de Gea ya hana hara-harai guda biyu na-ci shiga raga a lokaci guda.

    Da alama akwai aiki a gabana United a yammacin yau.

  13. Sheffield United 0-0 Man United, Sheffield United 0-0 Man United

    Man United ta fi rike kwallo sai dai har yanzu ba ta kai hari ko daya ba.

  14. Sheffield United 0-0 Man United, Sheffield United 0-0 Man United

    Mummunan hari ga Man United, Sheffield na nuna kwarewa da cikakken shirin samun maki uku a wasan nan.

    Sai dai mai tsaron ragar Man United David de Gea ya hana hara-harai guda biyu na-ci shiga raga a lokaci guda.

    Da alama akwai aiki a gabana United a yammacin yau.

  15. Sheffield United 0-0 Man United, Shefield United 0-0 Man United

    A karon farko Scott McTominay ba ya cikin tawagar United, don haka da yuwuwar wasan ya sauya, idon aka kwatanta da wasannin baya.

  16. Shefield United 0-0 Man United, Shefield United 0-0 Man United

    Alamu na nuna Man United ba ta son a sanya mata kwallo ganin yadda ta shirya bayanta a yau.

  17. Sheffield United, Shefield United 0-0 Man United

    Babu wanda ya samu nasara kan Sheffield United a wasa 5 na gasar Premier da ta yi a baya, ta yi nasara 2 ta kuma yi canjaras 3.

    Idan Sheffield United ta samu nasara za ta ci wasa uku a gida kenan a jere a karon farko tun watan Agustan 1993.

    Kwallo 9 kawai aka sa mata a raga cikin wasa 12 da ta buga a Premier bana, Leicester ce kawai aka saka wa kwallo 8 sai kuma Sheffield United.

    Sheffield United na da maki 17 bayan wasa 12, wanda wannan shi ne babban tarihin da wata kungiya da ta hauro Premier ta hada tun wanda West Ham ta yi a 2012-13.

    Za ta iya zama kungiyar farko da ta hauro Premier ta hada maki 20 cikin wasa 13 tun wanda Hull City ta samu a 2008-09.

    Za ta iya zama kungiyar da ta ci wasa uku a Premier a jere kuma ba tare da an sa mata kwallo ko daya ba.

  18. Shefield United 0-0 Man United, Shefield United 0-0 Man United

    kocin Manchester United na daya daga cikin manyan koci da ke bai wa yara kanana dama a gasar Premier ta bana.

  19. Manchester United, Shefield United 0-0 Man United

    Manchester United sun ci wasansu 5 cikin shida da suka buga a kowacce gasa.

    Haka zalika United din ta ci wasa daya ne kacal cikin 10 da ta buga a waje a gasar Premier. Ta yi rashin nasara shida ta kuma yi canjaras uku.

    A wasa 11 da ta buga babu wani wasa da ta tashi ba a saka mata kwallo a raga ba.

    Rabon da United ta shiga irin wannan hali - na sa mata kwallo a raga cikin wasa 12 - tun shekarar 1985-86.

    Tun bayan da Sir Alex ya bar United, kungiyar ta yi rashin nasara a wasa 19 a waje a hannun sabbin kungiyoyin da suka hauro Premier. Ta kuma yi nasarar cin wasa 11 da canjaras biyu.

    Rabon da Manchester United ta ci wasa biyu a jere a Premier tun watan Maris.

    Duka wadanda suke ci wa United kwallo a wannan Premier suna tsakanin shekaru 23 ne.

  20. Shefield United 0-0 Man United, Shefield United 0-0 Man United

    Wasa ne da kowacce kungiya ke bukatar makinsa domin samun komawa matsayi na 5 a Premier.