GOAL '55, Everton 0-1Norwich
Pukki ya bai wa Todd Cantwell kwallon in da shi kuma ya zira ta ga ragar Everton.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Pukki ya bai wa Todd Cantwell kwallon in da shi kuma ya zira ta ga ragar Everton.
Mane ya jefa kwallo a ragar Crystal Palace.
Kwallo ta farko ga Liverpool.
Kwallo ta 8 ga Mane a Premier bana.
Mo Salah yana motsawa yayin da 'yan wasan ke shigowa domin fara zagaye na biyu na wasan. sai yaushe ne Jurgen Klopp zai sa dan wasan.
Raul Jimenez na Wolverhampton ya fi kowanne dan wasan Premier jefa kwallo a raga a dukkanin gasanni da kwallonsa 14, inda ya kamo Raheem Sterling me 14 shi ma.
Bana Wolves tana kokari a Premier kuma yanzu haka tana matsayi na biyar.
Har yanzu babu kwallo a wasan, sai dai Leicester ce ke jan ragamar wasan.
Wolves ta kankane wasan.
James Tomkins ya jefa kwallon, bayan duba VAR aka gano an aikata laifi kafin an zira kwallon.
Arsenal sun kasa katabus tun bayan farke kwallonsu da suka yi.
Southampton na kara bude wuta a filin wasa na Emirates.
Southampton na da shot 7 cikin minti 34 yayin da Arsenal ke da biyu kacal, kuma a gida.
Raul Jimenez ya kara kwallo ta biyu, Wolves na jan ragamar wasan.
kiris ya hana kwallon da Barnes ya buga shiga.
An bai wa ChristophZimmermann katin gargadi saboda ketar da ya yi.
Joao Moutinho ya jefa kwallo a ragar Bournemouth
Yawan harin da ake kai wa Liverpool a wasan nan na nuni da kamar Palace za ta iya lashe ta.
Kodayake dai ko rabi ba a yi ba tukuna.
Alexandre Lacazette ya farke kwallon da aka ci Arsenal.
Jordan Ayew ya kai hari ragar Liverpool a cikin yadi na 18 kuma saura kiris ta shiga.
Sai dai ta gangara waje.
D. Ings ya jefa wa Arsenal kwallo a raga.