Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka fafata a wasannin Premier mako na 13
Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Arsenal
'YAn wasan :Leno, Chambers, Papastathopoulos, Luiz, Bellerin, Torreira, Guendouzi, Tierney, Ozil, Lacazette, Aubameyang
Yan canji :Maitland-Niles, Pepe, Mustafi, Nelson, Martinez, Willock, Martinelli.
Southampton
Southampton ta yi canji uku cikin 'yan wasanta da ta buga wasan Everton da su, wanda ta sha kashi da ci 2-1.
'YAn wasa :McCarthy, Cedric, Bednarek, Stephens, Bertrand, Ward-Prowse, Hojbjerg, Armstrong, Obafemi, Ings, Redmond.
YAn canji :Yoshida, Long, Djenepo, Romeu, Boufal, Gunn, Valery.
Brighton
'YAn wasan Brighton I:Ryan, Webster, Duffy, Burn, Montoya, Propper, Stephens, March, Trossard, Maupay, Mooy.
Yan canji : Bissouma, Gross, Balogun, Jahanbakhsh, Murray, Schelotto, Button.
Leicester City
Tawagar Leicester na nan kamar yadda ta buga wasanta da Arsenal.
'Yan wasan Leicester :Schmeichel, Ricardo Pereira, Evans, Soyuncu, Chilwell, Ndidi, Perez, Tielemans, Maddison, Barnes, Vardy.
'Yan canji : Justin, Morgan, Gray, Albrighton, Ward, Iheanacho, Praet
Liverpool
Liverpool ta yi canji daya cikin 'yan wasanta da suka samu nasara a wasan da ta buga da Manchester City, An bar Mo Salah a benci saboda fama da rauni a idon sahunsa, an kuma maye gurbinsa da Alex Oxlade-Chamberlain
Mourinho ya ci wasansa na farko, West Ham United 2-3 Tottenham
Mourinho ya ci wasansa na farko da ya ja ragama a Premier bayan kusan shekara daya, sakamakon kokarin zaratan 'yan wasa Son da Harry Kane.
Jose Mourinho ya ci dukkanin wasanni 36 da ya buga wadanda a cikinsu ya fara zira kwallo biyu ko fiye da haka a raga, yau kuma ya ci na 37.
Har bayan minti 70 na wasan West Ham ba ta nuna za ta yi wani katabus ba sai da Antonio ya farke guda daya a minti na 74.
Son Hueung-min ne ya fara jefa kwallo a ragar West Ham cikin minti na 36 bayan ya ja kwallo cikin raga ta bangaren hagu, inda ya shauda ta da kafar hagun.
Sai kuma a minti na 43 da Son din ya taimaka wa Lucas Moura ya ci ta biyu, minti biyar bayan haka kuma Harry Kane ya kara ta uku.
Son ya ci wa Tottenham kwallaye mafi yawa a kowacce gasa sama da kowanne dan wasa a shekarar 2019, inda ya ci 18 - kwallo daya kenan tsiransa da Harry Kane.
Shi kuwa Harry Kane ya shiga jerin 'yan wasan da suka fi ci wa Tottenham kwallaye a tarihin kungiyar. Yanzu yana da kwallo 175, inda yake bin bayan Jimmy Greaves da ke da kwallo 266 da kuma Bobby Smith me 208.
Ogbonna ne ya farke ta biyu a mintin karshe bayan an kara minti shida, abin da ya kada hantar Tottenham.
Sakamakon ya sa Tottenham ta koma matsayi na shida amma wasannin da za a yi na gaba ka iya sauya mata zama a teburin.
Crystal Palace
Kocin Crystal Palace Roy Hodgson ba yi wasi sauyi ba a bangaren shi, saboda kada Liverpool ta samu nasara ta 5 a jere a kansa, sai dai ya matsar da dan wasan tsakiyarsa Jordan Ayew sama.
Mourinho, West Ham United 2-3 Tottenham
Sakamakon wasan da aka ta shi bai nuna wani banbanci ba daga kungiyoyin biyu. Amma dai Tottenham ta cancanci nasara.
Jose Mourinho zai matukar murna da wannan nasarar, sai dai sakamakon ya nuna akwai bukatar ya yi gyara a kungiyar musamman saboda kwallaye 2 da aka zira wa kungiyar a karshen lokaci.
West Ham na tsaka mai wuya.
Wasannin Premier, za mu kawo muku wasannin 6 nan gaba.
Arsenal vs Southampton
Brighton & Hove Albion vs Leicester City
Crystal Palace vs Liverpool
Everton vs Norwich City
Watford vs Burnley
An tashi daga wasa., West Ham United 2-3 Tottenham
Nasara ga Mourinho ta farko a Tottenham.
Nasara ta farko bayan buga wasanni 5 babu nasara.
Mourinho ya zo da sauyi a kungiyar da alamu.
GOAL '90+6, West Ham United 2-3 Tottenham
Da da sauran lokaci da West Ham ta ba da mamaki.
An kara minti '3, West Ham United 1-3 Tottenham
Da alamun maki uku ya tabbata a hannumn Mourinho.
Michail Antonio ya raina Tottenham., West Ham United 1-3 Tottenham
Duka kwallaye 4 da Antonio ya ci Tottenham a Premier ya ci su ne a filayen wasa daban daban, Upton Park, White Hart Lane, Tottenham Hotspur da kuma Filin wasa na London.
Rice ya yi satar gida, West Ham United 1-3 Tottenham
An hana kwallon bayan duba VAR an kuma gano Rice ya yi satar gida.
Katin gargadi, West Ham United 1-3 Tottenham
An baiwa Kane da Snodgrass katin gargadi, bayan wata hatsaniya da ta barke tsakaninsu.
Labarai da dumi-dumi, Babu Salah a jerin 'yan wasan Liverpool
Mohamed Salah ba ya cikin yan wasan da za su fara buga wa Liverpool a yau, wasan da za ta kara da Crystal Palace, saboda ciwon idon sahu da ya samu. Salah ne kawai a benci, amma Robertson dake da irin wannan raunin za a fito da shi wasan.
Alex Oxlade-Chamberlain zai maye gurbin Salah din.
A wani wasan kuma, Troy Deeney zai buga wasansa na farko a Watford tun watan Agusta, an dai fito da dan kwallon a benci a wasan da kungiyar ta yi da Burnley bayan farfadowar da ya yi daga tiyatar ciwon gwiwar da aka yi ma shi.
Tottenham ta yi canji biyu
An cire Dele Alli an saka Eriksen, sai kuma Moussa Sissoko da ya karbi Lucas Moura.
GOAL '74, West Ham United 1-3 Tottenham
Antonio ne ya zare wa West Ham kwallo daya.
Da ma cen ya matsa wa bayan Spurs din kuma idan tawagar Mourinho ba ta yi hankali ba za ta sha mamaki.
Katin gargadi ga Ben Davies, West Ham United 0-3 Tottenham
Ben Davies ya karbi katin gargadi