An tashi., Arsenal 2-2 Southampton
Arsenal ta sha da kyar.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Arsenal ta sha da kyar.
Babu shakka James Tarkowski ya raba gardama babu ta yadda za a farke wadan nan kwallaye.
Southampton na kokari sai dai tana wasa da damar da take samu kuma kwallo daya ce kawai tsakanin ta da Arsenal.
Ashley Barnes ya raba gardama a wannan wasa.
Har yanzu Jamie Vardy ne ke jan ragamar wadanda suka fi yawan cin kwallo a Premier bana da kwallo 12
Firmino ya kara kwallo ta biyu, bayan wata doguwar turka-turka a ragar Crystal Palace.
Wilfred Zaha ne ya farke. Dama ya matsa wa 'yan bayan Liverpool.
Vardy ne ya ci bayan Maddison ya ci wata kwallo an duba VAR an ki karba.
Ward-Prowse ya buga finariti ya zubar amma ya kara abarsa da kansa, kafin golan ya ta shi.
An ya Unai zai kai karshen kakar wasanni ta bana da Arsenal?
Tun da aka dawo zagaye na biyu Everton take ta kokari amma dama daya Norwich ta samu ta yi amfani da ita.
Ayoze Perez ya ci wa Leicester City kwallonta
Wilfred Zaha ya hada wata kwallo mai hadari cikin ragar Liverpool amma Jordan Ayew ya buga kwallon waje.
Steve Cook ya farke kwallo daya cikin biyu da aka zira musu.
Chris Wood ya jefa kwallo a ragar Watford
Aubameyang ya kai wani mummunan hari a cikin yadi na 18 din Southampton.
Ya buga kwallon kuma mai tsaron raga Alex McCarthy ya doke ta waje.