Kwallo biyu, Man United 2-0 Brighton
An kuma tabbatar da kwallo ta biyun ne bayan duba VAR da aka yi ko United ta aikata wani laifi kan ta zira kwallon.
Muna kawo maku sharhi da rahotanni kai-tsaye game da wasannin kwallon kafar Ingila na Premier League.
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
An kuma tabbatar da kwallo ta biyun ne bayan duba VAR da aka yi ko United ta aikata wani laifi kan ta zira kwallon.
Wolves na ta kokarin ganin ta jefa kwallo yayin da Raul Jimenz ya watse a sama sai dai kwallon ta bude da yawa.
Mc Tominy ne ya ci kwallon amma fa sai da VAR ta duba ta saboda ana tunanin Harry Maguire ya taba kwallon da hannunsa.
Pereira ne ya buga kwallon ta bigi jikin dan bayan Brighton, abin da ya hana golan Brighton din yin komai domin tare ta.
Wannan ce kwallonsa ta uku ga United
Rashford ya dada kwallo mai kyau ga mai tsaron ragar Brighton Mathew Ryan sai dai golan ya kame ta.
Shot na-ci na gfarko kenan a wasan.
Da yake hira da BBC Sport Ole Gunnar Solskjaer ya ce, "Brandon ya na kokari duk lokacin da aka sa shi a kwallo don haka yana da kyau a gwada shi a karon farko, mun fara gwada shi ne a ranar Alhamis domin ya shiruya wa yau"
"Munyi Matukar kokari a Carabao da Europa, mu ka kara kokari a wasan Liverpool, kuma gaskiya kokarinmu na Premier ya kara habbaka, samun nasara a yau abu ne mai mahimmanci, sai mu tafi hutun wasannin kulob cikin yanayi mai dadi."

Asalin hoton, Getty Images
Allah sarki Jed Steer, wanda ya fara buga wa Aston Villa wasansa na farko amma amma an sauya shi da Orjan Nyland minti takwas kacal da take wasa.
Abu bai yi dadi ba.
James ya hango Rashford a cikin yadi na 18, ya bugo masa kwallon amma 'yan bayan Brighton sun cilla ta kwana.
Man United ta buga kwanarta ta farko a wasan.
Bayan Mason Greenwood, Brandon Williams shi ne dan wasan Manchester United na biyu da ke tawagar a wannan shekarar wanda aka haifa a shekara 2000.

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ba ta taba rashin nasara ba a gida a wasa 11 da ta buga da Brighton a kowacce gasa.
Sau daya ne kacal Brighton ta taba samun maki daya a hannun Manchester United a wasanni da suka buga: sun yi canjaras daya a Old Trafford a 1983.
Graham Potter ya yi sauyi biyu cikin kungiyar daga ‘yan wasan da suka buga wasan Norwich, ya sanya Shane Duffy da Leandro Trossard suka maye gurbin Adam Webster da Pascal Gross.
Yan wasa: Ryan, Montoya, Duffy, Dunk, Burn, Trossard, Propper, Stephens, Alzate, Maupay, Connolly.
Yan benci: Button, Gross, Balogun, Murray, Mooy, March, Schelotto

Asalin hoton, BBC Sport
Williams zai buga wa Manchester United wasan farko a Premier.
Sauyi daya aka samu a bangaren United daga cikin ‘yan wasan da suka buga mata wasan Bournemouth, shi ne matashin yaro mai shekara 19 Brandon Williams wanda zai fara buga wasan farko a Premier ya kuma maye gurbin Ashley Young ne da aka dakatar.
Yan wasa: De Gea, Wan-Bissaka, Lindelof, Maguire, Williams, McTominay, Fred, Pereira, James, Rashford, Martial.
Yan benci: Romero, Jones, Mata, Lingard, Rojo, Greenwood, Garner.

Asalin hoton, BBC Sport
Masu bibiyarmu barkanku da rana ta biyu ta wasannin Premier.
Umar Mikail da Buhari Muhammad Fagge ne gaishe ku. To me za mu jira?
Sai mu fara abin da ya kjawo mu kawai.