GOAL '65, Man United 3-1 Brighton
Rashford ya jefa kwallo ta uku, a iya cewa ya zamarwa United madogara,
Muna kawo maku sharhi da rahotanni kai-tsaye game da wasannin kwallon kafar Ingila na Premier League.
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Rashford ya jefa kwallo ta uku, a iya cewa ya zamarwa United madogara,
An girke wani kwamitin tarar motocin 'yan wasa tare da yi musu barka da zuwa a kofar shiga filin wasa na Anfield.

Asalin hoton, rueters
'Yan sandan Merseyside a wannan makon za su yi aiki tare da Liverpool da Manchester City domin tabbatar da magoya baya sun kalli kwallo cikin aminci da jin dadi.
An dauki matakin hakan ne bayan korafin da City ta yi na gudun kar a maimaita abin da ya faru a shekarar da ta gabata, da aka kai farmaki motar 'yan wasanta.
Kyaftin din Brighton ne Lewis Dunk ya yi tsalle tsakanin 'yan bayan United ya saka mata kai bayan an bugo kwana.
Fred ya kai wani, tun daga kusan yadi na 25 ya dada wa Bryan kwallo kuma da kyar golan ya sake kamo kwallon bayan ya sake ta ta fadi kasa
An bai wa Steve Williams katin gargadi bayan ya yi wa Steven Alzate wata keta mai kama da kong fu.
Da farko sai da VAR ta duba ketar tukunna ko da abin ya kai girman jan kati amma sai ta ce yalon kati ne.
Harry Maguire ya fito daga layyin bayan United har ya zo kusa da yadi na 24 ya dada kwallo. Sai dai ta daki jikin dan wasan Brighton ta fita kwana.
United ta buga kwanarta ta biyar a wasan
Har Man United ma ta bugo kwana - ta hudu kenan a wasan
United ta fi kowacce kungiya amfana da kwallon da abokan wasanta ke cin gida a Premier. Hakan ya faru ga United sau biyar sama da kowacce kungiya a Premier.
A minti na 19 ne D. Propper ya ci gida bayan Harry Maguire da Mc Tominay sun saka masa matsi a gaban ragar Brighton.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
A iya cewa Wolves na yadda ta saba wajen buga kwallo a kasa da kai kora don nuna jajircewa da kuma tsayawa kan neman sakamako a karshen wasa.
Masu masaukin baki na jan ragamar wasan a filin wasa na Molineux
An tafi hutun rabin lokaci yau dai United abin sai san barka, da haka suke kokari da wasu daga magoya bayansu ba su rika tafiya hutu ba.
Brandon Williams na kokari sosai magoya bayan kungiyar ba za su yi korafi kan dan wasan ba.
Idon da wanda zai yi korafi shi ne dan wasan gaban Brighton Neal Maupay, wanda ya fusata da yadda yaron ke danne shi ya fitar da kwallo waje.
Ruben Neves ya jefa kwalo a ragar Aston Villa.
An bai wa Rashford katin gargadi bisa keta da ya yi wa Mantoya - da ma dazu shi ma Mantoya ya yi masa ketar. Ban sani ba ko ramawa ya yi.
James fa yau yana kokarin kawo kwallo daga bangaren dama. Da da tsautsayi da tuni Rashford ya kara ta uku, sai dai 'yan baya sun yi aikinsu sun figtar da ita kwana.
Wolves na neman a ba ta finareti lokacin da Matt Targett, wanda yau ba ya kokari, ya kayar da Matt Doherty... Babu finareti, in ji lafari.
Manchester United ta fi son ta ga kwallo a kafar Marcus Rashford ko da yaushe, kuma za a iya ganin dalilin cewa shi ne ya fi kowa saurin zuwa raga, shi yake haddasa duk wata matsala ga Brighton.
Rashford na kwance a tsakiyar fili bayan ya yi taho-mu-gama da Shane Duffy.
An bai wa Mantoya katin gargadi bayan ya fyalli Macos Rashford.
Cikin minti biyu kacal United ta ci ta biyu. Wannan sakamakon ya mayar da Man United mataki na bakwai a teburi amma fa sai idan an tashi a haka.
Ko za a tashi hakan? Ko za ta kara? Muna nan dai muna zuba ido.

Asalin hoton, Getty Images