Liverpool 2-0 Man City, Liverpool 2-0 Man City
Liverpool da ci City da buga kwallo
Muna kawo maku sharhi da rahotanni kai-tsaye game da wasannin kwallon kafar Ingila na Premier League.
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Liverpool da ci City da buga kwallo
kwana ta 5 amma babu wacce ta shiga.....
Van Dijk a ba shi da damuwa a wasan. Don City ba su kai kora cikin yadi na 18.
City ta kara matsa lamba domin zare kwallonta
Angelino ya buga ta daki turke
Aguero ya shaka wa Allison kwallo mai zafi a cikin yadi na 18. Bai iya kamata ba sai turewa.
Liverpool na taba kwallo cikin salo mai kayatarwa.. City dole su yi hakuri har suma su samu damar hakan.
A bude ake wasan babu jin tsoro babu wanda ya koma baya..... Liverpool za ta dauko kwana ta farko a wasan.
Kocin City ya ki zama wuri daya.. wannan dai abin da ba a taba kawowa zai faru bane cikin minti 12 an zira kwallo biyu..
Abu kamar mafarki, Ana ta yiwa Sterling ihu a duk fadin filin wasa.
Liverpool na son tabbatar da cewa da safe ake kamun fara.. Ko City za ta iya farkewa wannan shi ne abin da masu kallo za su so ganin kan karshen wannan karawa mai cike da kalubale.
Mo salah ya jefa kwallo ta biyu.
Robertson ne ya hango shi yana tikar gudu a gefen dama kuma ya shilla masa ita, inda shi kuma bai yi wata-wata ba ya saka mata kai kuma sai a ragar Bravo.
Wannan wasa ba irin na kullum ba ne.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
City ta kara samun bugun tazara.
Liverpool na kara samun wurin zama daram a teburin Premier. maki 9 ne yanzu haka tsakaninta da City. kuma in aka tashi a haka City ta koma ta 4 a teburi.
Fabinho ya jefa kwallon farko daga kusan yadi na 24. Liverpool na kan gaba kuma da alama sai kun gyara zama domin irin wadannan wasannin ba a fiya tashi ba tare da ruwan kwallaye ba.
De Bruyne ya bugo anma ta fita kwana.
Wake da shewa ne kawai ke tashi a filin wasa na Anfield.
City ce kungiya ta karshe da ta ci Liverpool a Premier kwanaki 311 da suka gabata.
Kusan duka kungiyoyin da ke Premier sun dogara ne kan wannan wasan, babu wata kungiya da ake ganin za ta iya takawa Liverpool birki a bana in ba City ba. idan har ta cinye Liverpool a yau hakan zai bai wa sauran kungiyoyi damar jarraba sa'arsu a wata mai kamawa da ake yawan buga wasanni.