Liverpool ta bayar da tazarar maki 8 a saman teburi

Muna kawo maku sharhi da rahotanni kai-tsaye game da wasannin kwallon kafar Ingila na Premier League.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Liverpool 3-0 Man City, Liverpool 3-0 Man City

    Wasan ya bude kowa na kai kora babu jin tsoro.

  2. Ana yi wa Sterling ihu, Liverpool 3-0 Man City

    Har yanzu magaoya bayan Liverpool ba su daina yi wa Sterling ihu ba, kuma fa a hakan ma sun ci wasa kenan. Me zai faru kenan da su ake ci?

  3. Katin gargadi ga Rodri, Liverpool 3-0 Man City

    Rodri ya karbi katin gargadi.

  4. Liverppol ta yi canji, Liverpool 3-0 Man City

    Henderson ya fita Milner ya shigo tare da karbar kambun kaftin.

  5. Liverpool 3-0 Man City, Liverpool 3-0 Man City

    Ana ta yi wa Pep ihu amma bai damu ba. Yana ta karawa yan wasansa karfin gwiwa na ganin sun rama kwallon da aka ci.

  6. Liverpool 3-0 Man City, Liverpool 3-0 Man City

    Liverpool ta hana City ta rika samun dama har takai da ta rama ko da kwallo daya daga cikin kwallon da aka ci ta.

  7. Man City, Liverpool 3-0 Man City

    Aikin ya kara kwabewa City ina mafuta?

  8. Manchester City, Liverpool 3-0 Man City

    Wanene ya yi saura akwai Agüero akwai Sterling akwai De Bruyne...

  9. Sterling, Liverpool 3-0 Man City

    Sterling ya fara motsi kamar yadda ya kamata.

  10. Liverpool 3-0 Man City, Liverpool 3-0 Man City

    Abin da ake gudu ya faru anya City za ta farfado daga baccin da take?

  11. GOAL '50 Maneeeeeee, Liverpool 3-0 Man City

    Mane ya kara ta uku...

  12. Mane, Liverpool 2-0 Man City

    Yau dai Mane ya buya a wasan ba kamar yadda yake motsi ba a wasannin baya.

  13. Liverpool 2-0 Man City, Liverpool 2-0 Man City

    Da alamun City ta dawo da karfinta. Amma abin gudun shi ne kar ayi irin na wasan Wolves da Aston Villa su fita neman ci a karshe a zo a kara musu wata kwallon.

  14. Mo Salah da abokan aikinsa, Liverpool 2-0 Man City

    Mo Salah da abokan aikinsa ba za su huta ba sai sun tabbatar sun tafi da maki ukun nan domin dai ko ba komai sun san cewa magoya baya Premier League ne kawai a gabansu.

    Mo Salah

    Asalin hoton, Getty Images

    Tawagar Liverpool

    Asalin hoton, Getty Images

  15. An dawo wasa, Liverpool 2-0 Man City

    Duka bangarorin sun dawo cikin karsashi da kwarin gwiwa.. Liverpool na son kare kwallon da ta ci yayin da City ke neman farke kwallon da aka zira mata.

    Idan City ta sake aka tashi haka to babu mamaki Liverpool ta dauki kofin Premier. Wa ya sani ne!

  16. Pep, Liverpool 2-0 Man City

    Pep Guardiola ya zaku a dawo ga shi nan a tsaye na jiran yan wasa su fito a ci gaba da wasa.

  17. Gary Lineker, Liverpool 2-0 Man City

    Leicester ce kawai za ta iya cinye Liverpool a yanzu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. Hutun rabin lokaci, Liverpool 2-0 Man City

    Liverpool na kara tabbatr da matsayinta na babu wanda ya cinye ta a Premier bana, City na tsaka mai wuya ko don wajenta da za ta rasa a teburin gasar ta koma matsayi na 4.

    Menene zai faru a rabin lokaci na biyu? sai mun gani ku kasance tare da mu har karshen wasan.

    Fabinho

    Asalin hoton, @LFC

    Bayanan hoto, Fabinho ne ya bude wasan da wata kwallonsa mai kama da harbin bindiga
  19. Anfield ta dau sowa, Liverpool 2-0 Man City

    Filin wasa na Anfield ya harke da sowa yayin da kungiyoyin ke saka wa juna matsi.

    Ana iya cewa ba a san maci tuwo ba gaskiya duk da cewa Man City ta fi taka rawa.

  20. Liverpool 2-0 Man City, Liverpool 2-0 Man City

    Fernandinho ya kwace kwallo mai kyau a hannun Salah.. da alama kuma Salah ya bugu a kafarsa ga shi nan dai a kwance.