Liverpool ta bayar da tazarar maki 8 a saman teburi

Muna kawo maku sharhi da rahotanni kai-tsaye game da wasannin kwallon kafar Ingila na Premier League.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Man United ta cinye Brighton, ta koma ta 7, Man Utd 3-1 Brighton

    Manchester United ta lallasa Brighton 3-1 a wasan Premier mako na 12 a filin wasa na Old Trafford.

    Sakamkon ya sa Manchester United ta gangaro zuwa mataki na bakwai a teburi da maki 16, maki tara kenan tsakaninta da 'yan hudun farko.

    Pereira ne ya fara saka masu masaukin bakin a gaba da kwallon da ya ci a minti na 17 bayan ya buga ta ta daki jikin dan bayan Brighton, abin da ya hana mai tsaron raga Bryan tabuka komai domin hana ta shiga.

    Sai kuma D. Propper na Brighton da ya ci gidansu a minti na 19 bayan Harry Maguire da Scott Mc Tominay sun saka masa matsi a bakin ragarsu.

    Hakan ya sa Man United ta zama kungiyar da ta fi kowacce amfana da kwallon da abokan wasanta suka ci gida har sau biyar sama da kowacce kungiya a Premier.

    Marcus Rashford bai yi kasa a gwiwa ba sai da ya saka tasa a minti na 66. Anthony Martial ne ya taimaka masa, inda ya ba shi kwallo a cikin yadi na 18, shi kuma ya dada ta har sai da ta bigi tirke kafin ta kwanta.

    Wannan nasara za ta saukaka wa mai horarwa Ole Solskjaer ganin irin yadda kungiyar ta yi ta fama da sakamako maras dadin ji a 'yan makonnin nan.

    Martial da Rahsford

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Liverpool, Liverpool v Man City 5:30

    Shima kocin Liverpool ya yi canji 4 daga yan wasan da suka buga wa kungiyar wasan Champion wanda ta cinye Genk. An sanya Andy Robertson, Jordan Henderson kuma zai shigo tsakiya, Roberto Firmino da Sadio Mane kuma su buga a gaba.

    YAn wasa :Alisson, Alexander-Arnold, Lovren, van Dijk, Robertson, Henderson, Fabinho, Wijnaldum, Salah, Firmino, Mane.

    Yan benci :Milner, Keita, Gomez, Adrian, Oxlade-Chamberlain, Lallana, Origi.

    Liverpool

    Asalin hoton, BBC Sport

    Bayanan hoto, Liverpool
  3. Manchester City, Liverpool v Man Cty 5:30

    Canji shida City ta yi daga yan wasan da suka buga mata wasan Champion wanda ta yi canjaras da Atlanta a tsakiyar mako.

    John Stones aka hada da Fernandinho a tsakiyar bayan, tare da Kyle Walker da kuma Angelino. Rodri kuma yana tsakiya.

    Yan wasa :Bravo, Walker, Stones, Fernandinho, Jose Angelino, De Bruyne, Rodri, Gundogan, Bernardo Silva, Aguero, Sterling.

    Yan benci :Gabriel Jesus, Silva, Mahrez, Joao Cancelo, Otamendi, Carson, Foden.

    Manchester City

    Asalin hoton, BBC Sport

    Bayanan hoto, Manchester City
  4. A shirye kuke domin bibiyar bayanai kan wasa mafi kalubale a Premier ta bana?, Liverpool v Man City 5:30

    Duk da cewa duka suna kokari amma a yanzu babu wanda ya ci wasanninsa uku na baya a jere.

    Klopp da Guardiola

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Klopp da Guardiola
  5. Gaba dai gaba dai Raul Jimenez, Wolves 2-1 Aston Villa

    Kwallo 14- Raheem Sterling ne kawai ya zira kwallo a kowacce gasa a cikin duka 'yan wasan Premier a bana, sama da dan wasan gaban Wolves Raul Jimenez da ya ci kwallo 13.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Manchester United, Man Utd 3-1 Brighton

    Nasara mai cike da nishadi, United ta dawo ta 7 a teburin Premier.

  7. An tashi, Man United 3-1 Brighton

    Duk da barin damar da United ta yi ta kai bantenta.

  8. An tashi, Wolves 2-1 Aston Villa

    Kwallo da Villa ta ci a makare ba ta kara mata komi ba.

  9. Martial ko Rashford!, Man United 3-1 Brighton

    Du ranar da suka yi kokari abin yana yi wa United dadi. Wa za a bai wa gwarzon wannan wasa a cikinsu?

    Rashford: Ya ci 1, ya buga shot 7, ya yi fasin sau.

    Martial: Ya taimaka an ci kwallo biyu, ya yi shot 3, ya yi fasin sau 17.

    Matial da Rashford

    Asalin hoton, Getty Images

  10. GOAL '90, Wolves 2-1 Aston Villa

    Trezeguet yau ma ya kara ci wa Aston Villa kwallo,

  11. United ta yi canji, Man United 3-1 Brighton

    Marcus Rashford da Brandon Williams sun fita. Marcos Rojo da Mason Greenwood sun shiga

  12. GOAL '86, Wolves 2-0 Aston Villa Raul Jimenez

    Raul Jimenez ya kara kwallo ta biyu, Aston Villa garin neman gira an rasa ido.

  13. Wolves 1-0 Aston Villa, Wolves 1-0 Aston Villa

    Aston Villa ta kara matsawa sosai, yadda duk 'yan wasanta suka fito domin samun ko maki daya ne a hannun Wolves, suna ta kai kwallo cikin yadi na 18, sai dai masu masaukin bakin a nutse suke cire kwallon ba tare da tashin hankali ba.

  14. Man United 3-1 Brighton, Man United 3-1 Brighton

    Kasa da minti 10 ne ya yi saura a wasan, United na ci gaba da jan ragama, sai dai ta na wasa da damar da take samu ta kara kwallo.

  15. Bugun tazara, Man United 3-1 Brighton

    Fred ya buga bugun tazara a wuri mai hadari, sai dai bugun nasa babu hadari. Kwallo ta fita waje.

  16. Wolves 1-0 Aston Villa, Wolves 1-0 Aston Villa

    Aston Villa na nuna damuwa ga Tyrone Mings da ya fadi kasa, da alamun yana cikin yanayi mara dadi. tuni dai Villa ta kammala canjinta 3 sai dai anyi sa a Mings zai iya ci gaba da wasan.

  17. Rashford ya kwallafa, Man United 3-1 Brighton

    Marcus Rashford ya shigo da kwallo cikin yadi na 6 ta bangaren hagu amma ya hana kowa ya ce sai ya ci alhalin golan ya tare bangaren.

    An dai yi asarar wannan kwallo.

  18. Katin gargadi ga Pröpper, Man United 3-1 Brighton

    Katin gargadi na 5 kenan da aka bai wa Brighton a yau.

  19. Old Trafford ta barke da sowa, Man United 3-1 Brighton

    Filin Old Trafford fa ya dau sowa, Man United na yin abin da suka yi ta marari a makonnin da suka gabata.

    Zuwa yanzu ta buga shot 13 kuma 7 daga ciki na-ci ne (on target). Brighton kuma 6 ta buga biyu daga ciki na-ci ne.

  20. Wolves 1-0 Aston Villa, Wolves 1-0 Aston Villa

    Wolves na neman kara kwallo ta biyu domin tabbatar da nasararta a filin wasa na Molineux, yayin da Raul Jimenez ya kai wani hari sai dai kwallon ta yi sama sosai.