Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An gano maganin hana coronavirus yaduwa

Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya har da rahotanni kan coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Dahiru Bauchi ya yi tsokaci kan cire Sarki Sanusi II

    Babban malamin addinin musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi kira ga al'ummar jihar Kano su kwantar da hankalinsu kuma su yi hakuri bisa sauke Sarki Muhammadu Sanusi II da gwamnatin jihar ta yi.

    Malamin ya yi addu'ar Allah ya kawo sauki cikin lamarin kuma ya kiyaye mutane.

    Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wa Sarki addu'ar Allah Ya sa wannan mataki ya zama alkhairi a gare shi.

  2. An dauke Sarki Sanusi daga Loko

    Wakilan BBC da suka kai ziyara kauyen Loko na jihar Nasarawa da ke Najeriya, inda aka fara kai Sarki Muhammadu Sanusi II bayan sauke shi daga sarautar Kano ranar Litinin, sun tabbatar da cewa an dauke sarkin zuwa garin Awe.

    A lokacin da wakilan namu suka isa garin, sun ga jirgi mai saukar ungulu ya tashi kuma sun tabbatar ya dauki sarkin zuwa garin Awe duk a jihar Nasarawa.

  3. Kalli bidiyon fitowar Aminu Ado Bayero don yin rangadi a Kano

  4. Mutum biyu sun kamu da coronavirus a Burkina Faso

    Ma'aikatar lafiya a Burkina Faso ta tabbatar da bullar cutar coronavirus - karon farko da cutar ta bulla a kasar.

    Mutanen biyu da suka kamu da cutar ma'aurata ne da a watan Fabrairu suka koma kasar daga Faransa, kamar yadda ministar lafiyar kasar Claudine Lougue ta fada wa 'yan jarida. Mutumin dan shekara 73 ne sai mai dakinsa da take 57.

    An tabbatar sun kamu da cutar ranar Litinin kuma tuni aka kebe su, a cewar hukumomin kasar.

    Mutum na uku da aka rawaito ya yi mu'amala da ma'auratan shi ma an kebe shi. Burkina Faso ce kasa ta shida a yankin kudu da hamadar Sahara da cutar ta bulla.

  5. Fitowar sabon Sarki Aminu Ado Bayero

    Bayanai daga Kano a arewacin Najeriya na cewa Hakiman masarautar Kano da suke 'yan gaban goshi a wajen tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II sun yi wa sabon sarkin da gwamnati ta sanar mubaya'a.

    Wakilin BBC a Kano ya rawaito sabon Sarkin na shirin kai wa mahaifiyarsa ziyara a gidanta da ke Gandu daga nan kuma ya wuce gidansa da ke Nassarawa.

    Daga cikin wadanda suka yi wa sabon Sarkin mubaya'a akwai Makaman Kano da Wazirin Kano da Madakin Kano da kuma Dan Amar Din Kano.

    Tuni dai rahotanni suka ce jami’an tsaro sun kai Muhammadu Sanusi II garin Loko da ke jihar Nassarawa.

    An sauke Muhammadu Sanusi II a gidan limamin garin inda jami’an tsaron suka koma bayan sun sauke shi.

  6. An kama masu satar mutane a Ghana

    Rundunar `yan sandan Ghana reshen jihar Ashanti ta tabbatar da kama mutum goma sha biyu da ake zargi da aikata fashi da makamai da kuma satar mutane don neman kudin fansa wadanda suka addabi wasu al`ummar Fulani makiyaya a wasu kauyukan jihar.

    Hukumomi sun ce nan gaba kadan ne za a gurfanar da mutanen su 12 a gaban kuliya.

    Rundunar ta ce a 'yan shekarun nan, jihar Ashanti na fama da masu satar mutane don neman kudin fansa kuma ta bukaci duk wani wanda ya ke da bayani kan masu aikata laifin su taimaka wa rundunar.

  7. Sarki Sanusi ya kwana kauyen Loko

      • Marubuci, Yusuf Tijjani
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

    Rahotanni daga kauyen Loko na jihar Nassarawa sun ce jami’an tsaro sun kai Muhammadu Sanusi II garin da misalin karfe 3 na daren Litinin.

    An sauke Muhammadu Sanusi II a gidan limamin garin inda jami’an tsaron suka koma bayan sun sauke shi.

    Wata majiya ta tabbatarwa BBC cewa babu wani daga cikin iyalan tsohon Sarkin a lokacin da aka kawo shi kauyen na Loko.

    Jim kadan kafin dauke shi daga cikin fadar masarautar Kano, tsohon sarkin ya yi jawabi mai sosa rai inda ya ce ya dauki kaddara ya kuma bukaci a yi wa sabon sarki mubaya'a.

  8. Cire Sarki Sanusi II: Buhari ya yi gum da bakinsa

    Kusan sa'o'i 24 bayan sauke Sarki Muhammadu Sanusi daga karagar mulki, har yanzu Shugaba Muhammadu Buhari bai ce uffan ba a hukumance kan batun.

    Sai dai Gwamnatin Najeriya ta karyata rahotannin da ake yadawa a shafukan sada zumunta da ke cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana kan sauke Sarki Muhammadu Sanusi II.

    Mai taimaka wa shugaban kan kafafen yada labarai Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a Twitter inda ya ce labarin da jaridar ta intanet ta wallafa mai taken '' ba ni da masaniya an cire Sanusi, wa ya cire shi?" ba gaskiya ba ne.

    Ya bukaci 'yan kasar su yi watsi da labarin wanda ya ce na kanzon kurege ne.

    A ranar Litinin ne gwamnatin Kano ta sanar da cire Sarki Muhammadu Sanusi II daga kan karaga tare da maye gurbinsa da Aminu Ado Bayero.

  9. Ana shirin gudanar da zanga-zanga kan almundahana a ma'aikatar tsaro

    Hadin gwiwar FP, jam'iyyun siyasa masu adawa na bangaren Front Patriotique a jamhuriyar Nijar sun yi kira ga magoya bayansu da su zauna cikin shiri don gudanar da zanga-zangar nuna kin amincewa da almubazzaranci da dukiyar kasa a ma'aikatar tsaro.

    Gungun 'yan adawar na FP dai ya nemi magoya bayan ko wane bangare su amsa kiran da kungiyoyin farar hula suka yi na fita zanga-zanga ranar Laraba.

    Mataimakin shugaban gungun jam'iyyun adawa na bangaren FP kuma dan majalisar kasa daga jam’iyar MPN Kiishin Kasa Honorable Masani Korone a cikin wata hira da BBC ya tabbatar da cewa basu da wata fargaba kan irin yunkurin da su ke yi don ganin kasar ta ci gaba .

    Ya kuma kara da cewa za su yi dukkan kokarinsu don ganin cin hanci da rashawa basu mamaye Nijar ba.

    Dan majalasar ya furta cewa dole ne su bi kadin kudin kasa da aka sace kuma jama’ar kasa su sani sai sun tashi tsaye domin samar wa kansu 'yanci da walwala a mulkin demokaradiya a kasar ta Nijar.

  10. Wani da ake zargin yana dauke da coronavirus ya tsere daga asibiti

    A wata sanarwa, ma'aikatar lafiya a Zimbabwe ta tabbatar da cewa wani mutum da ake zargin yana dauke da coronavirus ya tsere daga asibiti kafin a yi masa gwaji.

    Mutumin mai shekara 26 ya shiga Zimbabwe ne a watan Fabrairu daga Thailand kuma ya fara zazzabi da atishawa. Bayan da mutumin ya tsere an bi shi gidansa don kamo shi amma ba a yi nasara ba kuma an bukaci jami'an 'yan sanda su nemo shi.

    Kawo yanzu dai, alkaluma sun nuna cewa an samu masu dauke da cutar 100 a fadin Afirka.

    Su ne:

    • Masar - 55
    • Algeria - 20
    • Afirka ta Kudu - 7
    • Tunisia - 5
    • Senegal - 4
    • Maroko - 2
    • Kamaru - 2
    • Burkina Faso - 2
    • Najeriya - 2
    • Togo - 1
  11. Kungiyar malaman jami'o'i a Najeriya sun fara yajin aiki

    Kungiyar malaman jami'o'i a Najeriya ta fara yajin aiki na makonni biyu.

    Kwamitin zartarwar kungiyar ne ya ayyana yajin aikin bayan zaman da ya yi a Enugu ranar Litinin.

    Shugaban kungiyar Biodun Ogunyemi ya sanar da fara yajin aikin a Enugu kamar yadda wasu kafofin yada labaran kasar suka ruwaito.

    Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kungiyar ta ce ta yanke shawarar fara yajin aikin ne bayan matakin da gwamnatin Najeriyar ta dauka na dakatar da albashin malaman da ba su shiga tsarin albashin gwamnati na bai daya na IPPIS ba.

    Haka kuma, rahotanni sun nuna cewa ASUU na fatan yajin aikin zai zaburar da gwamnati ta sa hannu kan yarjejeniyoyi da kungiyar ta yi da gwamnatin a shekarun 2009 da 2013 da 2017.

  12. Wane ne Aminu Ado Bayero, sabon Sarkin Kano?

    An haifi Alhaji Aminu Bayero a kwaryar birnin Kano ranar 21 ga watan Agusta, 1961, gabanin mahaifinsa Ado Bayero ya zama sarkin Kano da shekara biyu.

    A 1990 mahaifinsa Alhaji Ado Bayero ya fara ba shi mukamin sarauta, inda aka nada shi Dan Majen Kano kuma Hakimin Nassarawa.

    Daga nan ne kuma aka kara masa girma zuwa Dan Majen Kano Hakimin Gwale a dai shekarar ta 1990.

    A shekrar 1991 kuma likkafa ta kara gaba inda aka nada shi Turakin Kano kuma Hakimin Dala a watan Janairun 1991 zuwa Janairun 2001, ma'ana dai ya shekara 10 a wannan mukami.

    Alhaji Aminu Ado Bayero ya zama Sarkin Dawakin Tsakar Gida, Hakimin Dala daga watan Janairun 2001 mukamin da ya rike har zuwa 2014.

    A watan Oktobar 2014 Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya nada shi a matsayin Wamban Kano kuma dan majalisar sarki. Ya rike mukamin har zuwa watan Mayun 2019.

    A watan Disambar 2019 ne kuma Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nada shi Sarkin Bichi na farrko bayan kirkirar sabbin masarautu.

    Ku karanta cikakken tarihin sabon Sarkin Kanon a nan.

  13. An wayi gari da sabon sarki a Kano

    Al'umar jihar Kano sun tashi yau da sabon Sarki, Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda ya maye gurbin Sarki Muhammadu Sanusi II.

    Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya cire Sarki Sanusi II sannan ya nada Aminu Ado Bayero bisa abin da ya bayyana dalilai na "rashin biyayya".

    Matakin da gwamnan ta dauka bai zo wa mutane da dama da mamaki ba, ganin cewa an shafe shekaru ana zaman doya da manja tsakanin Ganduje da tsohon Sarkin.

    Ba abin mamaki ba ne yadda Ganduje ya tsige Sanusi sannan ya yi sauri ya bayar da sanarwar nada sabon sarki kafin kotu ta shiga lamarin. Masu kula da al'amura sun tsammaci faruwar hakan.

    Amincewar da Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi na karbar sarautar Bichi, duk da cewa 'yan uwansa sun gargade shi cewa bai kamata ya taimaka wurin kacaccala masarautar Kano ba, hakan ya dadada wa Ganduje, domin kuwa ya karfafa gwiwar gwamnan.

    Tsohon Sarkin ya yi jawabin ban kwana ga al'umar jihar Kano inda ya dau kaddara sannan ya bukace su, su yi biyayya ga sabon sarki:

  14. Barka da war haka

    Da fatan kun wayi garin Talata lafiya, kuma barkamu da sake kasancewa a wannan shafi mai kawo maku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da makwabtanta kaman Nijar da Ghana da Kamaru har ma da wasu kasashen duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu a yau!

  15. Takaitaccen tarihin masarautar Kano

    Masarautar Kano tana cikin manyan masarautu a kasar Hausa a yammacin Afirka.

    Tarihi ya nuna tsohuwar masarauta ce da aka kafa shekaru aru-aru tun zamanin jahiliyya kafin zuwan addinin Islama.

    Masarautar ta taimaka wajen bunkasa garin Kano da Arewa da ma Najeriya baki daya.

    Garin Kano ya kasance cibiyar kasuwanci a yankin arewacin Najeriya da Jamhuriyyar Nijar da ke makwabtaka da garin.

    Asalin Kalmar 'Kano'

    Mutanen da suka fara zama a Kano makera ne da suka tashi daga garin Gaya domin neman kasa mai arzikin tama, wacce za su sarrafa su yi karfe da ita.

    Mutanen sun yi dace da samun kasar mai kunshe da sinadarin tama, sannan kuma mai albarkar noma da ruwa da dazuzzuka da za a iya yin farauta.

    Wajen ya kuma kasance mai matukar tsaro kasancewar akwai manyan duwatsu da tsaunuka, da mutane za su iya hawa su fake idan an kai musu hari.

    Duwatsun su ne dutsen Dala da Goron Dutse da Fanisau da Jigirya da Magwan.

    Akwai kuma koguna daban-daban da suka kewaye yankin, da suka hada da kogin Jakara, da kuma kogin Kano.

    Hakan ya sa mutane da dama suka ringa yin kaura zuwa yankin domin zama.

    Karanta cikakken tarihin masarautar a nan.

  16. An tafi da Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi II jihar Nasarawa

    Bayanai daga jihar Kano na nuna cewa an tafi da Sarki Muhammadu Sanusi II jihar Nasarawa inda zai zauna.

  17. Aminu Ado Bayero ne sabon sarkin Kano

    Masu zabar sarki a Kano sun zabi Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano na goma sha biyar.

    Aminu Ado Bayero dai da ne ga marigayi tsohon Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero.

  18. Kai Tsaye- Bayyana sabon Sarkin Kano

  19. Masu zabar Sarkin Kano a gidan gwamnati

    Masu zabar Sarkin Kano a gidan gwamnatin jihar Kano, wajen da za a bayyana sabon sarki.

    • Masu zabar sarkin sun hada da:
    • Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani
    • Makaman Kano, Alhaji Sarki Abdullahi
    • Sarkin Dawaki Mai Tuta, Alhaji Bello Abubakar
    • Sarkin Bai, Alhaji Mukhtar Adnan
  20. Ana shirin bayyana sabon sarki a Kano

    A yanzu haka ana shirin bayyana sabon sarki a jihar Kano bayan tsige Muhammadu Sanusi II.