Kafatanin wasannin hukumar kwallon kafar Turai ta Uefa da suka hada da Champions League da Europa League, wadanda za a buga a mako mai zuwa, an dage su saboda coronavirus.
Taron raba kungiyoyi a gasar Europa da za a yi ranar 20 ga watan Maris ma an dage shi.
A gasar Champions League, wasannin da aka dakatar sun hada da Manchester City v Real Madrid, Juventus v Lyon, Barcelona v Napoli da Bayern Munich v Chelsea.
A Europa kuma, an dage wasannin Manchester United da na Wolves da Rangers.
Su ma wasannin matasa na gasar Uefa Youth League da za a yi ranar 17 da 18 ga Maris an dage su.
Uefa ta ce za ta bayyana ranakun da za a buga wasannin da aka dage din "a lokacin da ya dace".
Hukumar ta gayyaci wakilai daga kungiyoyi 55 kawayenta zuwa wata ganawa a ranar Talata domin tattauna matakin da za a dauka kan annobar coronavirus.
Za a tattauna batun dage gasar kasashen Turai ta Euro 2020 a wurin taron.
Sama da mutum 125,000 ne aka gano suna dauke da cutar coronavirus a kasashe 118 a fadin duniuya, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya.
Wadanda suka mutu kuma sun zarta 4,600.