Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An gano maganin hana coronavirus yaduwa

Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya har da rahotanni kan coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Shugaba Buhari a Kebbi

    Da safiyar yau Alhamis Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Kebbi don halartar taron baje-kolin kayan amfanin gona.

    Taron wani bangare ne na shirye-shiryen bikin kamun kifi na Argungu.

    Ana gudanar da bikin na al'ada a jihar ta Kebbi da ke arewa maso yammacin kasar.

  2. Magufuli ya biya tara ga dan hamayya

    Shugaban Tanzania John Magafuli ya biya tarar da aka kakaba wa daya daga cikin jagororin hamayya domin ba shi damar shakar iskar 'yanci.

    Shugaba Magafuli ya biya sama da $16,500 kwatankwacin sama da naira miliyan bakwai da rabi ga Peter Msigwa, daya daga cikin 'yan siyasa na jam'iyyar Chadema da aka yanke wa hukuncin biyan sama da $150,000 ko kuma su je gidan yari na tsawon wata biyar.

    Ya kamata Mr Msigwa ya biya sama da $17,000.

    Tun da farko, an saki wasu 'yan siyasa uku daga jam'iyyar ta Chadema da aka tsare a kurkuku bayan da magoya baya suka tattara kudaden biyan tarar.

    Labarin biyan makudan kudaden da Shugaba Magafuli ya yi ya zo wa da 'yan kasar da mamaki inda wasu ke kira ga jam'iyyar ta ki karbar kudaden.

    ''Ku fada masa cewa mun riga mun biya masa,'' kamar yadda wani mai amfani da shafin Twitter Rich Mwanisanzule ya fada.

    A ranar Litinin ne aka samu 'yan siyasar tara da laifin shirya gangami ba bisa ka'ida ba.

  3. Atiku ya nemi a hana saukar jirage daga kasashe masu coronavirus

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya yi kira ga gwamnatin kasar ta takaita saukar jirage da suka fito daga kasashen da ke fama da annobar coronavirus.

    Atiku ya ba da shawarar ta shafinsa na Twitter inda ya ce shawarar ta yi daidai da matakan da sauran kasashen duniya ke dauka.

    Ya ce ya kamata gwamnati ta dauki irin wannan matakin har sai ta karfafa matakan yaki da cutar.

    Kazalika, Atiku ya kuma nemi gwmanatin ta bude iyakokin kasar da aka rufe ba tare da duba matsayinsu ba.

    A cewarsa, har yanzu, ba a iya gano mutanen da suka shiga jirgi da dan Italiyar da ya kamu da cutar.

  4. Yadda aka kwashe dukiyar Sarki Sanusi II daga Masarautar Kano

    • Mece ce manufar El-Rufa'i ta bai wa Sanusi II Muhammadu mukamai?
    • Kalubalen da ke gaban sabon Sarkin Kano

    Falakin Kano Mai Murabus Mujitaba Abubakar Abba wanda shi ne tsohon babban sakatare na fadar sarki, a wata hira da ya yi da BBC ya ce dan uwan nasa, Muhammad Sanusi ya bar daukacin dawakansa da sauran kayan daki da aka zuba na kawa a gidan sarkin domin amfanin wanda ya gaje shi, sannan sun dauke motocin da suke mallakin tsohon sarkin na Kano.

  5. Ana neman kafa hukumar bunkasa tsakiyar Najeriya

    Dan majalisa mai wakiltar Mazabar Benue ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Abba Moro ya gabatar da kudirin neman kafa hukumar raya yankin Arewa ta Tsakiya a zauren majalisar.

    Sanata Moro ya ce kafa hukumar zai ba da damar bunkasar noma da harkokin kasuwanci da masana'antu.

    'Yan majalisar irin su Sanata Philip Aduda wanda shi ne mataimakin bulaliyar majalisar da Sanata Aliyu Sabi duk sun nuna goyon baya ga kudirin.

    Tuni Shugaban majalisar Ahmad Lawan ya mika kudirin ga kwamitin samarwa da harkokin gwamnati wanda zai ba da rahoto nan da wata daya.

    Najeriya dai na da yankuna shida kuma ya zuwa yanzu akwai hukumomin raya yankunan Neja Delta da Arewa maso gabashin kasar da aka kafa - yankunan da suke fama da masu satar mai da 'yan Boko Haram.

  6. Hotunan yadda aka kwashe litattafan tsohon sarki Sanusi II

    Makusantan tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II sun ce sun kwashe litattafansa daga dakin karatunsa.

    Falakin Kano mai murabus, Mujitaba Abubakar Abba, ya shaida wa BBC cewa litattafan sun kai 42,000 sannan kuma darajarsu ta kai ta naira miliyan 200.

    Ga wasu daga cikin hotunan dakin karatun tsohon sarkin yayin da ake kwashe litattafan.

  7. Ghana ta kara ware $100m don coronavirus

    Ghana ta kara ware wasu kudi kusan dala miliyan 100 don yaki da yaduwar cutar coronavirus a kasar.

    Wannan ya zo ne bayan da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana kwayar cutar coronavirus a matsayin annobar da ta bazu a duniya.

    Shugaba Nana Akufo Addo ya yi jawabi ga 'yan kasar, inda ya ce ya gamsu da irin shirin da jami'an kasar ke yi a bangarori daban-daban don hana cutar shiga kasar.

    Ya ce ana sa ido sosai kan masu shigowa kasar.

    Amma Shugaban ya ce dole ne Ghana ta kara daura damarar ganin cutar ba ta shiga kasar ba, kuma idan ta shiga a samu hannyoyin dakile ta.

  8. Yadda Coronavirus ke yaduwa a duniya da matakan da ake dauka

    Yadda Coronavirus ke yaduwa a duniya da matakan da ake dauka.

    Hukumomi sun tabbatar da cewa zuwa yanzu an samu masu dauke da cutar coronavirus 124,000 a duniya baki daya inda mutum 4,600 suka mutu.

    Hukumar Duniya Ta Duniya WHO sun ayyana ta a matsayin annoba.

    Ga jerin kasashen da masu cutar suka fi yawa a alkaluman baya-bayan nan:

    • China -80,980 masu dauke da ita sai kuma 3,136 da suka mutu
    • Italiya -12,462 masu dauke da ita sai kuma 827 da suka mutu
    • Iran -9,000 masu dauke da ita sai kuma 354 da suka mutu
    • Faransa -2,269 masu dauke da ita sai kuma 48 da suka mutu
    • Spaniya -2,140 masu dauke da ita sai kuma with 49 da suka mutu
  9. Ana zargin jami'an gwamnati da fasa kwabrin jini a Kenya

    Gwamnatin Kenya ta fara wani bincike don gano yadda ake fasa kwabrin jinin da aka bayar gudunmuwa daga kasar zuwa Somaliya.

    Ministan Lafiya a Kenya ya ce akwai yiwuwar cewa akwai wasu jami'an gwamnati da ke da hannu a lamarin.

    Kenya ta dade tana fama da matsalar karancin jini. Amma binciken da ake yi yanzu kan yiwuwar ana sayar da jinin da 'yan kasar ke bayar wa a matsayin gudunmuwa a ciki da wajen kasar, ya gigita mutane a fadin Kenya.

    Wannan ne karon farko da gwamnatin Kenya ta fito fili ta bayyana cewa tsarin kasar na karba da tantance jini na da nakasu.

    Dama can Amurka ce ke tallafa wa tsarin ta fannin kudi tsawon shekaru 15 – duk da cewa Amurka ta dakatar da bayar da tallafin a bara. Tun daga nan ne, kasar ta shiga halin ha'u'la'i kan ma'ajiyar jininta.

  10. An kashe sojin Birtaniya da na Amurka a wani hari makamin roka a Iraki

    An halaka mutum uku, bayan wani harin makamin roka da aka kai kan wani sansani da dakarun Amurka da Birtaniya ke zaune a Iraki.

    A kalla mutum 12 aka raunata a sansanin soja da ke Taji a arewacin Bagadaza.

    Wasu majiyoyin sojan Amurka sun ce, wani Ba’amurke dan kwangila da wani sojan Birtaniya sun rasa rayukansu a harin. Sai dai ba a bayyana sunan kowa ba tukuna.

    Ana cikin matukar zaman dar-dar tun da Amurka ta kashe babban kwamandan Iran, Qasem Soleimani a wani harin jirgin sama mara matuki da aka kai cikin watan Janairun da ya gabata.

    Harin ramuwar gayya da Iran ta kai al-Asad- wani sansanin da sojojin Amurka ke zaune- a ranar 8 ga watan Janairu, ya bar sojoji fiye da 100 suna fama da wasu lahanoni da suka shafi kwakwalwa.

    Sai dai kuma da alamu Iran da Amurka duka suna neman jan layi game da lamarin, kuma tun daga sannan babu wata barkewar rikici.

    Wani bayani da ya fito daga rundunar hadin gwiwar da Amurka ke jagoranta a Iraki da Siriya, ta gasgata cewa makaman roka 18 suka kai hari a sansanin, kuma an kashe jami’an rundunar su uku.

    Tun da farko wani sakon tuwita da wani mai magana da yawun hadin gwiwar sojojin ya yada, ya ce harin ya auku ne da karfe 7:35 na lokacin kasar (wato 4:35 agogon GMT) a ranar Laraba. Ya kara da cewa, an fara gudanar da bicike kan lamarin.

  11. An killace 'yan wasan Real Madrid kuma an dage La Liga

    Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta bai wa duka 'yan wasanta umarnin killace kansu bayan da wani dan wasan kwallon kwando na kungiyar ya kamu da cutar coronavirus.

    Da 'yan kwallon kafa da 'yan kwallon kwando na kungiyar na amfani da ban daki guda, wanda hakan ya sa aka dage duka wasannin gasar La Liga tsawon mako guda.

    Jami'an La Liga sun gana da Hukumar Kwallon Kafa ta Sufaniya (RFEF) da Kungiyar Kwallon Kafa ta Sufaniyar ranar Laraba da Alhamis kafin su yanke wannan hukuncin.

    Dama dai Tawagar kwallon kafa ta Real Madrid din za ta fafata ne da Eibar a La Liga ranar Juma'a ba tare da 'yan kallo ba.

    Sufaniya na da sama da mutane 2,000 da suka kamu da cutar coronavirus.

  12. Dalibai da malamin da aka yi wa gwaji a Najeriya ba sa dauke da coronavirus

    'Yan makaranta da malamin da aka yi wa gwaji a Najeriya ba sa dauke da coronavirus.

    Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Lagos a kudu maso yammacin kasar a ranar Alhamis, ta ce an gano cewa yaran nan 'yan gida daya su hudu da malaminsu da aka killace ba sa dauke da cutar.

    Ma'aikatar lafiyan ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter.

    Sun shiga Najeriyar ne daga Amurka kuma sun yi alaka da wani da ke dauke da cutar.

    Kwamishinan lafiya na Lagos Farfesa Akin Abayomi ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa ''Mun killace yara hudu da malaminsu bayan da suka shigo kasar daga Amurka da kuma wani mutum da ya taho daga Burtaniya, wadanda suka yi mu'amala da wani da yake dauke da cutar."

  13. Sabon salon gaisuwa don tsoron kamuwa da Coronavirus

  14. Najeriya ta nemi taimakon abokan diflomasiyyarta kan coronavirus

    Ministan lafiya a Najeriya, Osagie Ehanire ya bukaci abokan diflomasiyyar kasar su ba ta taimakon kayan kare kai da na gwajin coronavirus.

    A lokacin wani taro da jami'an kasashen waje kan matakan da na Najeriya ke dauka kan yaduwar coronavirus, ministan ya ce har yanzu kasar ba ta da na'urar bincike a kafofin shigowa kasar.

    Ya kara da cewa kasar ba ta da niyyar rufe iyakokinta ga 'yan kasashen waje da ke fama da cutar.

    Ya kuma ce ba za a hana 'yan kasar da suka shiga kasashen da ke fama da cutar dawowa ba, amma za a tabbatar an yi masu gwaje-gwajen da suka kamata sannan a killace tsawon makonni biyu.

    Ya ce ya kamata duka kasashe su yi aiki tare don wayar da kan mutane kan cutar.

  15. Mutum na farko mai dauke da Coronavirus ya warke a Saudiyya

    Saudiyya ta sanar da mutum na farko da ya warke daga cutar coronavirus daga cikin wadanda suka kamu.

    Wata sanarwa daKamfanin Dillancin Labaran kasar na SPAya wallafa a shafinsa na intanet daga Ma'aikatar Lafiya, ta ce mutumin wanda dan kasar ne ya kasance a cibiyar killace marasa lafiya da ke babban Asibitin Qatif a yankin Gabashin kasar, kuma yana cikin halin lafiya a yanzu.

    Sanarwar ta ce an kammala duk wasu gwaje-gwaje da ke da alaka da cutar tasa kuma an tabbatar da cewa ba ya dauke da ita ba.

    Zuwa jiya Laraba akwai mutum 21 da ke dauke da coronavirus a kasarMa'aikatar ta nemi duk wadanda suka shiga kasar da su bayyana kasashen da suka je kafin Saudiyyar ta hanyar kiran wata lambar waya ta musamman.

    Haka kuma Ma'aikatar Lafiyar ta karyata rahotannin da ke cewa an samu masu dauke da cutar har 600.

  16. An gabatar da kudirin dokar haramta amfani da janareto a Najeriya

    Wani kudirin doka na haramta shigo da janareto Najeriya ya tsallake karatu na farko a majalisar dattijan kasar.

    Sanata Muhammad Bima ne ya gabatar da kudirin dokar mai suna 'Generating Set (Prohibition/Ban) Bill, 2020' ranar Laraba a gaban majalisar.

    A Najeriya, mutane da masana'antu da yawa sun dogara ne da janareto saboda matsalar tsayayyar wutar lantarki da ta zama babbar matsala ga kasar.

  17. Indiya ta soke bayar da biza kan Coronavirus

    Indiya ta sanar soke bayar da biza har tsaon wata daya don hana yaduwar cutar Covid-19.

    Haka kuma an dakatar da bayar da biza kyauta da ake yi ga 'yan kasashen waje har sai 15 ga watan Afrilu.

    Ana ganin hakan zai shafi harkokin yawon bude ido da otel da masana'antar zirga-zirgar jiragen sama, al'amarin da zai yi nakasu ga tattalin arziki.

    Indiya ta tabbatar da cewa mutum 73 sun kamu da cutar, a cewar ma'aikatar lafiya.

    Ana sa ran wannan adadin zai karu nan da kwanaki masu zuwa, sakamakon gwaje-gwajen da aka yi wa wasu da dama.

    Sai dai wannan mataki na hana bayar da biza bai shafi jami'an diflomasiyya da jami'an gwamnati ba, kuma ranar Juma'a matakin zai fara aiki.

  18. Dan fim din Amurka Tom Hanks ya kamu da coronavirus

    Shahararren dan fim din nan na Amurka Tom Hanks ya bayyana cewa shi da matarsa Rita na dauke da cutar coronavirus a kasar Australiya.

    Mista Hanks da matar tasa masu shekaru 63 sun je asibiti bayan da suka fara jin alamun mura a garin Queensland, kamar yadda dan wasan ya rubuta a shafinsa na Instagram.

    A yanzu an kebe su a wani asibiti a Australiya kuma suna samun sauki, a cewar jami'ai.

    Ma'auratan sun je kasar ne don hada wani fim a kan mawaki Elvis Presley.

    Mista Hanks ya rubuta cewa: "Mun ji 'yar gajiya, kamar dai muna mura, da kuma ciwon jiki. Da dan zazzabi ma."

  19. An kashe mutum 10 a wani hari a Mali

    Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe mutum 10 tare da kona wani kauye a yankin tsakiyar Mali, kusa da iyakarta da Burkina Faso.

    Wanda suka shaida lamarin sun ce maharan sun zo ne a kan babura a yammacin jiya Laraba.

    Ana yawan samun hare-haren 'yan bindiga a yankin na tsakiyar Mali.

    A watan Fabrairu, sama da mutum 30 aka kashe a wani kauyen Fulani a wani hari da aka dora wa mayakan kabilar Dogon alhakin kaiwa.

    Masu ikirarin jihadi sun sha kai harin ramuwar gayya tare da yi wa dakarun kasar da na kasashen waje a yankin kwanton bauna.