Ministar lafiyar Burtaniya, Nadine Dorries ta kamu da coronavirus kuma ta killace kanta a gida.
Amma ba ita kadai ce babbar 'yar siyasa a duniya da ta kamu da cutar ba.
A Faransa, Ministan Al'adu Franck Riester ya kamu da cutar kuma rahotanni sun nuna cewa yana samun sauki.
Baya ga shi, 'Yan majalisar Faransa biyar suma sun kamu da cutar.
A Italiya, Shugaban jam'iyyar Democrat Nicola Zingaretti ya kamu da cutar kuma an killace shi a makon jiya.
Baya ga China, Italiya ce kasar da ta fi ko wacce yawan mutane masu dauke da cutar. Shi ya sa ma aka saka dokar hana shiga da fita a kasar.
Shugaban Majalisar Taryyar Turai David Sassoli ma ya killace kansa, bayan ya kai ziyara Italiya a karshen makon da ya wuce.
A Iran ma cutar ta shafi ministoci da 'yan siyasa, inda har 'yan siyasa biyu suka mutu dalilin cutar.
Fatemeh Rahbar da Mohammad Ali Ramazani da kuma Mohammad Mirmohammadi, wani mai bai wa Ayatollah Ali Khamanei shawara duk sun rasa rayukansu dalilin cutar.