Yadda kasashen Afirka ke kara matsa kaimi kan coronavirus
Hukumar Lafiya ta Duniya a jiya ta ayyana cutar sarkewar numfashi ta Coronavirus a matsayin annobar duniya.
Shugaban hukumar, Dokta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce yawan mutanen da ke kamuwa da cutar a tsakanin kasashen da ba China na ya ninka har sau 13 cikin mako 2.
Ga yadda wasu kasashen duniya ke daukar wasu matakai don hana yaduwar cutar:
- Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo ta killace mutum 109, wadanda ake tunanin sun yi mu'amala da mutum na farko da ya kamu da cutar covid-19.
- Afirka ta Kudu ta tabbatar da karuwar mutum 6 da suka kamu da cutar a jiya Laraba. Kawo yanzu, mutum 13 ne ke dauke da cutar a kasar.
- Makwabciyarta Botswana kuwa, ta ba da tabbacin cewa ba ta rufe iyakarta da Afirka ta Kudun ba kuma ba za ta rufe ba. Kusan 'yan Afirka ta Kudu 100 ne a birnin Wuhan na China ake sa rai za su dawo kasarsu gobe Juma'a.
- Burkina Faso, wacce take da mutane biyu masu dauke da cutar, ta haramta duk wani taron jama'a, yayin da makwabciyarta Nijar ta dakatar da duka tarukan kasa da kasa da aka sa lokaci za a yi a Yamai, babban birnin kasar.
- Uganda ta tsaurara dokokinta na tafiye-tafiye zuwa kasashe 9 ciki har da Burtaniya da Amurka kuma za ta fesa wa mutane magungunan kashe kwayoyin cuta a lokacin da suka iso kasar.
- Ma'aikatar lafiya a Eritrea ta bukaci matafiya masu shiga da fita kasar su soke shirye-shiryensu "don kansu" saboda barkewar cutar covid-19 a fadin duniya.
- A Mauritius, ma'aikatar lafiya ta tabbatar wa al'umar kasar cewa tana da isassun magunguna ko da cutar ta barke a kasar.
- Gwamnatin tsibirin Seychelles ta sanar da cewa ta rufe tsibirin ga jiragen ruwan yawon bude ido.
- Jaridar New Times mai goyon bayan gwamnatin Rwanda ta ruwaito cewa, kasar na neman wata hanyar shigo da kayayyaki yayin da wasu kasashen Afirka ke kokawa kan karewar da wasu kayan China suka yi saboda annobar.