Gwamnatin Birtaniya ta umarci duk wanda ya san yana tari ko zazzabi ya killace kansa a gida tsawon mako guda, a wani mataki da kasar ke dauka don hana yaduwar coronavirus.
Daga ranar Juma'a kuma za a hana tafiye-tafiye na makarantu zuwa kasashen waje, sannan an shawarci tsofaffi da wadanda suka san ba su da isasshiyar lafiya da ka da su je shawagi na jiragen ruwa.
Firai Minsita Boris Johnson ya ce ''wannan annoba ce mafi muni a zamanin nan.''
Zuwa yanzu mutum 10 ne suka mutu a Birtaniya sakamon cutar.
Akwai masu dauke da cutar 596 a fadin kasar.
Da yake jawabi kan matakan a wani taron gaggawa, Mista Johnson ya ce ''Wasu mutanen na kwatanta cutar da irin murar da aka saba ta yanayi, amma ba haka ba ne.
''Rashin ingantacciyar garkuwar jiki na sa cutar ta zama mai hadari.''
''Za ta ci gaba da yaduwa, amma ina tare da ku, ina tare da al'ummar Birtaniya, iyalai da yawa za su rasa masoyansu kafin lokacinsu ya yi.''
Yawan masu dauke da cutar a Birtaniya sun karu da mutum 100 a ranar Alhamis daga 456 a ranar Laraba - Ingila na da 491, da 60 a Scotland da 20 a Arewacin Ireland da kuma 25 a Wales.