Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da sassan duniya

Wannan shafin yana kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Buhari ya nada kwamitin sasanta ’yan jam’iyyar APC

    Buhari

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari tare da shugabancin jam'iyyar APC mai mulki sun kafa wani kwamiti da zai sasanta tsakanin 'ya'yan jam'iyyar.

    Wata sanarwa da APC ta fitar ranar Litinin ta ce za a rantsar da kwamitin ranar Talata 11 ga watan Fabarairu a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja, da nufin lalubo hanyoyin magance korafe-korafen 'ya'yanta a fadin kasa baki daya.

    Kwamitin yana da mambobi 12 kamar haka:

    1. Chief Bisi Akande (Shugaba)

    2. Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello

    3. Gwamnan Osun, Gboyega Oyetola

    4. Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattijai, Sanata Yahaya Abdullahi

    5.Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Ahmed Idris Wase

    6. Sanata Umaru Tanko Al-Makura

    7. Sanata Kashim Shettima

    8. Karamar Ministar Muhalli, Sharon Ikeazor

    9. Alh. Nasiru Aliko Koki

    10. Sanata Khairat Gwadabe-Abdulrazak

    11. Sanata Binta Garba

    12. Sanata John Enoh (Sakatare)

  2. Ana lalata tan 100 na matattun takardun Naira a kowane mako – CBN

    Matattun takardun naira

    Asalin hoton, The Sun

    Babban bankin Najeriya na CBN ya ce a kowane mako yana lalata sama da tan 100 na takardun kudin da suka fita daga hayyacinsu.

    Babban bankin ya bayyana haka ne a cikin wasu bayanai da ya fitar, inda ya kara da cewa yana yin hakan ne ta hanyar kona kudaden a wasu kebabbun cibiyoyi 12 da yake da su a fadin kasar.

    Kazalika bankin zai yi aiki tare da kamfanoni masu zaman kansu domin sabunta lalatattun takardun kudin na Naira.

    Ya ce yin hakan ya zama wajibi saboda kona kudaden na da illa ga muhalli sannan kuma ya ci karo da tsare-tsaren bankin.

    A cewar sanarwar, sashe na 18(d) na dokar CBN ta 2007 ya bai wa babban bankin damar shirya lalata matattun kudaden da kuma kwandaloli bisa tanadin sashe na 20(3) na dokar ko kuma idan bankin ya gano kudaden da bai dace a rika amfani da su ba.

  3. Ebola ba ya shirin ritaya daga dambe

    Abdurrazak Ebola
    Bayanan hoto, Abdurrazak Ebola shi ne wakilin Kudawa

    Fitatcen dan wasan damben gargajiya Muhammad Abdurrazak Ebola ya ce ba ya shirin yin ritaya daga wasan.

    Ebola wanda ke wakiltar bangaren Kuda kuma yake daure hannunsa na hagu, ya ce kawo yanzu babu wani dan wasa da zai iya kare mutuncin Kudawa kamar yadda yake yi.

    Dan wasan daga jihar Kaduna ya ce kawo yanzu babu wani babban dan dambe da zai iya tare yaki da zarar ya tunkaro Kudawa.

    Ya kara da cewar shagonsa, Taufik dogon Ebola da Dan Alin Ba ta Isarka suna nimijin kokari da sauran matasa, to amma wasu damben ya fi karfinsu, shi ya sa har yanzu yake yin wasan.

  4. An ci tarar mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea kan almubazzaranci

    Teodorin Obiang

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, An san Obiang da nuna kwalliya a shafukan sada zumunta

    Kotu a kasar Faransa ta ci tarar dan gidan shugaban kasar Equatorial Guinea tarar yuro miliyan 30, kwatankwacin kusan naira biliyan 11, saboda laifin almubazzaranci da kudin gwamnatin kasar a nahiyar Turai, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Teodorin Obiang, dan gidan Shugaba Teodoro Obiang Nguema kuma mataimakin shugaban kasar, ya fuskanci hukuncin daurin shekara uku tare da tarar dala miliyan 32.9 tun a shekarar 2017 amma sai ya daukaka kara.

    Kotun ta Faransa ta tabbatar da hukuncin kotun baya, inda ta kama shi da laifin kashe kudi kan jirgin sama mallakarsa zuwa kasashen Turai sannan ya sayi wani gida mai hawa shida a unguwa mai tsada a birnin Paris na Faransa.

    Alkalan kotun sun yanke cewa ya kamata a kwace gidan nasa wanda aka kiyasta kan yuro miliyan 107 (naira biliyan 42). Obiang mai shekara 50 bai halarci zaman kotun ba.

  5. Ballewar kura daga keji ya sanya fargaba a zukatan al'umbar Imo

    Hyena

    Asalin hoton, Getty Images

    An fuskanci tashin hankali a Nekede kusa da Owerri da ke jihar Imo, kudu maso gabashin Najeriya bayan da aka samu rahoton wata kura ta balle daga gidan ajiyar namun daji na jihar.

    Shugaban gidan namun dajin, Mr Frank Abioye ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).

    Abioye ya ce masu kula da namun daji sun kama kurar - sa'o'i shida bayan da ta balle daga keji.

    Ya ce lamarin ya haifar da fargaba a Nekede da ke kamaramr hukumar Owerri ta yamma a jihar.

    Shugaban ya ce an yi amfani da wata dabara ta “Physical Restricted Method” wajen kamo kurar.

    Ya kuma ce ba a samu asarar rai ba sakamakon ballewar kurar.

    A cewarsa, kurar ta haka wani rami a karkashin kasa abin da ya bata damar ballewa daga kejin da take ciki.

  6. Kasashen Afirka na nazari kan rufe iyakokin Najeriya

    Jami'an Kwastam a Najeriya

    Asalin hoton, Nairametrics

    Shugabannin kasashen kungiyar hadin kan Afirka ta AU sun kafa wani kwamiti da zai duba sannan ya hada rahoto game da yadda Najeriya ta garkame iyakokinta na kasa tsakaninta da makwabtanta.

    Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito Garba Shehu, mai magana da yawun gwamnatin Najeriya yana cewa an yanke shawarar ne a daren ranar Lahadi yayin taron kungiyar ta AU a Addis Ababa, babban birnin Habasha wato Ethiopia.

    Garba Shehu ya bayyana hakan ne ranar Litinin, inda ya ce kwamitin zai yi aiki ne karkashin jagorancin shugaban kasar Burkina Faso, Roch Marc Christian Kabore.

    Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya shaida wa 'yan jarida bayan taron cewa Shugaba Muhammdu Biuhari ya halarci taron, wanda shugaban AU, Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar ya jagoranta.

    Kazalika Garba Shehu ya ce shugabannin sun tattauna kan sabon kudin Eco na kasashen Afirka ta Yamma da kuma yanayin da ake ciki a kasar Guinea Bissau bayan kammala zaben shugaban kasa.

  7. Zan mayar da NTA kamar CNN idan aka ba ni rancen ‎₦181b — Lai Mohammed

    Lai Mohammed ya dade yana jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Lai Mohammed ya dade yana jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya

    Ministan watsa labaran Najeriya, Lai Mohammed, ya sha alwashin mayar da gidan talbijin din kasar, NTA, tamkar gidan talbijin na CNN da ke Amurka idan majalisar dokokin kasar ta bari ya karbo rancen $500m, kwatankwacin kusan naira biliyan 181.

    Kafofin watsa labaran Najeriya, ciki har da jaridar Guardian, sun rawaito cewa ministan ya bayyana haka ne lokacin da ya je gaban kwamitin da ke kula da karbo bashi a ciki da wajen kasar na majalisar dattawa.

    Ya kara da cewa yana so su amince a karbo bashin ne daga cikin $29.96b da Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar ta amince ya karbo domin gudanar da manyan ayyuka a kasar.

    'Yan Najeriya da dama sun yi ta yi wa ministan shagube a shafukan sada zumunta, inda yanzu haka yake cikin manyan abubuwan da aka fi tattaunawa a kansu a shafin Twitter.

    Wani mai amfani da Twitter, Olusegun Iselaiye, ya ce ko da NTA za ta samu ninkin kudin da Lai Mohammed yake so a ranto, ba za ta zama tamkar gidan talbijin mai zaman kansa na kasar Channels TV ba, ballantana CNN.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Rikici na neman barkewa a ABU bayan an bukaci shugaban jami'ar ya tafi hutun ritaya

    ABU Zaria

    Asalin hoton, @Tweet_abuzaria

    Takaddama na neman barkewa a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria sakamakon umarnin da majalisar gudanarwar jami'ar ta bai wa shugaban makarantar mai barin gado, Farfesa Ibrahim Garba na tafiya hutun ritaya.

    A ranar 30 ga watan Afrilun bana ne wa'adin shugabancin Farfesa Garba zai cika kuma umarnin da majalisar gudanarwar jami'ar ta ba shi gabanin cikar wa'adin na janyo ce-ce ku-ce.

    Sai dai Farfesa Graba ya bayyana wa Daily Trust cewa ba shi da niyyar zuwa hutun har sai karshen wa'adin shugabancinsa na shekara biyar ya cika.

    A nata bangaren kungiyar tsofaffin daliban ABU ta sa baki a lamarin inda ta ce babu wata doka da ta bai wa shugabannin jami'a damar zuwa hutun ritaya a don haka ne ma ta bukaci majalisar da ta gaggauta janye umarnin.

    Daily Trust ta kuma rawaito cewa a watan Janairu ne ABU ta nada tsohon mataimakin shugaban jami'ar, Farfesa Kabir Bala a matsayin sabon shugaban jami'ar kuma a ranar 1 ga watan Mayu zai fara aiki.

  9. Boko Haram ta kashe mutum 30 a Borno

    Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutum fiye da 30 a garin Auno na jihar Borno.

    Kazalika, 'yan bindigar sun yi awon gaba da wasu da har yanzu ba a gano adadinsu ba wanda kuma yawancinsu matafiya ne, kamar yadda dan majalisar wakilai Satomi Ahmad ya shaida wa BBC.

    Dan majalisar ya ce 'yan Boko Haram sun kona motoci kusan 20 kuma wasu akwai mutane a cikinsu sannan kuma akwai mata da kananan yara a cikin wadanda suka yi awon gaba da su.

    Garin Auno yana da nisan kilomita 24 daga babban birnin jihar Maiduguri da misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi.

    Gwamnan jihar Babagana Umara Zullum ya wallafa ziyarar da ya kai wurin da abin ya faru a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce gwamnatin jihar tare da gwamnatin tarayya na kara himma wajen kawo karshen ayyukan Boko Haram a Maiduguri da kewayenta.

    Auno shi ne garin da shingen jami'an tsaro suke na karshe wanda daga shi sai shiga garin Maiduguri.

    Borno Attack

    Asalin hoton, Borno Govt

    Borno Attack

    Asalin hoton, Borno govt

  10. An tashi baram-baram a wajen sulhun Sudan ta Kudu

    Salva Kiir da Macahr

    Asalin hoton, Getty Images

    An tashi ba tare da cimma matsaya ba a tattaunawar da ake yi domin kawo zaman lafiya mai dorewa a Sudan ta Kudu, tsakanin bangaren gwamnatin kasar da na ‘yan adawa.

    Taron tattaunawar dai na gudana ne a Addis-Ababa, babban birnin Habasha.

    Shugaba Salva Kiir da abokin hamayyarsa Riek Machar sun shafe kwana biyu suna ganawar sirri a kokarin cimma yarjejeniya kafin kwana 100 din da aka diba don kafa gwamnatin rikon kwarya su cika.

    Sai dai abin mamaki ba a iya cimma matsaya ba.

    Babban bambancin ra'ayin da ke tsakanin su shi ne yawan jihohin da za a samu a kasar.

    Gwamnatin na son a samu jihohi 32, yayin da su kuma 'yan hamayya ke son a mayar da yawan jihohin 10.

    An shafe shekara shida ana rikici a Sudan Ta Kudu inda dubun-dubatar mutane suka mutu, miliyoyi kuma suka rasa muhallansu a yakin basasar mai muni.

    Shugaba Kiir da Machar za su iya sake cimma yarjejeniya kafin a kammala taron a ranar Litinin.

  11. Dan majalisar dattawan Najeriya Longjan ya rasu

    Jam'iyyyar APC mai mulki Najeriya ta sanar da mutuwar daya daga cikin 'yan majalisar dattawan kasar, Ignatius Longjan.

    A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, APC ta ce ta yi matukar kaduwa da samun labarin rasuwar Sanata Longjan.

    Dan majalisar, wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin al'adu da yawon bude ido a majalisar dattawan, ya taba zama mataimakin gwamnan jihar Filato.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. 'Yar Najeriya Asisat Oshoala ta zaku ta ci gaba da yin nasara a Barcelona

    'Yar Najeriya Asisat Oshoala ta ce ta zaku ta ci gaba da samun nasara a Barcelona Femenino bayan nasarar farko da ta samu a gasar kwallon kafar Spain.

    'Yar wasan mai shekara 25 ta zura kwallo a wasan da Barcelona ta bai wa Real Sociedad da ci 10-1 a gasar mata ta cin kofin Spain a Salamanca.

    "Samun nasara a Super cup bayan wacce muka samu a Copa Catalunya a bara abin alfahari ne," a cewarta a hirar da ta yi da BBC Sport.

    "Amma babban burina shi ne na ci gaba da himma sannan ina samun nasara."

    Asisat Oshoala

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Asisat Oshoala ta ce burinta shi ta ci gaba da zura kwallo
  13. An kai harin kunar bakin wake Aljeriya

    taswirar Aljeriya

    Wani soja ya mutu a wani harin kunar bakin wake da aka kai a wani sansanin sojoji a kudancin Aljeriya.

    Wannan ne hari na farko a kasar cikin shekaru da dama.

    Babu wani bayani kan wanda ya assasa harin, wanda aka kai a yankin Bordj Baji, kusa da iyakar kasar da Mali.

    Rikici a makwabciyarta Libya da kuma tabarbarewar tsaro a Mali sun taimaka wajen karuwar ayyukan soji a yankunan hamadar Sahara da Sahel a arewacin Afirka.

  14. Farin dango sun mamaye kasar Uganda

    Hukumomi a Uganda sun ce farin dangon da suka isa kasar ranar Lahadi sun mamaye akalla lardi biyu da ke arewa maso gabashin kasar.

    Firai Minista Ruhakana Rugunda ya gudanar da taron gaggawa tare da 'yan siyasa da msu ruwa da tsaki awowi kadan bayan farin dangon sun mamaye yankunan.

    Hukumomi a kasar sun ce sun fitar da tsarin da zai kai ga kawar da farin dangon.

    Wakiliyar BBC Catherine Byaruhanga, wadda ke Kampala, babban birnin kasar ta ruwaito cewa galibin 'yan kasar ba za su iya tuna lokacin da farin dango suka taba mamaye kasar ba.

    Galibin 'yan kasar ba za su iya tuna lokacin da farin dango suka taba mamaye Uganda ba

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Galibin 'yan kasar ba za su iya tuna lokacin da farin dango suka taba mamaye Uganda ba
  15. Yadda jami'an tsaron Najeriya ke azabtar da jama'a

    Shirin BBC na Africa Eye ya bankado yadda jami'an tsaron Najeriya ke azabtar da jama'a duk kuwa da cewa dokokin kasar sun haramta yi wa mutane irin wannan azaba wadda ta zarce hankali.

    Ku latsa bidoyon da ke kasa domin kallon cikakken rahoton Mayeni Jones:

    Bayanan bidiyo, Africa Eye: Yadda jami'an tsaron Najeriya ke azabtar da jama'a
  16. AU: Guterres ya yi Alla-wadai da yakin Libya

    Guterres

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah wadai da rikicin da ke ci gaba a kasar Libya, yayin da aka shiga wuni na biyu na taron kolin Tarayyar Afirka. Ya ce katsalandan din kasashen waje a kasar da cewa wani babban abin kunya ne. Ya ce ci gaba da rikicin ya ba shi kunya, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma takunkumin hana bazuwar makamai da aka cimma a watan jiya. "Akwai takunkumin makamai amma ana keta ta gatse-gatse," in ji Mista Guterres.

  17. An fara aikin rijistar masu zabe a Nijar

    An fara aikin rijistar masu zabe a jihohi hudu a Jamhuriyar Nijar.

    Wannan shi ne zango na biyu na aikin rijistar masu zaben da hukumar zaben kasar ta CENI ke yi.

    Kawo yanzu dai mutane da dama ne suka yi rijista yayin wasu ke cewa sai mutane sun ragu.

    Ga rahoton Tchima Illa Issoufou daga Yamai:

    Bayanan sautiRahoton Tchima kan rijitar masu zabe a Nijar
  18. Buhari ya caccaki shugaban Dattawan Arewa

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya caccaki shugaban kungiyar Dattawan Arewacin kasar, Farfesa Ango Abdullahi.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Femi Adesina, ya fitar ranar Lahadi ya ce Ango Abdullahi ba shi da wata kima kuma kusan shi kadai ne yake kidansa ya yi rawarsa a Kungiyar Dattawan.

    A cewarsa, “Ranar Lahadi Farfesa Ango Abdullahi ya sanya hannu a kan wata sanarwa da ta tabo batutuwa da dama game da arewaci da ma Najeriya baki daya.

    Tsohon shugaban Jami’ar ya sanya hannu kan takardar ne a madadin Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya.

    Amma a hakikanin gaskiya, Ango Abdullahi shi ne kadai a kungiyar. Kungiya ce da ba ta da wata martaba. A iya cewa shugabanta kamar soja ne da ba shi da dakarun da ke bin sa.”

    Mr Adesina ya ce tun gabanin zaben 2019 Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta nuna rashin kaunarta ga Shugaba Buhari, sannan ta bayyana dan takarar da take goyon baya.

    Ya kara da cewa gwamnatin Buhari ba ta bukatar mutane irinsu Farfesa Abdullahi don gaya mata yadda za ta tafiyar da harkokin kasar.

    Buhari

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mr Adesina ya ce Buhari ba ya bukatar mutane irinsu Farfesa Abdullahi don gaya masa yadda zai tafiyar da harkokin kasar.
  19. Za a kama mutanen da ke kasuwanci da dalar Amurka a Zimbabwe

    Ministan kudin Zimbabwe Mthuli Ncube ya gargadi ‘yan kasuwan kasar da su kauracewa neman da suke yi wa abokan kasuwacinsu cewa su rika ba su dalar Amurka wajen saye da sayarwa ko kuma su fuskanci hukunci.

    A watan Yuni, kasar ta daina amfani da dalar Amurka inda ta koma yin amfani da dalar Zimbabwe –wadda aka soke amfani da ita kusan shekara 10 da suka gabata--a harkokin saye da sayarwa.

    Sai dai karancin dalar Zimbabwe da kuma rashin darajarta a kasuwa sun sa ‘yan kasar na ci gaba da amfani da dalar Amurka.

    Zimbabwe na shigo da kusan dukkan kayan masarufinta, ciki har da man fetur da abinci daga kasashen waje.

    ‘Yan kasuwa na shan wahala matuka kafin samun dalar Zimbabwe daga babban bankin kasar.

    Karancin dalar Zimbabwe ya sa ‘yan kasar na ci gaba da amfani da dalar Amurka.

    Asalin hoton, Getty Images

  20. An kammala zaben Kamaru wanda dubban mutane suka kauracewa

    Rahotanni daga Kamaru sun nuna cewa ranar Lahadi masu kada kuri’a basu fito sosai ba domin yin zaben ‘yan majalisar dokokin da aka dade ana jinkirtawa a kasar.

    An rufe kada kuri’a da misalin karfe shida a agogon kasar kuma ana sa ran fitar da sakamakon zaben nan da mako biyu.

    A yankunan da ke amfani da turacin Ingilishi na kasar, inda aka kwashe tsawon lokaci ana tafka rikici, an bayar da rahoton yin taho-mu-gama a garin Muyuka kuma ganau sun ce sun ji karar harbe-harben bindigogi a birnin Buea da kuma garin Kuma.

    A farkon makon jiya, ‘yan a-waren Ambazoniya sun bukaci magoya bayansu da kada su shiga zaben, yayin da wasu mazauna yankunan suka rika tserewa daga gidajensu domin fargabar arangama tsakanin ‘yan tawaye da jami’an tsaro.

    Wata mata na kada kuri'arta a zaben 'yan majalisar dokokin Kamaru

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Wata mata na kada kuri'arta a zaben 'yan majalisar dokokin Kamaru