Sojojin Syria na gab da kwace ikon hanyoyin shiga manyan biranen kasar
Rahotanni daga Syria na cewa sojojin gwamnatin kasar suna gab da kwace ikon manyan hanyoyin da ake amfani da su wajen shiga manyan biranen kasar hudu.
Majiyoyin gwamnati sun ce babbar hanyar da ta doshi yankin da 'yan tawaye ke rike da shi a arewa-maso-yammacin Siriya nan da 'yan sa'o'i kadan sojoji za su kwace ikon wurin.
Sojojin gwamnati da ke samun goyon bayan Rasha suna ta kai hare-hare a cikin watannin biyu da suka gabata, don sake bude hanyar da ta hada Damaskus da Aleppo.
Akwai rahotannin da ke cewa 'yan tawayen da ke samun goyon bayan Turkiyya sun harbo wani jirgi mai saukar angulu mallakar gwamnatin Syria a wani waje da ke Idlib.

Asalin hoton, AFP













