An hana matar mataimakin shugaban kasa ganin 'ya'yanta
Wata kotu a Zimbabwe ta hana matar mataimakin shugaban kasar Constatino Chiwenga, Marry Mubaiwa, ganin 'ya'yansu da ma shiga gidan da suke ciki.
Babbar kotu ta yi watsi da bukatar Ms Mubaiwa da ke son a ba ta dama ta rika shiga gidan tana ganawa da 'ya'yansu.
Kotun ta bukaci ta rika zama a gidan iyayenta har sai ta kammala yanke hukunci a kan shari'ar da suke yi.
A bara ne aka kama Ms Mubaiwa ana tuhumarta da yunkurin kashe Mr Chiwenga da yin mu'amala da kudaden haramun.
An bayar da belinta ranar shida ga watan Janairu sannan aka bukaci ta mika fasfo dinta na difilomasiyya da kuma takardun gidajen mahaifinta.
Tun daga wancan lokacin take neman kotu ta ba ta damar shiga gidan Mr Chiwenga domin ganawa da 'ya'yansu.

Asalin hoton, Getty Images













