Ebola ba zai yi ritayar damben gargajiya ba

Fitatcen dan wasan damben gargajiya Muhammad Abdurrazak Ebola ya ce bai yi shirin yin ritaya daga wasan ba.
Ebola wanda ke wakiltar bangaren Kuda wanda ke daure hannunsa na hagu ya ce kawo yanzu babu wani dan wasa da zai iya kare mutuncin Kudawa kamar yadda yake yi.
Dan wasan daga jihar Kaduna ya ce kawo yanzu babu wani babban dan dambe da zai iya tare yaki da zarar ya tunkaro Kudawa.
Ya kara da cewar Shagonsa Taufik dogon Ebola da Dan Alin Bata isarka suna nimijin kokari da sauran matasa, to amma wasu damben yafi karfinsu shi ya sa har yanzu yake yin wasan.
Akwai manyan 'yan dambe a bangaren Guramada da suke da jiki da karfi kamar su Dogo Mai Takwasara da Garkuwan Cindo Dogon Kyallu da Habu na Dutsen Mari da dai sauransu.
Haka ma a yankin Arewa kamar Ali Kanin Bello su Bahagon Shagon 'Yan Sanda sai namijin gaske.

Ebola ne ya fara lashe mota a damben Kano da aka fara, haka kuma ya kai wasan daf da na karshe a wasannin Kaduna a shekarar nan.
Ebola ya kara da Bahagon Shagon 'Yan Sanda a Dei-Dei inda wasan ya kai da takaddama, aka bai wa Bahago mota.
Sai dai sun kara haduwa a wasan karshe a damben Kaduna a Marabar Nyanya jihar Nasarawa, inda Ebola ya buge Bahagon Shagon 'Yan Sanda.
Kawo yanzu kisa uku da uku ne tsakanin Ebola da Ali Kanin Bello, yayin da Ebola ya yi nasarar buge Mai Takwasara 3-1.

Sai Sarkin dambe Garkuwan Cindo da ya ci mota biyu a kan Ebola, amma bai yi kisa a wasan farko ba.
Sai a haduwa ta biyu ne Garkuwan Cindo ya buge Ebola.
Haka kuma Bahagon Mai Takwasara ya buge Ebola a bara a Abuja, koda yake Taufik ya daukarwa Ebola fansa inda ya buge Bahagon Mai Takwasara.
A wannan shekarar ta 2020 Abdurrazak Ebola ya ce zai dauki fansa a kan Sarkin dambe Garkuwan Cindo da Bahagon Mai Takwasara.

Ya kara da cewar zai kafa tarihin da bai yi shi a baya a harkar dambe zai kuma tsaya ya cui gaba da kare martabar Kudawa.
A harkar dambe Ebola ya samu alheri da dama yana kasuwanci da sauran hanyoyin da yake samun daukar nauyin 'yan uwa da abokan arzuka sai dai bai yi aure ba kawo yanzu.










