Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da sassan duniya

Wannan shafin yana kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Barka da Ranar Masoya ta Duniya

    Muna fatan kuna cikin koshin lafiya a wannan rana ta Juma'a, haji babbar rana. Ranar ce kuma ta fado daidai da 14 ga watan Fabrairu, wato Ranar Masoya ta Duniya.

    Da fatan za ku bibiye mu domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman al'amuran da ke faruwa a Najeriya da Nijar da ma sassan duniya.

    Ranar Masoya ta Duniya

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Rufewa

    A nan muka kawo karshen labarai da bayanai kai-tsaye da muke kawo maku a wannan a shafi.

    Sai kuma gobe Juma'a, idan Allah Ya kai mu.

    Za ku iya duba kasa don karanta abubuwan da suka faru a Najeriya da sauran sassan duniya ranar Alhamis. Mun gode.

  3. An ajiye bam mai 'ya'ya a yankunan da ake gina gidaje a Libya

    An ajiye bam mai 'ya'ya a Libya

    Asalin hoton, Human Rights Watch

    Bayanan hoto, An ajiye bam mai 'ya'ya a Libya

    Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch, ta ce an ajiye bam mai 'ya'ya a yankunan da ake gina gidaje a ranar 2 ga watan Disambar 2019.

    Kungiyar ta ce, mayakan da ke biyayya ga jagoran 'yan tawayen Libya Janar Khalifa Haftar ne suka ajiye bam din.

    A yayin wata ziyara da kungiyar ta kai yankunan gidajen a ranar 17 ga watan Disambar 2019, kungiyar ta gano bam din wadanda aka binne.

    Kungiyar ta ce an kai wasu hare-hare ta sama wadanda ba mamaki dakarun da ke goya wa janar Haftar baya ne suka kai ko kuma kasashen da ake goya masa baya ciki har da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Rasha.

    Babu wani rahoton samun rauni ko rasa rai, saboda tuni mazauna yankin da ke kudancin birnin Tripoli suka yi kaura suka barshi.

    Tuni dai aka haramta amfani da bam mai 'ya'ya a cikin wata yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a 2008.

    Koda yake Libya na cikin kasashe 75 ciki har da Rasha da Amurka wadanda suka ki sanya hannu a yarjejeniyar.

  4. Atiku ya ji dadin bai wa PDP kujerar gwamnan Bayelsa

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce ya ji dadin bayyana dan takarar gwamnan PDP na jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, wanda ya sha kaye a zaben watan jiya a matsayin zababben gwamnan jihar.

    Ranar Alhamis kolin Najeriya ta soke zaben da aka yi wa, David Lyon na jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar.

    Alkalan kotun biyar, wadanda Mai shari'a Mary Odili ta jagoranta wajen yanke hukuncin, sun ce sun soke zaben Mr Lyon ne saboda mataimakinsa Biobarakuma Degi-Eremienyo ya mika wa hukumar zaben kasar takardun bogi domin a bar shi ya tsaya takara a zaben ranar 16 ga watan Nuwambar da ya gabata.

    A wani sako da ya wallafa a Twitter, Atiku Abubakar ya taya Sanata Douye Diri da mataimakinsa Mr. Lawrence Ewhrujakpor da ma jam'iyyar PDP murna.

    Kazalika ya yi kira ga alkalan kotun su ci gaba da yanke hukunci ba tare da sani ko sabo ba.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Takardun bogi sun sa an soke zaben gwamnan Bayelsa

    Kotun kolin Najeriya ta soke zaben gwamnan jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin kasar. Kotun ta soke zaben David Lyon, na jam'iyyar APC mai mulkin kasar ne kwana guda kafin ya sha rantsuwar kama aiki.

    Alkalan kotun biyar, wadanda Mai shari'a Mary Odili ta jagoranta wajen yanke hukuncin, sun ce sun soke zaben Mr Lyon ne saboda mataimakinsa Biobarakuma Degi-Eremienyo ya mika wa hukumar zaben kasar takardun bogi domin a bar shi ya tsaya takara a zaben ranar 16 ga watan Nuwambar da ya gabata.

    A watan Nuwambar 2019, hukumar zaben kasar INEC ta ayyana Lyon na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan ranar 16 ga watan Nuwamba, bayan ya samu kuri'u 352,552.

    Hakazalika hukumar zaben ta bayyana cewa Mista Douye Diri na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 143,172.

    David Lyon da Shugaba Buhari

    Asalin hoton, NIGERIAN PRESIDENCY

  6. Rayuwata daga dan gudun hijira zuwa babban lauya

    Hashi Mohammed

    Asalin hoton, Hashi Mohamme twitter

    Bayanan hoto, Hashi Mohammed

    Hashi Mohammed lauya ne kuma dan jarida mai yada labarai a birnin Landan.

    Ya je Birtaniya ne a lokacin yana da shekara tara tare da iyayensa 'yan kasar Somalia da Kenya bayan barkewar yakin basasa a Somalia.

    Hashi, ya wallafa wani littafi wanda ya yi bayani a kan daraussan da ya koya a rayuwarsa da kuma kalubalen zamantakewar da ya fuskanta saboda suna da kuma kalar fatarsa da ma aikin iyayensa.

    Hashi ya shaida wa BBC cewa, ya sha gwagwarmaya kafin ya zama lauya da kuma mai yada shirye-shirye.

    Ya ce: "Saboda ni dan Afirka ne bakar fata aka tsangwame ni, amma kuma hakan bai sanyaya mani gwiwa ba na dage na yi karatu har na zama abin da na zama a yanzu".

  7. Mai dakin shugaban Namibia za ta bayar da dukiyarta sadaka

    Uwargidan shugaban kasar Namibia ta yi alkawarin bayar da dukiyarta sadaka bayan ta mutu.

    Monica Geingos, na da dukiyar da aka kiyasta cewa za ta kai dala miliyan uku, wadda aka ce ta tsara mika ta ga daya daga cikin gidauniyoyinta don tallafawa al'umma.

    Gidauniyar ta kan bayar da tallafi ga masu kananan masana'antu, da bayar da tallafi ga dalibai marassa gata da kuma bayar da tallafi ga matan da aka ci zarafinsu.

    Mai dakin shugaban kasar, lauya ce, wadda kuma ta kare wadanda aka ci zarafi.

    Kazalika ta musanta zargin cewa ta na neman mukamin gwamnati.

    Ms Geingos ta ce " Na yi amanna cewa gado na daya daga cikin babban abin da ke janyo rashin dai-daito a tsakanin al'umma, shi ya sa na yanke shawarar sadaukar da dukiyata ga ma bukata".

    Monica Geingos

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Monica Geingos ta auri shugaba Hage Geingob a 2015
  8. 'Kashi 34 cikin 100 na 'yan Najeriya ke amfani da kwaroron roba'

    Wani sabon bincike ya nuna cewa kashi 34 cikin 100 ne kadai na 'yan Najeriya suke amfani da kwaroron roba yayin jima'i, kuma cikin wannan yawan kashi 28 cikin 100 ne kawai ke amfani da shi ko yaushe.

    Kungiyoyin da suka hada kai wajen yin binciken sun hada da cibiyar NOI Polls mai yin bincike kan wasu al'amura a Afirka Ta Yamma da Hukumar Takaita Yaduwar Cutar AIDS NACA da kuma Gidauniyar AIDS HealthCare Foundation (AHF).

    Shugaban NOI polls Dr Chike Nwangwu, Dr Chike Nwangwu, ya shaida wa BBC cewa duk da cewa kashi 83 cikin 100 na 'yan Najeriya sun yi amannar cewa mutanen kirki ne kawai ke amfani da kwaroron roba, kuma kashi 34 ne kawai suka yarda suke amfani da shi.

    "Kuma ko cikin kashi 34 din ma kashi 28 ne kawai ke amfani da shi ko yaushe."

    An fitar da rahoton ne don bikin Ranar Kwaroron Roba ta Duniya (ICD), da ake yi duk 13 ga watan Fabrairu, kwana guda kafin ranar Valentine, don wayar da kai kan masu son yin jima'i da kariya, ake kuma karfafa wa mutane su yi amfani da kwaroron roba.

    Kondom

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Coronavirus: China ta fara samun tallafi daga Liberia

    Wata likita 'yar kasar China da ke da asibiti a Monrovia, babban birnin kasar Liberia, ta fara aika gudunmuwar takunkumin rufe fuska da sauran kayayyakin kariya ga asibitocin da ke China wadanda ke kula da wadanda suka kamu da cutar coronavirus.

    Dr Zhai Yu, mai kimanin shekara 46, ta hada katan-katan na takunkumin rufe fuska da rigar kariya inda ta aika da su asibitocin da ke Wuhan domin bai wa mutane su kare kansu.

    Ta ce: ''Ko da na kai ziyara asibitina da ke Liberia a ranar Laraba, sai na yanke shawara ni da ma'aikatana a kan hada wadannan kayayyaki mu aike da su China.''

    Likitar ta ce ta shigo da wadannan kayan ne tun shekaru shida da suka wuce domin ayi amfani da su a asibitinta a lokacin da aka samu barkewar cutar ebola, amma yanzu ga shi za su yi rana.

    Dr Zhai Yu ta ce suna so su ma su yi tasu bajintar wajen taimakawa 'yan kasarta.

    Dr Zhai Yu
    Bayanan hoto, Dr Zhai Yu
  10. An saki dan jaridar da ya kwana 175 a gidan yarin Najeriya

    Wata kotu a jihar Cross River da ke Najeriya ta bayar da belin dan jaridar nan Agba Jalingo, wanda aka tsare bisa zargin cin amanar kasar.

    An kama Jalingo ranar 22 ga watan Agusta na 2019 bayan ya wallafa rahoton da ke zargin gwamnan jihar Ben Ayade da karkatar da N500m daga asusun jihar.

    An kulle shi a ofishin 'yan sanda da kuma kurkuku tsawon kwana 175.

    Lamarin ya jawo suka daga kungiyoyon kare hakkin dan adam da wasu 'yan kasar.

    Sai dai mai shari'a Sule Shuaibu, na babbar kotun tarayya da ke Calabar, ya bayar da belin Mr Jalingo a kan N10m bayan lauyansa Attah Ochinke ya nemi yin hakan.

    Kungiyoyin kare hakkin dan adam, irin su Amnesty International sun yi maraba da bayar da belin dan jaridar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. Malaman kananan makarantun Nijar sun fara yajin aiki

    Ranar Alhamis ne kungiyar malaman kananan makarantu 'yan kwantiragi ta SYNACEB a Jamhuriyar Nijar ta fara yajin aiki na kwana biyu don nuna kin amincewa kan wasu batutuwa da suka hada da rashin samun alawus a kai a kai da kuma yadda matsalar tsaro ke kawo cikas ga sha'anin illimi a jihar Tillabery, yayin da Malaman makarantu ke fuskantar barazana.

    Sakataren kungiyar ta malaman kwantaragi Munkaila Halidu ya yi wa Tchima Illa Issouffou karin bayani kan dalilansu na zuwa yajin aikin:

    Bayanan sautiSakataren kungiyar ta malaman kwantiragi na Nijar
  12. An samu karuwar wadanda suka kamu da kuma mutuwa sakamakon cutar coronavirus a Hubei

    An samu mutum 242 da suka mutu bayan sun kamu da cutar coronavirus a lardin Hubei na kasar China a ranar Laraba, rana mafi muni tun bayan barkewar cutar.

    Kazalika an samu karin wadanda suka kamu da cutar da suka kai dubu 14,840 a yanzu haka a sassan duniya.

    An kori wasu manyan ma'aikata a Hubei, sa'o'i bayan an sake samun wadanda suka kamu da cutar.

    Kafin ranar Laraba, wadanda ke kamuwa da cutar a Hubei ba su da yawa.

    Amma karin wadanda suka kamu da cutar a ranar Laraba, ya sa sun karu a fadin kasar ta China.

    Ana duba zafin wani mutum da na'urar auna zafin jikin mutum

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ana duba zafin wani mutum da na'urar auna zafin jikin mutum
  13. Sudan ta amince ta biya diyya ga Amurkawa

    Sudan ta sanya hannu a kan wata yarjejeniyar ta biyan diyya ga iyalan Amurkawan nan matuka jirgin ruwa da suka mutu a jirgin ruwan nan samufurin USS Cole, da aka sanyawa bam a gabar ruwan Yemen a shekarar 2000.

    Wannan wani sharadi ne da Amurka ta gindayawa Sudan domin a cire ta daga cikin jerin 'yan ta'adda.

    Ba a bayyana ko nawa za a biya diyyar ba.

    Kungiyar Al-Qaeda ta dauki alhakin kai hari kan jirgin yakin inda aka kai wa jirgin farmaki da ababen fashewa.

    Amurka ta dora dora alhakin a kan Sudan saboda 'yan kunar bakin waken da suka kai hari kan jirgin ruwan biyu, sun samu horo ne a Sudan din, abin da Sudan din ta musanta.

    Jirgin ruwa samfurin USS COLE

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Jirgin ruwa samfurin USS COLE
  14. Ana zanga-zanga a kan karancin fetur da buredi a Sudan

    Jama'a a Khartoum, babban birnin kasar Sudan na zanga-zanga a kan karancin fetur da buredi.

    Irin wannan bacin rai ya taba faruwa a karshen shekarar 2018 abin da ya haddasa mummunar zanga-zangar da ta janyo faduwar gwamnatin Shugaba Omar al-Bashir.

    Daya daga cikin matan da suke je shan mai a gidan mai ta shaida wa BBC cewa, sai ta yi jiran sa'o'i shida kafin ta samu mai.

    Kuma tana tare da 'ya'yanta a cikin mota abin da har sai da ya kai su dare har 'ya'yanta suka fara bacci a motar.

    An kebe layin mata masu shan mai daban, na maza ma daban.

    A kan bai wa maza biyar mai, sannan a ba wa mace guda, abin da ya janyo cacar baki.

    Mutane da dama dai sun bayyana cewa sun shafe dare suna layin mai, abin da ya harzuka su aka fara zanga-zanga.

    Mutane sun shafe tsawon dare a layin mai

    Asalin hoton, Tagreed Abdin

    Bayanan hoto, Layin Mai
  15. Kotu ta yi watsi da bukatar shugaban kasa

    Kotun tsarin mulki a Malawi ta yi watsi da daukaka karar da Shugaba Peter Mutharika da hukumar zaben kasar suka shigar inda suke so ta dakatar da hukuncin da ta yi makon jiya na soke zaben shugaban kasar.

    Kazalika kotun ta yi fatali da bukatar da hukumar zaben ta shigar cewa za a sake kashe makudan kudade wajen sake gudanar da zaben.

    Mai shari'a Dingiswayo Madise, ya ce mulkin dimokaradiyya yana da tsada amma 'yancin 'yan kasar yana da matukar muhimmanci.

    A makon jiya kotun ta yanke hukuncin da ya soke zaben da aka yi wa Mr Mutharika bisa zargin tafka magudi.

    Ta bukaci a sake gudanar da zaben nan da wata biyar.

    Peter Mutharika

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Peter Mutharika
  16. Ranar Rediyo Ta Duniya: Tasirin rediyo ga rayuwar matasa

    Ranar 13 ga watan Fabrairu rana ce da Hukumar bunkasa Ilmi da Al'adu da Kimiyya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ware don bikin ranar rediyo da inganta ayyukan hadin gwiwar kasashen duniya tsakanin kafofin yada labarai.

    Ranar tana karfafa gwiwar mahukunta su kirkiro tare da samar da hanyar samun bayanai ta hanyar rediyo ciki har da rediyon al'umma.

    Bikin dai na kokarin janyo hankulan jama'a ne kan tasirin rediyo wadda ta zama kafa mafi kai wa ga dumbin mutane kuma a yanzu take daukar sabbin siffofin fasahar zamani.

    Albarkacin wannan rana ta rediyo, BBC ta zanta da wani matashin mai sauraron rediyo, Zaidu Bala Kofar Sabuwa don jin ko wanne tasiri rediyo ta yi a rayuwarsa?

    Ku saurari hirar:

    Bayanan sautiHira da Zaidu Bala kan Ranar Rediyo Ta Duniya
  17. 'Yan majalisa sun amince a hukunta masu kalaman kiyayya

    Majalisar dokokin Ethiopia ta amince da kudurin dokar da zai hukunta duk mutumin da aka samu da laifin kalaman kiyayya da watsa labaran karya a jaridu da shafukan sada zumunta.

    Masu hamayya sun yi zargin cewa gwamnati za ta yi amfani da wannan doka domin hana masu adawa da ita tofa albarkacin bakinsu gabanin babban zaben da za a gudanar nan gaba a wannan shekarar.

    Zaben shi ne zai kasance na farko a Ethiopia tun bayan da shugaban kasar, wanda ya lashe kyautar Nobel kan zaman lafiya, Firai Minista Abiy Ahmed ya hau mulki a 2018.

    Ya kawo sauye-sauye a kundin tsarin mulkin kasar sannan ya sha alwashin gudanar da sahihin zabe.

    Masu hamayya sun yi zargin cewa gwamnati za ta hana su fadar albarkacin baki

    Asalin hoton, Getty Images

  18. 'Ina so na yi aure na haihu'

    Daga bakin mai ita wani shiri na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah.

    A wannan kashi na 14, shirin ya tattauna da Hadiza Aliyu Gabon, wata tauraruwar fina-finan Hausa.

    A cikin hirar, ta bayyana abubuwa da yawa da suka shafi rayuwarta da za su saku dariya da al'ajabi, ciki har da inda take hango kanta nan da shekara biyar.

    Bayanan bidiyo, Ina fatan in yi aure nan da shekara 5 - Hadiza Gabon
  19. 'Cin hanci ya yi katutu a hukumar kwallon kafar Afirka'

    Binciken da aka gudanar a asusun hukumar kwallon kafar Afirka (Caf) ya nuna cewa akwai matsaloli jingim a cikinta - musamman game da harkokin kudi da na gudanar da mulki.

    Hukumar Pricewaterhouse Cooper da ke gudanar da bincike kan harkokin kudi ta bayyana asusun Caf da cewa ba abu ne da 'za a dogara da shi ba kuma akwai rashin gaskiya' a cikinsa yayin da ta gano cewa kudin da caf ta kashe, wanda ya kai $20m, babu wata takarda da za ta nuna cewa an kashe shi.

    Hukumar ta bukaci a sake gudaar d bincike musamman kan 'rawar da shugaban caf' Ahmad da abokin aikinsa Loic Gerand, da sauransu suka taka a yarjejeniyar da suka kulla da kamfanin Tactical Steel na kasar Faransa- game da harkokin kudi.

    Ahmad ya musanta zargin aikata ba daidai ba.

    Ahmad ya musanta zargin aikata ba daidai ba.

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ahmad ya musanta zargin aikata ba daidai ba.
  20. An sake tuhumar Sowore da laifin cin amanar kasa

    Gwamnatin Najeriya ta sake gurfanar da mawallafin jaridar Saraha Reporter, Omoyele Sowore, a gaban kotu inda take zarginsa da laifuka biyu --yunkurin cin amanar kasa da kuma cin amanar kasa.

    Lauyoyin gwamnati sun zargi Sowore da aikata wadannan laifuka ne lokacin da ya sake gurfana a gaban wata kotu da ke Abuja, babbab birnin Najeriya ranar Alhamis domin ci gaba da shari'ar da ake yi masa.

    Sai dai ya musanta aikata laifukan.

    Kotun ta ware ranakun 11,12 da 13 ga watan Maris domin yin shari'a a kan wadannan sabbin tuhume-tuhume.

    Sowore