Twitter ya fito da ka'idojin yaki da labaran karya

Asalin hoton, Getty Images
Shafin Twitter ya fito da wasu sabbin ka'idoji domin maganin yada labaran karya ko masu karin gishiri a dandalin.
Manufar wannan matakin ita ce yin maganin matsalar saka bidiyo-bidiyo na bogi da aka hada ta hanyar amfani da na'ura mai kwalkwalwa, inda ake sauya kamannin mutum ko kuma furucinsa.
Twitter din zai fara aiwatar da wadannan ka'idojin a watan Maris.
Twitter ya ce ya dauki matakin ne sakamakon wani bincike na baya-bayan nan, wanda ya ji ra'ayoyin mutum 6,500.
An zabo mutanen daga kungiyoyin farar hula da malamai da kuma jama'ar gari.
Matakin na Twitter na zuwa ne kusan wata guda bayan Facebook ya sanar cewa zai cire bidiyo-bidiyo da aka sauya asalinsu ta hanyar amfani da ma'aikatansa da kuma masu bincike don tantance sahihancin bidiyo-bidiyo din.


















