Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da sassan duniya

Wannan shafin ya kawo muku labaran abubuwan da suka faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Yadda ake kula da masu fama da ciwon damuwa a Nijar

    Bayanan sautiLatsa nan don sauraron cikakken rahoton wakiliyar BBC Tchima Illa Issoufou kan masu fama da ciwon damuwa a Nijar

    Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa masu fama da rashin lafiya da dama a kasar na fama da matsalar matsananciyar damuwa.

    Kuma tuni hukumomi a kasar suka samar da kwararru a kan wannan fanni cikin asibitoci don taimaka wa masu fama da ciwon damuwa.

    Wata Jami'a da ke kula da sashen masu fama da damuwa a wani babban asibiti da ke Yamai, babban birnin kasar Aishatu Bukar ta shaida wa BBC cewa suna ba da shawarwari ga mutanen da suke fama da wannan matsala.

    Ta bayyana cewa ''muna bin masu fama da cutar sannu a hankali har sai an samar musu da mafita.''

  2. Uefa za ta taimaka wa mata 'yan kwallon kafa a Kamaru

    Tsohuwar 'yar kwallon kafar Netherlands Hesterine De Reus tana so a zuba jari kan harkokin kwallon kafar mata a Kamaru domin biyan bukatar masu sha'awar kallon kafar.

    Tsohuwar kocin ta Australiya mai shekara 58 ta ce harkar kwallon kafa a kasar za ta bunkasa ne kawai idan aka hada hannu sannan aka yi wasu sauye-sauye.

    Ta bayyana haka ne bayan ziyarar da ta kai kasar ta Kamaru kwanakin baya a wani shiri da hukumar kwallon kafar turai, Uefa, ta dauki nauyinsa.

    Hesterine De Reus

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Yau ce ranar yaki da yi wa mata kaciya ta duniya

    Bayanan sautiSaurari rahoton Mukhtar Adamu Bawa kan ranar yaki da kaciyar mata a duniya

    Yau ce ranar da aka kebe domin inganta wayar da kai da gangami wajen yaki da kaciyar mata a duniya.

    Wani kiyasi na Majalisar Dinkin Duniya na cewa a 2020 kadai, akwai 'yan mata sama da miliyan hudu a fadin duniya da ke cikin hatsarin fuskantar kaciya.

    'Yan matan da ake yi wa kaciya sukan yi fama da larurori na dan lokaci ciki har da matsanancin ciwo da zubar jini da dai sauran matsalolin da suka shafi jima'i da haihuwa.

    Mukhtar Adamu Bawa ya duba mana wannan batu kuma ya hada rahoto na musamman.

  4. An samar da ma'aikatan sa kai miliyan daya a Najeriya don yakar Corona

    Hukumar ba da agaji ta Red Cross a Najeriya ta ce ta samar da ma’aikatan sa kai miliyan daya a fadin kasar cikin shirin ko ta kwana domin dakile sabuwar cutar Coronavirus da ke ci gaba da yaduwa a duniya.

    Da yake zantawa da manema labarai a Abuja babban birnin kaar, babban sakataren hukumar Abubakar Ahmed Kende ya ce, sun dauki wannan matakin ne domin kare shigowar wannan cuta da kuma kara dakile yaduwar cutar zazzabin Lassa a fadin kasar.

    Ga rahoton da Buhari Muhammad Fagge ya hada mana:

    Bayanan sautiRahoton Buhari Fagge kan shirin Red Cross na yakar Corona
  5. An samu gawar wani saurayi da wata budurwa tsirara a wani gida a Kano

    'Yan sanda a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da samun gawar wani saurayi da wata budurwa tsirara a dakin girki a wani gida da ke unguwar Badawa.

    Sai dai har yanzu ba a tabbatar da dalilin mutuwar tasu ba, amma 'yan sandan sun ce suna bincike kan lamarin.

    Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya

    Asalin hoton, @POLICENG

  6. 'Rikicin ta-da-kayar baya na ci gaba da ruruwa a Najeriya'

    Bayanan sautiSaurari hira da Barista Audu Bulama Bukarti kan Kungiyar Ansaru

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun yi nasarar kashe mutanen da ta kira manyan 'ya'yan kungiyar 'yan ta'adda na kungiyar Ansaru 250 a dajin Kuduru da ke yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna.

    Ta ce sun kashe mutanen ne yayin wani samame da suka kai bayan samun bayanai game da wani makeken sansanin miyagun masu aikata laifuka a dajin.

    Kaduna, jiha ce da ke fama da karuwar tabarbarewar tsaro sakamakon hare-hare kan kauyuka da kuma satar mutane don neman fansa a tituna da garuruwa.

    Wani mai bincike kan ayyukan 'yan-ta-da-kayar-baya a yankin Takin Chadi Barista Audu Bulama Bukarti ya shaida wa BBC cewa bai yi mamakin harin ba saboda a cewarsa ''kungiyar Ansaru ta kafu ne a yankin arewa maso gabashin Najeriya.''

    ''Ita Ansaru asalinta 'yan kungiyar Boko Haram ne wadanda ba sa jin dadin abin da shugabansu yake a lokacin wato Abubakar Shekau suka fice daga kungiyar.'' in ji sa.

    Ya ce ''sun kafa wata sabuwar kungiya inda suka ce ba za su kashe 'yan ba ruwana ba, za su kai hare-hare a kan gwamnati da sojoji da mutanen kasar waje da wadanda ba Musulmi ba.''

  7. An jinkirta yanke hukunci kan 'yan luwadi a Najeriya

    Alkalin wata kotu a Najeriya ya sake jinkirta yanke hukunci kan 'yan kasar 47 wadanda ake zargi da “fito da sha'awarsu ta yin luwadi a bainar jama'a” bayan daya daga cikin manyan masu bayar da shaida a kan shari'ar ya gaza zuwa kotun.

    A zaman kotun na ranar Laraba, mai shari'a Rilwan Aikawa ya nuna damuwarsa saboda rashin zartar da hukunci kan batu sakamakon rashin bayyanar shaidar a gaban kotun, a cewar wakiliyar BBC Mayeni Jones.

    A kalla sau uku ana jinkirta shari'ar saboda rashin gabatar da cikakkun bayanai a gaban kuliya, in ji kamfanin dillancin labarai na Reuters..

    Alkalin ya gargadi masu shigar da kara cewa zai kori karar a zama na gaba idan suka gaza gabatar da shaidar.

    'Yan sanda sun kama mutanen ne a wata Agustan 2018 a samamen da suka kai a wani otal a birnin Lagos.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa za a iya yanke musu hukuncin daurin shekara 10 a gidan yari idan aka same su da laifi.

    gudumar kotu

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Dokar yi wa hanyoyin samun kudin shiga kwaskwarima ta janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya

    Bayanan sautiSaurari abin da dokar yin garambawul ga hanyoyin samun kudin shiga a Najeriya garambawul ta kunsa

    Masana a ciki da wajen Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a kan sabuwar dokar da ta yi wa hanyoyin samun kudin shiga a kasar kwaskwarima.

    A farkon wannan wata na Fabrairu ne dai dokar, wadda Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kai cikin watan jiya ta fara aiki.

    Hakan ya zo ne bayan da majalisar dokokin kasar ta amince da kudirin a karshen shekarar da gabata.

    Amma wasu bangarori na dokar sun jawo ce-ce-ku-ce.

    Wakilin BBC Muhammad Kabir Muhammad ya yi nazari a kan abin da dokar ta kunsa, da kuma yadda za ta shafi talaka a Najeriya.

  9. Hoton Jacob Zuma rike da bindiga ya jawo ce-ce-ku-ce

    Tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, ya jawo ce-ce-ku-ce bayan da ya wallafa wani hotonsa rike da bindiga yana saita wani wuri a shafinsa na Twitter.

    Ya wallafa hoton ne kwana daya bayan wata kotu ta bayar da sammacin kama shi.

    Babbar kotun ta Pietermaritzburg ta bayar da sammacin kama tsohon shugaban kasar ranar Laraba bayan da ya ki gurfana a gabanta.

    Lauyansa ya ce ba zai iya zuwa kotun ba saboda ba shi da lafiya - ko da yake masu shigar da kara sun ki yarda da hakan.

    Za a kama Mr Zuma ne kawai idan kotun ta tabbatar da ya yi karya kan batun rashin lafiyar tasa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. Ciwon koda yana karuwa a Borno

    Gwamnatin jihar Borno da ke arewacin Najeriya ta gayyaci masana kimiyya dmin su gudanar da bncke kan yawaitar ciwon koda a jihar.

    Wata sanarwa da Isa Gusau, mai magana da yawun gwamna jihar, Babagana Umara Zulum ya fitar ta ce masana za su gudanar da bincke ne kan ruwan sha da muhalli da kuma sauran abubuwan da ke haddasa ciwon koda.

    A cewar sanarwar, Gwamna Zulum ya dauki matakin sakamakon halin da ya ga masu fama da ciwon koda lokacin da ya kai ziyara a asibitin kula da masu ciwon koda da ke Maiduguri a watan Disambar da ya gabata.

    Gwamnan ya bukaci ma'aikatar kimiyya ta jagoranci takwarorinta na lafiya da albarkatun ruwa wajen kawo karshen wannan ciwo.

    Babagana Umara Zulum

    Asalin hoton, @ProfZulum

  11. Ashe mawakin Amurka Lil Wayne dan Najeriya ne?

    Wata jami'ar gwamnatin Najeriya ta yi maraba da mawakin nan dan kasar Amurka Lil Wayne bayan da ya ce gwajin kwayoyin halitta da ya yi ya nuna cewa kakaninsa 'yan asalin Najeriya ne.

    Mai taimaka wa Shugaba Muhammadu Buhari kan sha'anin 'yan kasashen waje, Abike Dabiri, ta bayyana Wayne a matsayin "dan uwanmu dan Najeriya".

    Ms Dabiri ta ce tana fatan yi masa marhabin idan ya je Najeriya.

    Wayne ya shaida wa gidan talbijin na Revolt TV cewa gwajin kwayoyin halittar ya nuna cewa kashi 53 na tsatsonsa daga Najeriya suke kuma yana fatan kai ziyara kasar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. An samu bullar coronavirus a kasar Ghana

    Jami'an lafiya a Ghana na gudanar da bincike kan mutum biyu da ake zargi sun kamu da cutar numfashi ta coronavirus a Accra, babban birnin kasar.

    Mutanen, guda dan kasar China ne, yayin da dayan kuma dan kasar Argentina ne, wadanda ke zaune tare amma sun yi balaguro zuwa China a ranaku daban-daban.

    Sun mika kansu ga sashen kula da masu bukatar gaggawa na asibitin koyarwa na Korle Bu da ke Accra ranar Laraba bayan wani asibitin kudi da suka je ya ki karbar su.

    Sun yi korafin fama da mura da tsamin gabban jiki.

    Jami'ai sun ce dan kasar ta Argentina ya isa Accra ne daga birnin Shanghai watan jiya, yayin da shi kuma dan kasar China ya isa birnin tun watan Satumba na 2019.

    Sakataren kungiyar likitoci ta Ghana, Dr William Baah, ya ce an killace mutanen biyu bayan da aka dauki jininsu domin yin gwaji.

    Likitoci

    Asalin hoton, Getty Images

  13. Jami'an kwastam sun lalata kayan kidan mawakin Mali

    Mawakin nan dan kasar Mali Ballake Sissoko ya yi ikirarin cewa ma'aikatan kwastam na Amurka sun lalata kayan kidansa lokacin da suke binciken kayansa.

    Mr Sissoko yana kidan goge.

    Ya ce lokacin da ya koma birnin Paris ranar hudu ga watan Fabrairu ya bude kayan kidansa inda ya ga sun kakkarye.

    Ya ga wata takardaar jami'an kwastam na Amurka a cikin jakarsa inda suka ce sun bude jakar ne domin yin bincike.

    Sai dai babu wani cikakken bayani kan ko a wanne lokaci ne kayan kidan nasa suka fashe.

    Har yanzu jami'an kwastam na Amurka basu bayar da amsa kan neman bayanin da BBC ta yi daga gare su kan wannan batu ba.

    Ballake Sissoko

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ballake Sissoko
  14. 'Yan sanda 'sun muzanta matar da aka yi wa fyade a Najeriya'

    Lauyan da ya taimaka wa wata mata ta shigar da kara wurin 'yan sanda kan fyaden da wasu suka yi mata ya yi zargin cewa 'yan sandan sun musguna mata.

    Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta bayyana haka a wani rahoto da ta fitar ranar Alhamis.

    Lauyan mai suna Goodness Ibangah ya ce matar mai shekara 21 ta shigar da kara a ofishin 'yan sanda da ke jihar Enugu a karkashen watan Janairun 2020 bayan da ta ki amincewa da rokon da suka yi mata na neman sulhu da wanda ya yi mata fyaden ba a wajensu ba.

    Sai dai, a cewar Human Rights Watch, 'yan sandan sun kai samame ofishin kungiyar kare hakkin mata ta the Women's Aid Collective (WACOL), inda a can ne Ibangah take aiki sannan suka muzanta ta.

    "Wannan halayya ta 'yan sanda abar allawadai ce kuma ta keta hakkin dan adam da ya kamata su kare," a cewar Anietie Ewang, mai bincike a kungiyar Human Rights Watch a Najeriya.

    Sufeton 'Yan sanda

    Asalin hoton, Facebook

  15. Barkamun da sake saduwa

    Muna yi muku barka da sake saduwa a wannan shafi da ke kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da wasu sassan duniya. Da fatan za ku ci gaba da kasancewa tare da mu a ko da yaushe. Kuna iya aiko mana da rahotannin abubuwan da ke faruwa a yankunanku a imel dinmu: hausa@bbc.co.uk

  16. Kammalawa

    Karshen rahotonnin kai-tsaye kenan daga Umar Mikail da Nabeela Mukhtar Uba. Kafin mu, Nasidi Adamu Yahaya ne da Halima Umar Saleh suka kawo maku bayanan.

    Mu hadu gobe Alhamis.

    Kafin nan, ku duba kasa domin karanta labaran ranar Laraba.

  17. Uganda ta killace mutum 100 saboda coronavirus

    Ma'aikatar lafiya ta kasar Uganda ta ce an killace sama da mutum 100 da suka isa kasar daga China domin hana bazuwar cutar coronavirus.

    Ministar lafiya Dr Jane Aceng ta fada wa manema labarai a Kampala, babban birnin kasar, cewa 44 daga cikin mutanen da aka killace 'yan China ne.

    Ta kuma ce ma'aikatar ba ta da masaniyar wani dan kasarta da ake zargin ya kamu da cutar.

    Kasar ta kuma tsananta matakan tantance mutanen da suke shiga kasar sannan ta bukaci matafiyan da suka fito daga China su gabatar da bayanansu domin jami'an lafiya su duba su.

    Gwamnatin ta ce akwai daruruwan daliban Uganda a China amma ta ce babu wani shirin kwashe su daga kasar.

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

  18. Coronavirus: WHO na neman tallafin ‎naira biliyan 245

    Coronavirus

    Asalin hoton, WHO

    Hukumar lafiya ta duniya WHO ta nemi tallafin dala miliyan $675, kwatankwacin kusan naira biliyan 245, domin yaki da cutar coronavirus ta hanyar zuba hannun jari a kasashen da suke cikin hadarin kamuwa da cutar.

    Shugaban WHO Tedros Ahanom Ghebreyesus ya bayyana hakan a wani taron manema labarai na duniya da aka gudanar a Geneva babban birnin kasar Switzerland.

    Ya ce milyan $60 na kudin zai zama na amfanin WHO, yayin da ragowar kudaden kuma za a taimaka wa kasashe don kare su daga coronavirus.

    A cewarsa, WHO za ta aike takunkumin kariya 500,000 da abin shakar iska 40,000 zuwa ga kasashe 24.

    Tedros ya kuma yaba da tallafin miliyan $100 daga gidauniyar Bill and Melinda Gates domin yin gwajin cutar da kula da masu ita da kuma bincike kan maganinta.

  19. Gwamnan Borno ya kwana biyu a Monguno don iza harsashin gina wa 'yan gudun hijira gidaje

    Gwamnan Borno

    Asalin hoton, @ProfZulum

    Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya Babagana Umara Zulum ya kai ziyara Monguno inda ya shafe kwana biyu a garin.

    Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan kan harkokin yada labarai Isa Gusau ya aike wa BBC a ranar Laraba.

    Yayin ziyarar, gwamnan ya iza harsashin ginin gidaje 1,000 domin 'yan gudun hijira da suka yada zango a makarantu.

    Gwamnan ya kuma iza harsashin ginin makarantar Islamiyya wadda za ta samar wa da mutum 10,000 da ke da ilimin addinin Musulunci damar samun difloma a ilimin zamani.

    Akwai 'yan gudun hijra 89,000 da ke zaune a Monguno wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.

    Kwamishinan sake gina Borno Injiniya Mustapha Gubio ya ce an iza harsashin gina rukunin gidajen domin samar wa 'yan gudun hijrar wajen zama.

    Ya ce hakan zai bai wa makarantun da 'yan gudun hijrar suka mamaye damar komawa bakin aiki.

  20. Wani jirgin fasinja ya tarwatse a Turkiyya

    Turkiyya

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani jirgin sama ya jirkice a wata tashar jiragen sama da ke Turkiyya inda ya tarwatse tare da raunata mutum 21, a cewar jami'ai.

    Jirgin a cewar rahotanni yana dauke da fasinjoji 171 da ma'aikatan jirgin shida lokacin da ya fado a filin jirgin saman Sabiha Gokcen a Santanbul.

    Ministan sufuri Mehmet Cahit Turhan ya ce ba a samu asarar rai ba.

    Gwamnan Santanbul Ali Yerlikaya ya ce an garzaya da mutum 21 asibiti sannan ana ci gaba da kwashe mutanen da abin ya rutsa da su.

    Jirgin na Pegasus Airlines ya sauka ne cikin mamakon ruwan sama bayan ya tashi daga lardin Izmir kamar yadda kafafen yada labaran Turkiyya suka rawaito.

    Jami'ai kuma na ci gaba da kokarin zakulo wadanda suka makale cikin jirgin.

    Hoton bidiyo da ke watsuwa a shafukan sada zumunta ya nuna wuta ta tashi a jirgin saman sai dai daga bisani masu kashe gobara sun kashe wutar.