Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da sassan duniya

Wannan shafin ya kawo muku labaran abubuwan da suka faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Nabeela Mukhtar Uba

  1. 'Rashin iska ne ya kashe daliban da suka a turmutsin Kenya'

    Rahotanni daga Kenya na cewa shida daga cikin dalibai 14 da suka mutu sakamakon turmutsitsin da aka yi a yammacin kasar sun mutu ne sakamakon rashin iska kamar yadda gwajin da aka yi kan gawarwakinsu ya tabbatar.

    Wani likita Dickson Mchana ya ce tawagarsa na ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar sauran daliban takwas a turmutsitsin da aka yi a makarantar firamare ta Kakamega da yammacin Litinin.

    Dakta Mchana ya kara da cewa ''lokaci na neman kure musu yayin da suke neman karasa binciken sannan su shirya gawarwakin domin iyalan mamatan su karbe su domin yi musu jana'iza a filin wasa na Bukhungu da ke Kakamega.''

    'Yan sanda su ma suna gudanar da nasu binciken kan lamarin da ya yi sanadiyyar raunata wasu daliban 39.

    Sun samu bayanai daga malamai da dalaibai da wasu da abin ya faru kan idonsu domin gano abin da ya haddasa turmutsitsin.

    Biyu daga cikin daliban dai na samun kulawa a asibitin Kakamega.

    Kenya
  2. Likitan da ya ja hankali kan coronavirus ya mutu

    Mutuwar likitan da ya rika jan hankalin hukumomin China kan yaduwar cutar coronavirus ta jawo kakkausan suka a kasar.

    Li Wenliang ya mutu ne bayan ya kamu da cutar sakamakon kula da yake yi wa masu dauke da cutar a Wuhan, inda cutar ta fi kamari.

    A watan Disambar da ya wuce, ya aike da sako ga ‘yan uwansa likitoci inda ya yi gargadin cewa ya gano wata cuta wacce ta yi kama da cutar Sars – cutar da ke sarkafe numfashi.

    Amma ‘yan sanda sun bukaci ya "daina watsa labaran karya" sannan aka bincike shi kan "yada jita-jita".

    Li Wenliang

    Asalin hoton, DR LI WENLIANG

    Bayanan hoto, Li Wenliang
  3. An kashe shugaban Al-Qaeda na Yemen

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce kasarsa ta kashe shugaban kungiyar Al-Qaeda na yankin Larabawa.

    Fadar White House ta ce an kashe Qasim al-Raymi, wanda ya shugabanci kungiyar tun 2015, a wani samame da dakarun Amurka suka kai Yemen.

    Ana alakanta al-Raymi da hannu wajen kitsa kai jerin hare-hare kan hukumomin kasashen Yammacin duniya tun shekarun 2000.

    Ya zama shugaban Al-Qaeda ne bayan an halaka mutumin da ya gada a yayin wani hari da Amurka ta kai masa da jirgi maras matuki.

    An kafa reshen Al-Qaeda na kasashen Larabawa ne a 2009 daga bangarori biyu na kungiyar da ke Al-Qaeda da Yemen da Saudi Arabia, da zummar kawar da gwamnatocin da Amurka ke mara wa baya da kuma hukumomin Amurka da ke yankin.

    Qasim al-Raymi

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Qasim al-Raymi ya zama shugaban Al-Qaeda ne bayan an halaka mutumin da ya gada
  4. Masu yi wa kasa hidima sun gode wa Buhari

    Matasan da ke yi wa kasa hidima a Najeriya sun kai ziyarar godiya ga shugaban kasar Muhammadu Buhari.

    Wannan ziyara na zuwa ne kwanaki kadan bayan gwamnatin kasar ta soma biyan kowanne mai yi wa kasar hidima N3300 duk wata.

    A baya dai ana biyansu N19,800 kowanne wata a matsayin alawus.

    Wani sako da shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce masu yi wa kasar hidima sun je wurinsa ne domin su bayyana jin dadinsu kan matakin da gwamnati ta dauka na kara musu alawus.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Barkanmu da sake saduwa

    Da fatan masu bibiyarmu kun wayi gari lafiya. Kuma muna fatan za ku sakce tare da mu tsawon wannan ranar ta Juma'a domin samun labarai da rahotanni da ma sharhi kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da wasu sassan duniya.

  6. Sai da safen mu

    A nan muka kawo karshen labarai da rahotanni da muke kawo muku na wannan lokaci.

    Ku tara ranar Juma'a domin jin wainar da ake toyawa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da wasu sassan duniya.

    Ka da ku manta za ku iya ci gaba da karanta sauran labarai a shafinmu na intanet bbchausa.com, sannan ku bibiye mu a shafukan sada zumunta.

    Mun gode

  7. Buhari ya karbi rahoton masu ba da shawara kan tattalin arziki

    Shugaban Najeriya Muhammadu ya ce masu ba shi shawara kan tattalin arziki sun mika masa kwarya-kwaryar rahoto.

    A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban kasar ya ce sun ba shi shawarwari da dama wadanda ya ce zai sanya su cikin tsarinsa na bunkasa tattalin arziki.

    A cewarsa, tuni ya bayar da umarnin gaggawa ga sakataren gwamnatin kasar domin ya dauki mataki kan yadda za a cike gibin da ake samu a tsakanin ma'aikatun gwamnati.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Hatsarin mota ya kashe sojojin Kamaru biyu

    Wasu sojoji biyu da ke aiki da bataliyar soji ta 12 da ke Jamhuriyyar Kamaru sun gamu da ajalinsu yayin wani hatsarin mota a garin Kaigama da ke gabashin kasar.

    Bayanai sun ce karin wasu sojojin sun jikkata a yayin aukuwar lamarin.

    Ga rahoton Muhamman Babalala daga Kamaru:

    Bayanan sautiRahoton Babalala kan hatsarin sojojin Kamaru
  9. 'Yan sanda a Najeriya sun kashe manyan kwamandojin Ansaru da ake nema ruwa a jallo

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta halaka wasu kwamandojin kungiyar ta-da-kayar-baya ta Ansaru biyu da ake nema ruwa a jallo.

    Rundunar ta bayyana hakan ta shafinta na Twitter ranar Alhamis.

    Ta ce ta kai harin ne a dajin Kuduru da ke Birnin Gwari a jihar Kaduna.

    Ta kara da cewa an kame wasu 'yan ta'adda uku tare da gano wasu kunshin makamai masu yawa.

    Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da rundunar 'yan sandan mai yaki da 'yan fashi ta Operation Puff Adder ta ce ta kai samame wani sansanin kungiyar 'yan bindiga ta Ansaru, inda ta kashe 250 daga cikinsu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. An kafa kwamitin yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya garambawul

    Shugaban majalisar dattawa a Najeriya Ahmad Lawan a ranar Alhamis ya kafa kwamitin mutum 56 domin yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul.

    Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar Ovie Omo Agege.

    Sannan kuma ya kunshi wasu manyan jami'an majalisar guda takwas - sanata daya daga jihohi 36 sannan da mambobi biyu da ga yankuna shida da ake da su a kasar.

    Wasu daga cikin mambobin kwamitin sun hada da shugaban masu rinjaye na majalisar Yahaya Abdullahi, da mataimakinsa Farfesa Robert Ajayi Boroffice.

    Akwai kuma shugaban marasa rinjaye Eyinnaya Abaribe da mataimakinsa Sanata Emmanuel Bwacha

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. INEC ta sanar da ranar zaben cike gurbi na 'yan majalisar tarayya

    Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta sanya ranar Asabar 19 ga watan Satumbar 2020 domin gudanar da zaben gwamnan jihar Edo.

    Haka kuma hukumar ta sanya 10 ga watan Octoban 2020 a matsayin ranar zaben gwamnan jihar Ondo.

    Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana haka ranar Alhamis din nan yayin taron manema labarai a babban ofishin hukumar da ke Abuja.

    Farfesa Mahmud ya kara da cewa INEC za ta gudanar da zaben cike gurbi na wasu 'yan majalisar tarayya na kasa da na jihohi a ranar 14 ga Maris na 2020.

    Mazabun sun hada da ta dan majalisar tarayya mai wakiltar Magama/Rijau a jihar Niger.

    Sai kuma mazabar dan majalisar dokokin jihar Kwara a mazabar Fetigi.

    Haka kuma za a gudanar da zaben na kujerar dan majalisar dokokin jiha mai wakiltar Kebe a jihar Sokoto.

    Shugaban na INEC ya ce za a gudanar da zabukan na cike gurbi sakamakon mutuwar wakilan da ke wakiltar mazabun.

    INEC

    Asalin hoton, INEC NIGERIA

  12. Kudirin bai wa kananan hukumomin Najeriya 'yancin gashin kai ya wuce karatu na biyu

    Rahotanni daga Najeriya na cewa kudirin bai wa kananan hukumomin kasar damar cin gashin kansu ya samu wucewa karatu na biyu a zauren majalisar wakilai ranar Alhamis.

    Kudirin kuma na neman bai wa kananan hukumomin wa'adin zangon mulki na bai daya a sassan jihohin kasar.

    Kudirin wanda dan majalisa Mansur Soro ya gabatar yayin da yake jagorantar muhawara kan kudirin, ya ce abin da ake gani a kasar yanzu ya sha bamban da tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya.

    ''Kananan hukumomi ba su da 'yanci a siyasance saboda gwamnatocin jihohi na yi musu karen tsaye a zabukansu.''

    Mataimakin shugaban majalisar, Ahmed Wase wanda ya jagoranci zaman majalisar ya bayyana cewa ba kowace jiha ba ce ta gudanar da zaben kananan hukumomi ba sannan wasu gwamnonin ba su sa baki a harkokin kananan hukumomin.''

    Majalisar wakilai
  13. An samu mutum na uku da ya kamu da coronavirus a Birtaniya

    An samu mutum na uku da ya kamu da cutar Corona a Birtaniya, a cewar babban jami'in lafiya a kasar.

    Mutumin wanda ya kamu da cutar a wata kasa, yana samun kulawar likitoci a cibiyar kula da marasa lafiya ta NHS.

    ''Muna amfani da matakan dakile yaduwar cutar,'' in ji Farfesa Chris Whitty.

    Mutum 28,256 a fadin duniya sun kamu da cutar sannan ta halaka wasu mutum 565 - akasarinsu a China.

    Farfesa Whitty ya ce asibitin a shirye yake ya kula da cutar inda ya kara da cewa ''muna aiki domin gano mutanen da mutumin ya yi mu'amala da su.''

    Wasu karin marasa lafiya biyu - dukkansu 'yan China na ci gaba da samun kula a cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa da ke Newcastle.

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

  14. 'Yan sandan Isra'ila sun harbe mutumin da ya bude musu wuta

    'Yan sanda a Isra'ila sun ce sun harbe wani Bafalasdine da suka ce ya bude wuta kan jami'ansu a Birnin Kudus.

    Lamarin kuma ya yi sanadiyyar jikkatar wani daga cikin 'yan sandan.

    A baya-bayan nan ne, sojojin Isra’ila suka kashe Falasdinawa biyu a yankin Jenin da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan.

    Sojojin sun ce rikici ya barke yayin da aka rushe gidan wani mutum da ake zargi da hannu a kisan wani dan Isra'ila shekara biyu da suka gabata.

    Isra’ilawa 12 ne suka ji rauni lokacin da Bafalasdinen ya durfafi ayarin sojojin a birnin Kudus - fararen hula biyu ne suka jikkata.

    Tashin hankali ya fara munana ne tun bayan da Shugaba Trump ya sanar da shirinsa na samar da zaman lafiya.

    Isra'ila

    Asalin hoton, Getty Images

  15. China ta bullo da matakan dakile yaduwar coronavirus

    Hukumomi a kasar China sun bullo da wasu matakai da zasu taimaka wajen dakile yaduwar cutar numfashi ta Corona.

    A lardin Hubei inda aka samu barkewar annobar ana dakatar da amfani da lifta a manyan gine-gine don hana mutane fita.

    A birnin Beijing, hukumomi sun hana cin abinci a cikin taron jama'a yayin bukukuwan haihuwa ko kuma na aure.

    Har ila yau, ana ci gaba da kara kauracewa kasar ta China.

    Yanzu haka dai Taiwan ta haramta wa wasu 'yan kasar China shiga yankinta.

    Coronavirus

    Asalin hoton, EPA

  16. Labarai da dumi-dumi, INEC ta rage jam'iyyun siyasar Najeriya zuwa 18

    Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta sanar da cewa ta mayar da jam'iyyun siyasar kasar zuwa 18 daga 91.

    Shugaban hukumar Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Alhamis.

  17. An ba da hutu a Kenya domin yin jana'izar arap Moi

    Hukumomi a Kenya sun ayyana Talata 11 ga watan Fabrairu a matsayin ranar hutu domin 'yan kasar su samu damar zuwa jana'izar ban girma ga tsohon shugaban kasar Daniel arap Moi.

    Mr Moi ya mutu ranar Talata hudu ga watan Fabrairu a wani asibiti mai zaman kansa da ke Nairobi babban birnin kasar yana da shekara 95 a duniya.

    Ya shafe shekara 24 yana shugabancin kasar.

    Da yake sanar da mutuwar Mr Moi, Shugaba Uhuru Kenyatta ya ce za a yi tsohon shugaban kasar jana'izar ban girma, wacce farar hula da soji za su halarta.

    Ranar Alhamis, ministan cikin gidan kasar, Fred Matiangi, ya sanar cewa hutun zai bai wa 'yan kasar damar halartar jana'izar domin nuna girmamawa ga tsohon shugaba kasar.

    Daniel Moi ya zama shugaban Kenya a 1978

    Asalin hoton, Getty Images

  18. Afirka ta Kudu da Jamus za su kulla yarjejeniyar kasuwanci

    Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa na karbar bakuncin Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel a Pretoria, babban birnin kasar inda suke yin taro kan kasuwacin.

    Jami'an gwamnatin Jamus da 'yan kasuwa masu zaman kansu ne suka yi wa Ms Merkel rakiya inda suke fatan kulla yarjajeniyar da za ta kai ga zuba jari a kasar.

    Afirka ta Kudu ce babbar kawar Jamus a fannin kasuwacin a nahiyar Afirka, inda aka yi kiyasin kamfanonin kasar fiye da 600 na kasuwacin a Afirka ta Kudu.

    Huldar kasuwacin da ke tsakanisu ta kai ta $6.7bn, galibi daga harkokin injina da kayan kere-kere.

    Ramaphosa da Merkel

    Asalin hoton, Getty Images

  19. Shugaba Buhari ya kaddamar da sabbin jiragen yaki

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu sabbin jiragen yaki masu saukar ungulu.

    hotunan da mai taimaka wa shugaban kan kafafen sada zumunta na zamani Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter sun nuna shugaban kasar tare da wasu jam'in gwamnati da na soji suna kaddamar da jiragen.

    A cewarsa, akwai wasu karin jirage 17 da ake sa ran za a samar nan gaba.

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

  20. Jariri sabuwar haihuwa ya kamu da cutar Coronavirus

    An gano cewa wani jariri dan China ya kamu da cutar coronavirus kimanin awa 30 bayan an haife shi, a cewar kafofin watsa labarai na kasar.

    An haifi jaririn ranar biyu ga watan Fabrairu a Wuhan, wato inda cutar ta fi kamari.

    Da ma dai mahaifiyar jaririn ta kamu da cutar tun kafin ta haife shi. Har yanzu ba a san yadda jaririn ya kamu da cutar ba - yana ciki ko bayan an haife shi.

    Yaran da suka kamu da cutar ba su da yawa, a yayin da coronavirus din ta kashe akalla mutum 565, sannan mutum 28,018 suka kamu da ita.

    .

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images