Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da sassan duniya

Wannan shafin ya kawo muku labaran abubuwan da suka faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Rufewa

    To masu bin mu a wannan shafi a daidai wannan lokaci muke cewa sai wani makon idan Allah Ya kai mu ranar Litinin, za mu zo muku dauke da labaran abubuwan da ke faruwa a duniyar.

    Kafin sannan, a madadin wadanda suka yi aikin na yau kamar Nasidi Adamu Yahaya, da Nabila Mukhtar Uba, ni Sagiru Kano Saleh nake cewa, Allah Ya sada mu da alkhairan wannan yammaci.

    Sai da safe.

  2. Mutum 180,000 sun yi gudun hijira a cikin wata daya, Hakan ya auku ne a watan Disamba a arewa maso yammacin Syria, inji MDD

    Mutane dubu dari da tamanin da takwas ne suka rasa matsugunansu sakamakon rikice-rikice a arewa maso yammacin Siriya tun daga farkon watan Disamba.

    Ana kuma hasashen rikicin zai tilasta wa karin kusan rabin adadin tserewa, yayin da sojojin gwamnatin Syria, da ke samun goyon bayan Rasha, ke ci gaba da kwace yankunan da ke hannun 'yan tawaye.

    Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana wadanda aka tilastawa barin gidajensu a matsayin mutane masu rauni a duniya. Majalisar ta ce tashin bama-bamai ya tilasta wa mutanen tserewa zuwa kananan yankuna.

    An kashe fararen hula kusan hamsin a cikin kwanakin farko na wannan watan nan kadai. Sojojin Siriya suna ci gaba da fuskantar wasu kungiyoyin 'yan tawaye, wadanda ake danganta su da kungiyar masu da'awar jihadi ta al-Qaeda.

    Harin Idlib a Syria

    Asalin hoton, AFP

  3. Kamfanin iPhone zai taimaka wajen rage coronavirus

    Annobar coronavirus a Wuhan

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin kayan laturoni na Foxconn mai kera wayoyin iPhone, zai bullo da wani shirin samar da ababen rufe fuskoki a kasar Sin da nufin taimakawa wajen rage yaduwar cutar numfashi ta coronavirus.

    Kamfanin na fatan samar da abun rufe fuskar kimanin miliyan biyu a rana a masana'antarsa ta Shenzhen daga nan zuwa karshen wata.

    Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadi game da matsalar karancin kayan aikin kariya daga cutar mai saurin yaduwa.

    A wani taro da WHO ta gudanar a Geneva, Shugaban hukumar Tedros Adhanom ya ce suna cigaba da nazari kan yadda za a samo mafita.

  4. 'Yan sanda sun kama sojan gona mai kwacen motoci

    Dubun wani sojan gona mai da mukarrabasa da ke kwacen motoci ta cika.

    'Yan sanda sun kwace mota akalla uku a hannun mutumin da ke sanye da kakin mai mukamin keftin da masu taimaka masa wadanda suka kware wurin kwacen mota.

    Kakakin 'yan sandan jihar Akwa Ibom Nudam Fredrick ya ce jami'an rundunar sun kuma yi nasarar kama wasu mutum uku da ake zargi da satar kananan yara a jihar.

  5. Masarautar Kano: Rikicin gwamna da Sarki ya kusa karewa

    Ricikin masarautar Kano tsakanin gwamna Abdullahi Ganduje da Sarki Muhammadu Sanusi II ta kusa karewa.

    Ganduje ya ce kwamitin dattawan Arewa na sulhu na ci gaba da tattaunawa da bangarorin domin sasanta tsakanin masu sabanin.

    Da yake amsa tambayoyin 'yan jarida a ziyarar da ya jagoranci wasu kusoshin jihar zuwa fadar shugaban kasa, Ganduje ya ce takun sakar da ke tsakaninsu lamari ne na tsarin mulki kuma kowane bangare na aikin gwargwadon matsayinsa.

    Tawagar jihar Kanon sun kai wa shugaban kasar ziyarar ne domin yi wa shugaban kasar godiya a kan ayyukan ci gaban da gwamnatinsa ta yi a jihar.

    Tawagar Kano a fadar shugaban kasa

    Asalin hoton, @BashirAhmad

  6. Masu amfani da Windows7 na cikin hadari, inji Pantami

    Isa Ali Pantami

    Asalin hoton, @FMICNigeria

    Masu amfani da kwamfutoci da ke amfani da manhajar Windows 7 domin huldar cinikayya ko musayar bayanai na cikin hadari.

    Ministan sadarwan Najeriya Isa Ali Pantami ya yi gargadin cewa Windows 7 zai daina daga ranar 14 ga watan Janairun da ya wuce na aka daina inganta manhajar ta yadda za ta kare bayanan da masu amfani da ita ke bayarwa.

    A sanarwar da ma'aikatar ta fitar, a ranar Juma'a, Pantami ya bukaci masu amfani da manhajar wurin huldar bankin da sauran harkoki da ke bukatar bayanan sirri su yi hattara.

    Ministan ya kuma bukaci masu amfani da Windows 7 su dauki matakan kare kansu domin kare bayanansu na sirri da kauce wa rasa muhimman bayanai.

    Shawarwarin da ma'aikatan bayar sun hada da sabunta manhajojin da suke amfani da su tare da yin hattara wajen sauke bayanai ko bude sakonni.

  7. Sabon albashi: Za a fara biyan ma'aikata a jihar Imo

    Gwamnatin jihar Imo da ke kudancin Najeriya ta bayar da umurnin biyan ma'aikatan jihar sabon albashi mafi karanci na naira 30,000.

    Kananan ma'aikatan jihar ne za a fara biya sabon albashin, kafin a daidaita a kan na manyan ma'aikata da sauran sauye-sauyen da suka danganci karin albashin.

    Mai magana da yawun gwamna Hope Uzodinma, Oguwuike Nwachukwu, ya ce gwamnan ya bayar da umurnin ne bayan tattaunawa da cimma yarjejeniya tsakaninsa da kungiyar kwadago a jihar, kamar yadda jaridar Dailiy Trust ta ruwaito.

    Hope Uzodinma

    Asalin hoton, @Govhopeuzodinma

  8. Buhari ya tafi taron kungiyar AU a Habasha

    Buhari

    Asalin hoton, @BashirAhmaad

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bar kasar domin zuwa taron kungiyar tarayyar Afirka AU.

    A yammacin Juma'a 7 ga watan Fabrairu ne shugaban ya bar Abuja domin halartar taron kungiyar karo na 33 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

    Buhari zai halarci taron ne tare shugabannin kasashe 55 da ke cikin kungiyar.

  9. Ana gwada matafiya shida saboda corona a Ethiopia

    Rahotanni daga Habasha na cewa an killace wasu mutum shida a Addis Ababa, babban birnin kasar saboda oronavirus.

    Ana kuma dakon sakamakon gwajin da aka yi wa mutanen.

    Mutanen - 'yan Ethiopia biyar da dan China daya sun je Wuhan, cibiyar annobar cutar ta Coronavirus da ta halaka mutum sama da 600.

    Gwajin jinin da aka yi na wasu mutum uku tuni aka aike zuwa Afirka ta kudu yayin da sauran gwajin za a aike su na ba da jimawa ba, a cewar shugaban cibiyar kula da lafiyar al'umma a kasar, Ebba Abate.

    Ya kara da cewa dukkan matafiya daga Wuhan ana killace su tare da yi musu gwaji.

    Jirgin Ethiopian Airlines na ci gaba da zirga-zirga zuwa China.

    An kuma wanke mutane takwas da a baya aka yi zargin sun kamu da cutar a kasar..

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

  10. An dakatar da dan tseren ninkaya saboda shan kayan kuzari

    An dakatar da tsohon zakaran gasar ninkaya wanda yataba lashe kyautar zinare a Olympic Roland Schoeman tsawon shekara daya bayan da gwajin da aka yi masa ya nuna cewa yana shan haramtattun kwayoyi.

    Dan kasar ta Afirka ta Kudu mai shekara 39 ya taba lashe lambar zinare a gasar ninkaya ta mita 4x100m a Athens a shekarar 2004.

    A watan Mayun 2019 ne aka gano yana shan kwayar GW501516, wacce ke kara kuzari.

    Schoeman

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Schoeman
  11. Tawagar Ganduje ta ziyarci Buhari don mika godiya

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin wata tawaga daga jihar Kano a fadarsa da ke Abuja, babban birnin kasar.

    Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan kafafen sada zumunta Bashir Ahmad ne ya bayyana haka a shafinsa na Twitter.

    Ya ce tawagar wadda ta hada da wakilai daga 'yan kasuwa da 'yan siyasa da kuma sarakunan gargajiya ta samu jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero.

    Da yake jawabi bayan taron, Ganduje ya ce sun kai wa Buhari ziyarar ta 'nuna godiya' saboda irin yadda yake marawa jihar Kano baya ta hanyar samar da abubuwan more rayuwa da tsaro.

    Buhari

    Asalin hoton, @BashirAhmaad

    Buhari

    Asalin hoton, @BashirAhmaad

    Buhari

    Asalin hoton, @BashirAhmaad

    Buhari

    Asalin hoton, @BashirAhmaad

  12. 'Dubban farar hula sun rasa matsugunansu a Syria'

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum 188,000 ne suka rasa matsugunansu sakamakon rikice-rikice a arewa maso yammacin Syria tun daga farkon watan Disamba.

    An kiyasta cewa rikicin zai sake tilasta wa kusan rabin adadin tserewa, yayin da sojojin gwamnatin Syria, wadanda ke samun goyon bayan Rasha, ke ci gaba da kwace yankunan da ke hannun 'yan tawaye.

    Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana wadanda aka tilasta wa barin gidajensu a matsayin mutane masu rauni a duniya.

    Majalisar ta ce tashe-tashen bama-bamai ya tilasta wa mutanen tserewa zuwa kananan yankuna.

    An kashe fararen hula kusan 50 a cikin kwanakin farko na wannan watan kadai.

    Sojojin Siriya suna fuskantar wasu kungiyoyin 'yan tawaye, wadanda ake danganta su da kungiyar masu da'awar jihadi ta al-Qaeda.

    Syria

    Asalin hoton, Getty Images

  13. Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin daurin shekara 12 kan Jolly Nyame

    Kotun Kolin Najeriya ta amince da hukuncin da kotun daukaka karar kasar ta yanke wa tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame na zaman shekara 12 a gidan yari.

    A watan Nuwambar 2018 ne ita ma kotun daukaka karar ta tabbatar da hukuncin da wata babbar kotun da ke Abuja ta yi wa tsohom gwamnan bisa samunsa da hannu a satar kudin jihar lokacin da yake kujerar gwamna.

    A hukuncin da suka yanke ranar Juma'a, alkalan kotun kolin biyar sun amince da wani bangare na bukatar Mr Nyame.

    Kotun kolin ta amince da bukatarsa game da samunsa da laifi da kuma yanke masa hukunci ko da yake ta ki amincewa da bangaren hukuncin wanda ya bukaci tsohon gwamnan ya biya miliyoyin naira.

    Jolly Nyame

    Asalin hoton, EFCC

  14. 'Yan China na jimamin rasuwar likitan da ya yi jan hankali kan corona

    Miliyoyin 'yan China na ci gaba da bayyana bacin ransu da fushinsu sakamakon mutuwar wani likita da ya yi gargadi game da barkewar sabuwar cuta ta numfashi.

    Li Wenliang ya mutu bayan kamuwa da cutar yayin da yake kula da wani mara lafiya a Wuhan, cibiyar barkewar annobar cutar.

    Abin da 'yan kasar suka kira na takaici shi ne yadda 'yan sanda suka ja kunnen likitan bayan ya gargadi abokan aikinsa likitoci suyi taka tsan-tsan sakamakon wata sabuwar cuta.

    Mahaifinsa ya shaida wa BBC cewa ya kamata a dauki mataki game da tsawatarwar hukuma.

    Akalla mutane dubu talatin da daya ne suka kamu da cutar - fiye da dari shida da talatin kuma sun mutu.

    China

    Asalin hoton, LI WENLIANG

  15. Masu fama da nakasa sun yi zanga-zanga a Lagos

    Masu fama da larurar nakasa sun gudanar da zanga-zanga a Lagos ranar Juma'a inda suka yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na haramta ayyukan 'yan acahab da keke napep.

    A farkon makon nan ne haramcin da gwamnatin ta yi wa masu sana'ar tuka babur mai kafa uku da kuma acaba ya soma aiki.

    Batun dai ya jawo wa gwamnatin jihar suka daga bangarori da dama, inda mazauna jihar ke cewa ba ta yi la'akari da mummunan halin da za su shiga ba.

    Sai dai gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne domin hana aukuwar hadura wadanda take zargin masu sana'ar achaba na haddasawa.

    Masu fama da nakasa
    Masu fama da nakasa
    Masu fama da nakasa
    Masu fama da nakasa
  16. Mawakin Ghana Sarkodie da mawakiyar Najeriya Alade sun dinke baraka

    Da alama fitaccen mawakin nan na Ghana Sarkodie da takwararsa ta Najeriya Yemi Alade sun dinke barakar da ke tsakaninsu bayan sun yi shekara biyu ba sa ga-maciji da juna.

    Ranar Alhamis, Sarkodie ya nemi Alade ta biyo shi a shafinsa na Twitter - kuma mawakiyar ta amsa gayyatarsa.

    Mawakan biyu sun yi fada ne a 2017 bayan Alade ta bukaci sanya Sarkodie a wani bangare na wakarta mai suna, Ego, amma bai amince ba.

    A wancan lokacin, Alade ta zargi Sarkodie da cewa bai san aikinsa ba kuma mawakan biyu sun janye jiki daga juna sai wannan lokaci.

    Sarkodie na daya daga cikin shahararrun mawakan Afirka

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Sarkodie na daya daga cikin shahararrun mawakan Afirka
    Alade ta ce Sarkodie bai san aikinsa ba

    Asalin hoton, Getty Images

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. Amnesty International na zanga-zanga kan dan jaridar Najeriya

    Kungiyar Amnesty International reshen Najeriya da wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam na gudanar da zanga-zanga a birnin Calabar na jihar Cross River don neman sakin wani dan jarida, Agba Jalingo.

    Kungiyar ta zargi gwamnatin jihar da kama dan jaridar a shekarar da ta wuce domin kawai yana gudanar da aikinsa.

    Ta yi kira ga hukumomi su yi biyayya sannan su daina danne masu fadin albarkacin bakinsu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. Coronavirus: Equatorial Guinea ta bai wa China tallafin $2m

    Shugaban Equatorial Guinea ya ce kasarsa mai arzikin man fetur za ta bai wa China tallafin $2m yayin da take fama da cutar corona - da ta kashe mutum 636.

    Amma duk da haka China tana alfaharin tattalin arzikinta shi ne na biyu mafi girma a duniya bayan na Amurka sannan ma'aunin tattalin arzikinta na $13.6tr ya danne na Equatorial Guinea wanda na ta ya kai $13.4bn.

    Matakain ya biyo bayan zaman da manyan jami'an gwamnatin suka gudanar ranar Talata sannan sun yi haka ne domin ''tallafawa da kuma nuna damuwa'' ga daya daga cikin abokanan kasar ta fannin kasuwanci.

    Duk da Equatorial Guinea ta kasance kasa ta uku mafi girma wajen samar da danyen mai, fiye da rabin al'ummarta na fama da talauci.

    Equatorial Guinea

    Asalin hoton, AFP

  19. Jam'iyyun da aka soke za su kai INEC kotu

    Wasu jam'iyyun siyasa da hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta soke rijistarsu sun ce za su maka hukumar a kotu domin matakin da ta dauka ya sabawa doka.

    Matakin na INEC -- wanda ya rage yawan jam'iyyun siyasar kasar daga 92 zuwa 18 -- bai zo wa da jam'iyyun ta dadi ba.

    Jam'iyyar People Trust wadda daya ce daga cikin jam'iyyun da aka soke rijistarsu ta ce INEC ta danne musu 'yanci.

    "Yanzu uwar jam'iyyarmu za ta tattauna kuma a karshe zamu daukaka maganar zuwa kotu," in ji Shugaban jam'iyyar ta People Trust Ibrahim Barde.

    INEC

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Minista ya yi murabus saboda wulakanta wata mace mai gadi

    Ministan shari'ar Rwanda Evode Uwizeyimana ya ajiye aikinsa bayan ya doki wata mai gadi inda ta fadi asa.

    Lamarin ya faru ne ranar Litinin, ko da yake ba a sani ba sai da wani mutum da ya shaida abin da ya faru ya wallafa hatsaniyar a shafinsa na Twitter.

    Mr Uwizeyimana ya nemi afuwa a Twitter, yana mai yin nadamar abin da ya faru.

    "Bai kamata a matsina na shugaba na yi wannan aika-aika ba. Ina neman gafara ga wannan mata da ke aiki a kamfanin samar da tsaro kuma ina neman afuwa ga jama'a."

    Daga bisani ministan ya ziyarci matar mai gadi a ofishin da take aiki.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X