Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassa na duniya 06/07/2026

Wannan shafin ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassa na duniya na ranar Litinin 6 ga watan Yulin, 2026

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Kutama

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Isra'ila ta ce ta kashe kwamandan mayaƙan Hamas a Gaza

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kashe Fadi Fallah Ashour Daghmash, wanda suka bayyana a matsayin kwamandan sashen horaswa na rundunar mayaƙan Hamas, a wani hari ta sama da suka kai a arewacin Gaza.

    A cikin wata sanarwa, sojojin Isra'ilar sun ce Daghmash ne ke jagorantar shirye-shiryen horas da mayaƙan Hamas, musamman rundunar ƙwararrunta.

    Sun kuma zarge shi da jagorantar hare-haren da aka kai kan sojojin Isra'ila a Gaza, tare da cewa a cikin watannin baya-bayan nan yana ƙoƙarin sake farfaɗo da ƙarfin mayaƙan Hamas.

    Sojojin Isra'ilar sun ƙara da cewa dakarunsu na ci gaba da kasancewa a yankin bisa yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma za su ci gaba da kai hare-hare kan duk wata barazanar tsaro da suka ce tana tunkararsu.

    Hamas dai ba ta fitar da wata sanarwa da ke tabbatar ko musanta ikirarin na Isra'ila ba.

  2. EFCC ta samu izinin ƙwace ƙarin kadarori daga tsohon ministan lantarki Saleh Mamman

    Saleh Mamman

    Asalin hoton, Efcc/X

    Babbar kotun tarayya a Najeriya ta bayar da umarnin ƙwace wasu ƙarin kadarori biyar mallakin tsohon Ministan Lantarki Saleh Mamman, wanda aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekara 75 kan laifukan cin hanci da rashawa.

    Mai shari'a James Omotosho ya bayar da umarnin ƙwace Walijam Apartments da ke Wuse 2 a Abuja a miƙa ga gwamnatin tarayya, inda kotun ta yanke cewa an sayi kadarar ne da kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya.

    Kotun ta kuma ba da umarnin ƙwace wasu kadarori huɗu na wucin gadi.

    Kadarorin sun haɗa da Bloom Luxury Suites Nigeria Limited da ke Kaduna, da wasu gidaje biyu a titin Misratah da ke Wuse 2 a Abuja, da kuma A.U.A Plaza da ke titin Kade a Wuse 2.

    Sai dai kotun ta umarci hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'annati (EFCC) ta wallafa sanarwar ƙwace waɗannan kadarori huɗu a wata jarida cikin kwanaki bakwai, domin bai wa duk wanda ke iƙirarin mallakarsu damar bayyana a gaban kotu ya nuna dalilin da ya sa ba za a ƙwace su gaba ɗaya ba.

    EFCC ta gurfanar da Saleh Mamman kan tuhume-tuhume 12 da suka shafi cin hanci da rashawa da halasta kuɗaɗen haram da yawansu ya kai naira biliyan 33.8.

    Kotun ta same shi da laifi a dukkan tuhume-tuhumen a ranar 7 ga Mayu, 2026, sannan ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 75 a ranar 13 ga Mayu.

  3. Trump ya tabbatar da cewa ya tsoma baki don a soke wa Balogun dakatarwa

    Trump da Infantino

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da cewa ya nemi Fifa ta sake duba hukuncin dakatarwar da aka yi wa ɗan wasan gaban Amurka Folarin Balogun na wasa ɗaya a gasar cin kofin duniya.

    Trump ya ce hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya "ta yanke shawarar da ta dace" wajen jingine hukuncin Balogun, inda ya ƙara da cewa da an aiwatar da hukuncin da hakan ya rage karsashin gasar ta bana.

    Balogun, wanda shi ne ɗan wasan tawagar Amurka da ya fi zura ƙwallaye a gasar da ake yi a yanzu, an shirya dakatar da shi ne a fafatawar da ƙasarsa za ta yi da Belgium a wasan zagaye na 16 a Seattle ranar Talata.

    Amma a daren Litinin, Fifa ta jingine hukuncin dakatarwar na wasa ɗaya na tsawon watanni 12, wanda hakan ya ba da damar a zaɓi ɗan wasan gaba mai shekaru 25.

    Da yake magana a Fadar White House ranar Litinin, Trump ya ce ya nemi Fifa ta sake duba hukuncin saboda "bai yi tunanin laifi ba ne".

    Trump ya tabbatar da cewa ya tattauna da shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino, amma ya ce abin da kawai ya yi shi ne neman a sake duba lamarin, tare da ƙarin bayanin cewa bai ce wa shugaban na Fifa ɗin ya jingine hukuncin dakatarwar da aka yi wa Balogun ba.

  4. Gawar marigayi Ali Khamenei ta isa birnin Qom

    gawar Khamenei ya isa birnin Qom

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafar yaɗa labarai ta ƙasar Iran ta fitar da wani bidiyo da ke nuna jirgin sama mai saukar ungulu ɗauke da gawar marigayi Ayatollah Ali Khamenei da wasu mutum huɗu daga cikin iyalansa ya isa birnin Qom.

    Tun da farko, shugaban kwamitin shirya jana'izar Khamenei, Hassan Hassanzadeh, ya ce bayan kammala jana'izar a Tehran da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, za a tafi da gawar zuwa Qom domin ta isa kafin lokacin sallar Magariba.

    Jirgin sama mai saukar ungulu ɗauke da gawar Khamenei ya isa birnin Qom

    Asalin hoton, IRIB News

    Bayanan hoto, Jirgin sama mai saukar ungulu ɗauke da gawar Khamenei ya isa birnin Qom

    Bisa ga jadawalin jana'izar da kafafen yaɗa labaran Iran suka wallafa a baya, ana sa ran za a ɗauki gawar Khamenei zuwa ƙasar Iraki gobe da rana, inda za a gudanar da wasu bukukuwan jana'iza a biranen Karbala da Najaf, kafin daga bisani a mayar da ita Iran domin binne ta a garinsu na haihuwa, Mashhad.

  5. Hotunan yadda dubban Iraniyawa suka yi wa Khamenei bankwana a birnin Tehran

    Jana'izar Khamenei a Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Ya ake rana ta uku ta jana'izar marigayi Ayatollah Ali Khamenei a birnin Tehran, inda dubban magoya bayansa suka taru domin yi masa bankwana.

    Jana'izar Khemenei a Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Jana'izar Khemenei a Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Ayatollah Ali Khamenei da wasu daga cikin iyalansa sun mutu ne a hare-haren Amurka da Isra'ila da aka kai ranar 28 ga Fabrairun 2026, lamarin da ya kawo ƙarshen shugabancinsa na tsawon shekara 36 a Iran.

    Jana'izar Khemenei a Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Jana'izar Khemenei a Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    An shirya jana'izarsa ta tsawon kwanaki shida a birane daban-daban na ƙasar, kafin a binne shi a ranar 9 ga Yuli a garinsu na haihuwa, Mashhad.

    Jana'izar Khemenei a Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Jana'izar Khemenei a Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Jana'izar Khemenei a Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Jana'izar marigayi Ayatollah Ali Khamenei da aka gudanar a birnin Tehran na Iran, inda dubban magoya bayansa suka taru domin yi masa bankwana.

    Tuni aka tafi da gawar marigayi jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, zuwa birnin Qom bayan an kammala jana'izarsa a Tehran.

  6. Ko Trump ya tsoma baki don a soke jan katin da aka ba Balogun?

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyo

    Janye dakatarwar da Fifa ta yi wa ɗan wasan Amurka, Folarin Balogun na ci gaba da ɗaukar hankalin magoya bayan ƙwallon ƙafa game da yadda ake ganin Donald Trump na yi katsalandan a harkokin wasanni.

    Ko hakan ne?

  7. Najeriya za ta binciki kamfanonin sada zumunta na Meta, X da AI

    Tinubu

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike kan manyan kamfanonin fasaha na duniya da suka haɗa da Meta, X (Twitter), Alphabet da kuma wasu kamfanonin fasahar AI da ke aiki a Najeriya.

    Hukumar kare haƙƙin masu amfani (FCCPC) ta ce binciken ya biyo bayan zarge-zargen karya dokokin amfani da ɗaukar bayanai daga kafafen yaɗa labarai ba tare da izini ba, da kuma wasu mu’amaloli da ake ganin na iya zama rashin adalci ga tsarin dijital a ƙasar.

    Matakin ya biyo bayan umarnin da shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar ga hukumar FCCPC, domin ta duba wani korafi da ƙungiyar masu yaɗa labarai ta Najeriya, NPO ta gabatar wa fadar shugaban ƙasa.

    Binciken zai mayar da hankali kan zargin cewa kamfanonin sun naɗi bahanai ko sun yi amfani da labarai da sauran bayanan kafafen yaɗa labarai na Najeriya wajen horar da fasahar AI ba tare da izinin hukumomi ba.

    Ƙungiyar NPO ta ce ta damu kan "yadda kamfanoni irin su Meta, Alphabet, X da wasu AI ke amfani da labarai ba tare da izini ko haƙƙin mallaka ba, wanda hakan ke rage samun kuɗaɗen shiga ga kafofin."

    Mataimakin shugaban FCCPC Mr. Tunji Bello, ya ce hukumar za ta gudanar da bincike na gaskiya bisa hujjoji, tare da tabbatar da cewa dukkan ɓangarori za su samu damar bayyana matsayarsu.

    Ministan yaɗa labarai da wayar da kai na ƙasar, Mohammed Idris, ya miƙa umarnin a wata takarda da yasanya wa hannu.

    FCCPC ta taɓa gudanar da bincike kan Meta a shekarar 2025, inda ta ci kamfanin tarar dala miliyan 220 bisa zargin karya dokokin kariyar bayanai, duk da cewa kamfanin ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

  8. Ƙarancin makaman kariya ya hana mu kakkaɓo makamai masu linzamin Rasha - Ukraine

    Volodymyr Zelensky

    Asalin hoton, Getty Images

    Dakarun Ukraine sun ce tsananin ƙarancin na'urorin kariya daga hare-haren sama ne ya sa suka kasa kakkabo ko guda daga cikin makamai masu linzami 23 da Rasha ta harba kan birnin Kyiv cikin dare.

    Hare-haren sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 17 a ciki da wajen babban birnin ƙasar, a cewar hukumomin Ukraine.

    Shugaban ƙasar, Volodymyr Zelensky, ya yi kira ga ƙawayen Ukraine na ƙungiyar tsaro ta NATO, waɗanda za su gudanar da taro gobe, da su ɗauki ƙarin matakai domin samar wa ƙasarsa da makaman kariya da za su taimaka wajen dakile hare-haren Rasha.

    Babban abin da ya fito fili a halin yanzu shi ne cewa Ukraine na fuskantar matsanancin ƙarancin na'urorin kariya daga hare-haren sama, lamarin da ke sa ta kasa dakile hare-haren makamai masu linzami yadda ya kamata.

    Ta ce wannan ne ya sa Shugaba Zelensky ke ci gaba da roƙon ƙawayensa su ƙara ba ƙasarsa kayan aikin kariya don kare fararen hula da muhimman cibiyoyi.

  9. An tafi da gawar Khamenei zuwa birnin Qom bayan kammala jana'iza a Tehran

    Jana'izar Khamenei

    Asalin hoton, Getty Images

    An tafi da gawar marigayi jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, zuwa birnin Qom bayan an kammala jana'izarsa a Tehran.

    Shugaban kwamitin shirya jana'izar Khamenei, Hassan Hassanzadeh, ya ce an kammala jana'izar da misalin ƙarfe 5:00 na yamma kamar yadda aka tsara tun farko.

    Ya ƙara da cewa an tafi da gawar zuwa birnin Qom kafin lokacin sallar Magariba da Isha'i domin ci gaba da shirye-shiryen binne shi.

  10. Jana'izar Khamenei: Ba za a yi taron bankwana ga jama'a a Mashhad ba

    ....

    Asalin hoton, Jamaran

    Wani jami’i daga kwamitin shirya jana’izar jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, a birnin Mashhad ya bayyana cewa ba za a gudanar da wani taron bankwana na jama'a a birnin ba.

    Sakataren kwamitin yaɗa labarai na kwamitin, Mehdi Shad, ya ce za a yi jana’izar da kuma sallar gawa ne a ranar Alhamis, 8 ga Yuli, kafin a binne marigayin daga baya a wannan rana.

    Ya ƙara da cewa za a gudanar da jerin gwanon jana’izar ne a manyan titunan da ke kaiwa harabar Masallacin Imam Reza da ke birnin Mashhad.

    A cewarsa, an tanadi wuraren masauki da za su iya ɗaukar sama da mutum miliyan biyu a kowane dare, ciki har da otal-otal, gidajen baƙi da sauran wuraren kwana domin sauƙaƙa wa masu halartar jana’izar.

  11. Jami'an Afirka ta Kudu na binciken kisan 'yan Najeriya biyu a ƙasar

    ....

    Asalin hoton, EPA

    Hukumar sa ido kan ayyukan 'yansanda ta Afirka ta Kudu IPID ta tabbatar da cewa tana binciken wani ƙorafi da aka shigar kan jami'an 'yan sanda a birnin Pretoria bayan mutuwar wasu ƴan Najeriya.

    Hukumar ta ce an shigar da ƙorafin ne a makon da ya gabata, amma ta ce har yanzu ba za ta iya bayyana cikakkun bayanai kan lamarin ba yayin da bincike ke gudana.

    Rahotanni sun nuna cewa ɗaya ya mutu ne yayin wata takaddama da ta shiga tsakaninsa da jami'an 'yansanda.

    A ranar 28 ga Yuni a lardin Mpumalanga kuma 'yansanda sun tabbatar da cewa suna binciken kisan ɗayan, wanda shi mai gidan gyaran gashi ne da aka harbe a wajen shagonsa da ke garin eMalahleni, tsohon Witbank.

    A cewar 'yansanda, wani mutum dauke da makami ne ya tare shi sannan ya harbe shi har lahira kafin ya tsere cikin wata farar mota.

    Har yanzu ba a kama kowa ba, kuma ba a san dalilin kashe ƴn Najeriya ɗin ba.

    'Yansandan suna kira ga duk wanda ke da bayanin da zai taimaka wajen cafke wanda ake zargi da ya tuntuɓe su.

  12. Za a kafa gwamnatin farar hula a Gaza bayan Hamas ta miƙa ragamar mulki

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Hamas ta sanar da rushe kwamitin da ke kula da harkokin gwamnatin Gaza, wanda ya jagoranci gudanar da mulkin yankin kusan tsawon shekara 20.

    A cewar sanarwar, shugaban kwamitin gaggawa na gwamnatin Hamas, Mohammed Fara, ya mika takardar murabus ɗinsa, yayin da aka amince da rusa kwamitin gaba ɗaya domin sauƙaƙa miƙa alhakin tafiyar da harkokin yau da kullum ga Kwamitin Kula da Gudanar da Gaza.

    Hamas ta karɓi ikon Gaza ne a shekarar 2007 bayan rikici da ƙungiyar Fatah, shekara guda bayan nasarar da ta samu a zaɓen majalisar dokokin Falasɗinawa na 2006.

    Tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila a watan Oktoban bara, Hamas ta bayyana a lokuta da dama cewa tana shirin janyewa daga tafiyar da harkokin yau da kullum na Gaza. sai dai har yanzu ba a warware batun kwance ɗamarar mayaƙanta.

    Mai magana da yawun Hamas ya ce matakin rushe kwamitin wani yunkuri ne na kawar da duk wata hujja da Isra’ila ke amfani da ita wajen ci gaba da kai hare-hare a Gaza.

    Ana kallon wannan mataki a matsayin wani yunkuri na buɗe ƙofa ga kafa gwamnatin farar hula da za ta tafiyar da harkokin yankin a nan gaba.

  13. Matatar Dangote ta fitar da man biliyan 757 zuwa Turai

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Matatar man Dangote ta fitar da man jirgin sama da darajarsa ta kai kusan Naira biliyan 757 zuwa Turai a watan Yuni.

    Jimillar man da aka fitar ta kai tan 466,000, wanda ya yi daidai da kusan lita miliyan 582.5.

    Rahotanni sun nuna cewa wannan shi ne mafi yawan man da Najeriya ta taɓa fitarwa zuwa Turai tun lokacin da matatar Dangote ta fara samar da irin wannan mai a shekarar 2024.

    Haka kuma, Najeriya ta zarce Amurka wajen samar wa Turai man jirgin sama a watan Yunin inda ta fitar da tan 466,000, yayin da Amurka ta fitar da tan 399,000 kacal.

    Masana sun ce wannan nasara na nuna yadda matatar Dangote ke ƙara bunƙasa fitar da kayayyakin mai daga Najeriya tare da ƙarfafa matsayin ƙasar a kasuwannin makamashi na duniya.

  14. MDD ta ba da umarnin gaggauta bincike kan rikicin El-Obeid

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kare haƙƙin ɗanadam ta Majalisar Dinkin Duniya ta ba da umarnin gudanar da binciken gaggawa kan zarge-zargen cin zarafin bil’adama a El-Obeid na Sudan, yayin da ta yi allawadai da ƙaruwar hare-haren RSF a yankin.

    Babban Kwamishinan MDD mai kula da haƙƙin ɗanadam, Volker Türk, ya yi gargaɗin cewa yankin na fuskantar wani sabon bala’in jin-ƙai, inda fararen hula suka shafe watanni 18 cikin mawuyacin hali sakamakon rikicin da ke tsakanin sojojin Sudan da RSF.

    Rahotanni sun nuna cewa mayaƙan RSF na ƙara taruwa a kewayen El-Obeid, lamarin da ya ƙara tsoron yiwuwar sabon hari, yayin da hukumomin jin ƙai ke gargadin ƙarancin man fetur, magunguna da ruwa mai tsafta a birnin.

  15. Tanzaniya ta tura sojoji da ƴansanda gabanin zanga-zangar ƙasa da aka shirya yi

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Tanzaniya ta tura sojoji da ‘yansanda zuwa manyan biranen ƙasar gabanin wata zanga-zangar da aka shirya gudanarwa ranar Talata domin neman sauye-sauyen dimokuraɗiyya da kuma adalci kan zaɓen 2025 da ake takaddama a kansa.

    Mahukunta sun dakatar da duk wasu tarukan siyasa tun ranar 26 ga Yuni, suna masu cewa matakin na da nufin kare tsaro, yayin da ‘yan adawa ke ganin hakan tauye ‘yancin jama’a ne.

    Jami’an tsaro sun ce suna da bayanan sirri da ke nuna cewa wasu na shirin amfani da zanga-zangar wajen tayar da hankali da aikata ta’adi.

    Rundunar sojin ƙasar ma ta yi gargaɗin cewa ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya ba.

    Tashin hankalin na da alaƙa da rikicin siyasa da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2025, wanda ya jawo zanga-zanga da asarar rayuka fiye da 500, a cewar wani kwamitin bincike na gwamnati.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da ‘yan adawa suna zargin gwamnati da ƙuntata fagen siyasa, yayin da gwamnati ke cewa matakan tsaron da take ɗauka na wucin gadi ne kuma domin kare lafiyar ƙasa da al’ummarta.

  16. Pezeshkian, Qalibaf da babban ɗan Ali Khamenei za su halarci jana’izarsa a Iraq

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin dillancin labaran Mehr ya ruwaito cewa za a kai gawar marigayi Ali Khamenei zuwa birnin Najaf gobe, Talata bayan an gudanar da jana’izarsa a birnin Qom.

    Rahoton ya ce Mustafa Khamenei, wanda shi ne babban ɗansa tare da shugaban ƙasar Iran Masoud Pezeshkian da kuma kakakin majalisar dokokin ƙasar Mohammad Baqer Qalibaf, za su tafi Najaf a gobe domin halartar jana’izar da za a gudanar a Iraq.

    An shirya gudanar da jana’izar Ali Khamenei a ranar Laraba a biranen Karbala da Najaf na ƙasar Iraq.

    Bayan haka, za a binne Khamenei ta Iran a ranar Alhamis a harabar hubbaren Imam Reza da ke birnin Mashhad.

  17. Cutar Ebola ta kashe mutum fiye da 500 a Gabashin DR Congo

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Mahukuntan lafiya a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DR Congo) sun sanar da cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon ɓullar cutar Ebola nau'in Bundibugyo ya kai 506.

    Tun bayan ayyana ɓarkewar cutar a ranar 15 ga Mayun 2026, an tabbatar da kamuwar mutum 1,561, yayin da mutum 628 ke killace ko kwance a asibiti a larduna uku na gabashin ƙasar.

    Lardin Ituri ne har yanzu ke kan gaba wajen yawan waɗanda suka kamu da cutar, inda yake da fiye da kashi 90 cikin 100 na dukkanin waɗanda aka tabbatar sun kamu.

    Haka kuma jami'an lafiya sun nuna damuwa kan yawaitar zirga-zirgar jama'a a yankunan da ke cikin haɗari, musamman sakamakon rikice-rikice da ayyukan haƙar ma'adinai.

    Barkewar cutar ta kuma shafi ma'aikatan lafiya, inda mutum 96 daga cikinsu suka kamu da cutar, yayin da 19 suka mutu. Duk da ƙarancin kayan kariya da matsalolin da ake fuskanta, jami'an lafiya sun ce ana samun ci gaba wajen bibiyar mutanen da suka yi hulɗa da masu ɗauke da cutar, kuma adadin waɗanda suka warke ya kai 254.

  18. Hatsarin mota a Ogun ya yi sanadin mutuwar mutum 10

    Aƙalla mutum 10 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu shida suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a gadar Saapade da ke kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a jihar Ogun.

    Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar kiyaye hadurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Ogun, Afolabi Odunsin, ya bayyana cewa hatsarin ya rutsa da wata babbar mota da kuma wata motar bas.

    Ya ce mutum 18 ne ke cikin motocin biyu a lokacin da hatsarin ya faru.

    A cewarsa, mutum 10 sun mutu nan take, ciki har da maza tara da yaro ɗaya, yayin da mutum shida suka samu raunuka daban-daban.

    Binciken farko ya nuna cewa saurin da ya wuce kima da kuma tuƙin ganganci ne suka haddasa hatsarin.

    Ma'aikatan ceto na FRSC sun garzaya wurin da hatsarin ya faru inda suka kai waɗanda suka ji rauni Asibitin Victory da ke Ogere domin samun kulawa, yayin da aka kai gawarwakin mamatan ɗakin ajiye gawa na FOS da ke Ipara.

    Kwamandan FRSC na jihar Ogun, Oludare Ogunjobi, ya jajanta wa iyalan mamatan tare da gargadin direbobi musamman na motocin haya da manyan motoci da su guji yin tuƙin ganganci da gudun da wuce kima da sauran laifukan tuki da ke jefa rayuka cikin haɗari.

  19. Tsohon shugaban Iran Ahmadinejad ya halarci jana'izar Ali Khamenei a Tehran

    ....

    Asalin hoton, MORE

    Kafafen yaɗa labaran Iran sun wallafa hotunan da ke nuna tsohon shugaban ƙasar, Mahmoud Ahmadinejad, yana cikin mahalarta jana'izar tsohon jagoran Iran, Ali Khamenei, da ake gudanarwa a birnin Tehran.

    Bayyanar Ahmadinejad a wajen jana'izar ta janyo hankali, kasancewar ba a gan shi a bainar jama'a ba tun bayan fara yaƙin Iran.

    A lokacin yaƙin, rahotanni sun ce yankin da gidansa yake ya fuskanci hare-hare.

    Ahmadinejad ya shugabanci Iran daga shekarar 2005 zuwa 2013, kuma ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2009 mai cike da cece-kuce.

    Bayan zaɓen ne aka tsare manyan jagororin adawa, ciki har da Mir Hossein Mousavi, Zahra Rahnavard da Mehdi Karroubi, lamarin da ya haifar da zanga-zangar Green Movement a fadin ƙasar.

  20. Yadda ake zagayawa da gawar Khamenei a tsakiyar miliyoyin mutane a Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hotunan da kafafen yaɗa labarai suka wallafa sun nuna ɗimbin jama'a da suka mamaye tituna da manyan filayen taro a birnin Tehran domin yi wa tsohon jagoran Iran, Ali Khamenei, bankwana na ƙarshe.

    Maza da mata sanye da baƙaƙen kaya sun hallara tun daga safiyar ranar jana'izar, inda wasu ke ɗauke da hotunansa da tutocin Iran.

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    A wasu daga cikin hotunan, ana iya ganin yadda gawar Khamenei ke tafiya a cikin wata mota ta musamman yayin da dubban masu makoki ke rakiyar ta a kan titunan birnin.

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Mahalarta taron sun nuna alhini da jimami, inda wasu ke yin addu'o'i tare da bayyana girmamawarsu ga mutumin da ya shafe shekaru yana jagorantar ƙasar.

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Jana'izar ta zama ɗaya daga cikin manyan tarukan da aka gani a Iran cikin 'yan shekarun nan, lamarin da ya sa hukumomi suka ɗauki matakan tsaro da na zirga-zirga na musamman.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana sa ran bukukuwan za su ci gaba kafin daga bisani a kai gawar marigayin zuwa birnin Mashhad, inda za a yi masa jana'iza ta ƙarshe da kuma binne shi.

    ....

    Asalin hoton, Getty Images