Abin da ya kamata ku sani kan jana'aizar Ayatollah Ali Khamenei

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin Iran sun fara shirye-shiryen gudanar da jana'izar tsohon jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Khamenei da aka kashe watanni da suka gabata.
Za a ɗauki aƙalla kwanaki shida ana gudanar da tarukan jana'izar a fadin biranen ƙasar waɗanda aka ɗauki tsauraran matakan tsaro a cikinsu.
An kashe Ayatollah Khamenei a wani harin haɗin gwiwar Isra'ila da Amurka a kan gidansa ranar 28 ga watan Fabrairun 2027.
Hukumomin Iran sun jinkirta jana'izar ne tsawon wata huɗu sakamakon yaƙin da aka ci gaba da gwabzawa tsakanin Iran da Amurka da kuma Isra'ila.
To sai dai yanzu bayan cimma yarjejniyar kawo ƙarshen yaƙin, wadda har yanzu ke tangal-tangal - hukumomin na Iran suka shirya gudanar da jana'izar mai cike da tarihi.
Za a fara hidimar janazar ne a ranar 4 ga wata a birnin Tehran, yayin da za a kammala ranar 9 ga wata a birnin Mashhad.
A waɗanne birane za a yi jana'izar?

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin Iran sun shirya gudanar da tarukan jana'izar da za a fara ranar Asabar a birane biyar na ƙasashen Iran da Iraqi.
Biranen da za a yi jana'zar sun haɗa da:
- Tehran
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Za a fara jana'izar ne a babban birnin ƙasar, wato cibiyar gwamnatin ƙasar.
Bayanai sun ce za a fara jana'izar ne a birnin Tehran in a babban masallancin Juma'a na birnin domin yin bankwana da gawar Ayatollah.
- Qom
Bayan kammala bankwana da gawar a birnin Tehran za kuma wuce birnin Qom, wato cibiyar mazhabin shi'a ta duniya, inda za a gudanar da jana'izar a hukumance.
A birnin Qom ne ake da babbar maƙabaratar ƴan Shi'a a duniya.
Daga cikin wuraren da za a yi jana'izar har da Masallacin Jamkaran da ke wajen birnin, wanda ke zama ɗaya daga cikin wurare mafiya muhimmanci ga mabiya shi'a.
- Mashhad
Daga nan kuma sai a kammala a birnin Mashhad, inda a nan ne kuma za a binne gawarsa.
Birnin Mashhad ya kasance mahaifar Ayatollah Khamenei, wato inda aka haife shi.
- Najaf da Karbala a Iraqi:
Biranen Najaf da Karbala na daga cikin biranen da za a gudanar da bukukuwan jana'izar Ayotallah a ƙasar Iraqi.
Abubuwan da za a yi a waɗannan birane - masu tsarki ga mabiya Shi'a - sun ƙunshi tarukan jimami da tattaki.
Ana kuma sa ran kai gawar zuwa waɗannan birane na Iraƙi domin mabiya Shi'a su yi bankwana da ita.
Gwamnati ta ziyarci biranen
Gwamnatin Iran ta kammala shirye-shiryen jana'izar, bayan da tawagar wakilanta ta ziyarci duka wuraren domin ganin irin shirye-shiryen da aka yi.
Kwamitin jana'izar ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar, Mohammad Reza Aref ta shafe tsawon makonni ta na lura da shirye-shiryen jana'izar.
Shi ma Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi - da ke cikin kwamitin - ya ziyarci biranen da za a yi jana'izar a Iraqi, inda ya gana da gwamnonin yankunan, domin jin shirin da aka yi.
Hukumomi sun ce mutum miliyan takwas ne ake tunanin za su halarci bukukuwan jana'izar a biranen biyar.
Ana sa ran mutane daga lardunan ƙasar 31 za su halarci jana'izar tsohon jagoran.
Matakan da aka ɗauka

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar tsaro ta Basij ce ke jagorantar tsara shirin jana'izar. Rundunar ta kuma ce za a gudanar da wasu sauye-sauye a biranen da za a gudanar da jana'izar.
Rundunar ta ce mayar da manyan titunan ƙasar wuraren ajiye motoci, yayin da masallatai da makarantu da filayen wasanni da jami'o'i za su kasance wuraren kwana tsawon lokacin wannan jana'izar.
Ana sa ran soke tashin jirage, kuma ana sa ran lura da shige da ficen birnin.
Rundunar juyin juya halin ƙasar, IRGC ce ke da ikon samar da tsaro a manyan biranen yayin jana'izar.
Su wane ne manyan jagororin da za su je jana'izar?
Kawo yanzu dai babu tabbas game da ko sabon jagoran addinin ƙasar, Mojtaba Khamenei - wanda ba a gani a bainar jama'a ba tun bayan naɗa shi - zai halarci jana'izar.
Kafofin yaɗa labaran Amurka , sun ambato wasu jami'an Iran na cewa Mojtaba Khamenei ya samu munanan raunuka a harin da ya kashe mahaifinsa, lamarin da ya sa aka yi masa jerin tiyata.
Hukumomin Iran dai ba su tabbatar da hakan ba a hukumance.
Shugaban ƙasar Pakistan, Asif Ali Zardari da firaministan ƙasar, Shehbaz Sharif sun tabbatar da cewa wakilan ƙasar za su halarci jana'izar.
Tuni wakilai daga gwamnatin Taliban suka fara hallara a Tehran domin wannan jana'iza.
Haka ma babu tabbas ko wasu shugabannin ƙasashen yankin Gulf ko na Rasha da China , waɗanda suke manyan kawayen Iran za su halarci tarukan janazar.











