Yadda jana'izar Rahollah Khomeini ta shiga Kundin Tarihi na Guinness

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, محمد همدر
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, بیبیسی عربی
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
A ranar Asabar ne za a fara hidimar jana'izar tsohon jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya jagoranci ƙasar na tsawon shekara 36.
An kashe shi a wasu hare-haren Amurka da Isra'ila a ƙarshen watan Fabrairun 2026.
Wannan na zuwa ne shekara 37 bayan jana'izar jagoran addinin ƙasar na farko, Ruhollah Khomeini da aka gudanar a birnin Tehran.
Bayan rasuwarsa ne majalisar ƙwararrun ƙasar suka zaɓi Ali Khamenei a matsayin sabon jagodan addinin ƙasar.
Jana'izar Ruhollah na ɗaya daga cikin manyan tarukan jana'izar da aka samu yamutsi a tarihi.
A cewar jami'an Iran, fiye da mutum miliyan 10 ne suka halarci taron jana'izar, lamarin da ya sa Kundin Adana Tarihi na Guinness ya ayyana taron jana'izar a matsayin wadda ba a taɓa ganin irinta ba a tarihin duniya, idan aka kwakwanta yawan waɗanda suka halarta da yawan al'ummar ƙasar.
Duk da cewa an samu labarin tsananta jikinsa gabain rasuwar tasa, labarin mutuwar tasa ta girgiza ƴan ƙasar da magoya bayansa da dama.
Ya rasu shekara 10 bayan juyin-juya halin ƙasar da ya kifar da gwamnatin tsohon sarkin ƙasar da ake kira Sha, tare da kafa sabon tsaron gwamnatin Jamhuriyar Musulunci, kuma ƙasa da shekara ɗaya bayan kammala yaƙin Iran da Iraqi.
Taron jana'izar ya rikiɗe zuwa tashin hankali, inda ya fi ƙarfin hukumomi.
Wasu daga cikin dandazon miliyoyin mutunen da suka halarci taron, sunzuwa kusa da gawar Jagoran Addinin.
Sakamakon haka ne, jami'an tsaro suka gaza shawo kan mutane, lamarin da ya sa aka dakatar da jana'izar a karon farko, yayin da daga baya aka sake shirya ta shin tsauraran matakan tsaro.
Me ya faru a wajen "bankwana'' da binne gawar?

Asalin hoton, Getty Images
A cikin wani rahoto na musamman mai suna "Ruhollah", da aka naɗa kan rayuwar Ayatollah Khomeini, ya nuna hotunansa a kwanakin ƙarshe na rayuwarsa a asibiti a kashi na ƙarshe na shirin.
A cikin rotunan, an ga Khomeini na kwance a kan gadon asibiti, likitoci da ƴan'uwansa na kewaye da shi.
An ga yadda jikinsa ya yi la'asar, yana motsi cikin tsananin wahalar jinya da kuma ba ya iya magana.
Rahoton an musamman ya kuma nuna wasu lokutan da Ruhollah Khomeini ke addu'a tare da taimakon wasu mutane, a wasu wuraren kuma an ga wasu mutanen da ke kusa da shi na ƙoƙarin ciyar da shi.
Sannan an ga hotunan likitoci da makusantansa na ƙoƙarin tallafo sh.
An ƙarƙare rahoton da nuna hotunan wasu ƴan'uwansa na kuka da jimami bayan samun labarin rasuwarsa.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ruhollah Khomeini ya rasu ne da maraicen 3 ga watan Yunin 1989, yayin da gidajen radiyo da talbijin na ƙasar suka sanar da labarin washe gari da safe.
A lokacin hukumomin ƙasar sun ayyana makokin kwana 40, kuma magoya bayansa sun nuna jimami a kan tatinan ƙasar.
A lokacin da labarin rasuwarsa ya yaɗu, dandazon mutane daga sassan ƙasar daban-daban sun ɗunguma zuwa birnin Tehran domin halartar jana'izar.
A ranar 5 ga watan Yuni ne aka kai gawarsa zuwa babban masallacin Juma'a ana birnin Tehran, domin bankwana da ita.
Bayan shirya gawar cikin likkafani, an sanyata cikin gilashi mai haske ta yadda mutane za su iya hangota, aka kuma ɗora ta kan wani abu mai tudu ta yadda duk wanda ya shiga masallacin zai hango ta.
Hotunan da aka ɗauka ta kyamarorin da ke yawo a sama sun nuna yadda dandazon mutane suka yi wa masallacin dafifi.
Wasu na kuka wasu na bugun ƙirgi wasu na jimami, duk a cikin alhinin mutuwar tsohon jagoran addinin.
An samu labarin cewa mutane da dama ne suka suma sakamakon zafi da cunkoson jama'a a wurin taron.
Gawar ta kwana a masallacin har zuwa washe gari, inda aka ɗauke ta zuwa maƙabartar Behesht Zahra da ke kudancin birnin Tehran, domin binne ta.
A nan ne kuma dandazon mutane suka sake taruwa, lamarin da ya ci ƙarfin jami'an tsaron da ke bayar da kariya a wurin.

Asalin hoton, Getty Images
An tsara tafiya daga tsakiyar Tehran zuwa Behesht Zahra, kusan kilomita 30 tsakani.
Hotunan da aka ɗauka sun nuna yadda mutane suka yi dafifi a kan titin Tehran zuwa Behesht Zahra.
Motar da ta ɗauki gawarsa ta riƙa tafiya a hankali saboda cunkoson jama'a a kan titin.
Waɗanda suka shirya jana'izar sun gaza aiwatar da tsarin jana'izar kamar yadad sukamshirya tun da farko saboda yawan jama'a.
Jami'an tsaro da dakarun juyin juya halin ƙasar, sun shiga domin buɗe hanya, don samar wa motar da ke ɗauke da gawar hanya.
Yayin da ake haka a kan hanya, can kuwa a garin na Behesht Zahra tuni ya cika maƙil da jama'a, wani abu da ya haifar da wahala wajen shigar da gawar zuwa maƙabartar.
Daga ƙarshe bayan da aka fahimci babu wurin da gawar za ta shiga garin ta ƙasa, hukumomi sun sake shiri, inda suka yanke shawarar ɗaukar gawar a jirgi mai saukar ungulu zuwa cikkin maƙabartar kai-tsaye.
To amma duk da haka, can ma a maƙabartar mutane sun cika ta maƙil.
Yayin da jirgin ya sauka a maƙabartar, dubban mutane sun ruga da guda domin samun damar taɓa gawar da nufin samun tabarraki.

Asalin hoton, Getty Images
Hotunan da aka ɗauka sun nuna yadda mutane suka tunkari jirgin da nufin taɓa gawar idan an fito da ita, lamarin da ya haifar da turmutsitsi a maƙabartar.
Jami'an tsaro da dakarun juyin juya hali sun samu nasarar ƙwace iko da gawar, tare da maida ta jirgin, inda ya sake tashi sama.
Akbar Hashemi Rafsanjani, wanda shi ne kakakin majalisar dokokin ƙasar na lokacin, ya halarci wurin a cikin jirgi mai saukar ungulu, inda ya sanya idanu a lokacin da ake maido da doka da oda a maƙabartar.
Ahmad Khomeini, ɗa ga Ruhollah Khomeini, shi ma ya halarci jana'izar.
A daidai lokacin ne kuma gidan radion ƙasar, ya sanar da ɗage jana'izar domin bai wa dandazon mutane damar ficewa daga makabartar.
Bayan wani lokaci, jirgin da ke ɗauke da gawar ya samu damar sauka a inda ya dace, inda kuma aka samu nasarar yin jana'izar.
'Mutum 10,200,000 suka halarci jana'izar'
A cewar wasu alƙaluma daga Kundin Adana Tarihi na Guinness dandazo da matsin da aka samu a wajen jana'izar ya haifar da mutuwar mutum takwas da raunata 500.
Majiyar Kundin ta ƙara da cewa adadin mutanen da suka halarci jana'izar ya kai mutum miliyan 10,200,000.
Ayatollah Khomeini, ya kasance ɗaya daga cikin mafiya tasiri a tsarin shugabanci da siyasar da kuam Addini a tarihin Iran.
Shi ne ya jagoranci juyin juya halin da ya kifar da gwamnatin Pahlavi.
Ali Khamenei ya gaje shi a 1989, inda ya zama jagoran addainin ƙasar na biyu, kuma mafi jimawa a mulki, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara muradun ƙasar da alaƙarta da ƙasashen waje.
Magoya bayan shagabannin biyu, na kallonsu a matsayin wata alama ta ƴancin kai da turjiya daga ƙasashen Yamma, yayin da masu suka ke zarginsu da tattare duka ikon ƙasar a hannayensu.
Jana'izar Khamenei
A yanzu haka jami'an Iran na shirya jana'izar Ayatollah Ali Khamenei
Hukumomin Iran sun ce suna sa ran samun miliyoyin mutanen da za su halarci jana'izar Ayatollah Ali Khamenei, wadda aka tsari yi cikin tsaurara matakan tsaro.
Haka kuma, yadda Mista Khamenei ya rasa ransa ya sa jana'izar za ta ɗauki wata alama ta musamman.
A bayanan da suke yi, jami'an gwamnatin Iran da magiya bayansa na bayyana shi a matsayin ''Shahidi'', wata kalma mai ɗauke da tarin daraja a Addinin Musulunci.











