Yadda ziyarar BBC ta kasance a Mashigar Hormuz - jirage sun yi cirko-cirko

Asalin hoton, Jack Garland / BBC
- Marubuci, Nawal Al-Maghafi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior international investigations correspondent, BBC World Service
- Aiko rahoto daga, Bandar Abbas, Iran
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 8
A tashar jiragen ruwa ta Bandar Abbas da ke kudancin Iran, ana ci gaba da harkokin kamun kifi duk da cewa ana rikici kan shafi Mashigar Hormuz, ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin zirga-zirgar jiragen ruwa a duniya.
Ana fuskantar rana mai tsananin zafi, yayin da su kuma masunta ke sauke kifayen da suka kamo.
Wani daga cikinsu na riƙe da ƙananan kifayen shark da ragarsa ta kama. Akwai kuma wani da ya ɗora manyan kifaye biyu a kan babur dinsa ya tafi.
Wannan ne karo na farko da ƴan jarida na ƙasashen waje suka samu damar ziyartar ɓangaren Iran na Mashigar Hormuz tun bayan fara rikicin.
Lokacin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da hare-hare a ranar 28 ga Fabrairu, Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan Isra'ila da kuma wasu ƙasashen yankin Tekun Fasha da rundunonin sojin Amurka ke da sasani.
Haka kuma ta yi amfani da damarta ta ƙasa mai iko da Mashigar Hormuz a matsayin wata muhimmiyar hanyar matsa lamba.
Daga nan ne dakarun IRGC na Iran, suka fara harbin jiragen dakon kaya da ke ƙoƙarin ratsa mashigar ba tare da izininta ba, lamarin da ya sa zirga-zirgar jiragen ruwa ta tsaya cak.
Hakan ya sa jiragen ruwa daga sassa daban-daban na duniya suka maƙale, yayin da farashin danyen mai ya yi tashin gwauron zabi. Hakan kuma ya ƙara farashin makamashi, man fetur da kuma kayayyaki da dama da ake safararsu ta ruwa zuwa ƙasashe daban-daban.
A sakamakon haka ne Amurka ta ƙaƙaba nata shingen ruwa ta hanyar hana duk wani jirgin ruwa da ya fito daga Mashigar Hormuz da amincewar Iran.
A dalilin wannan rikici, ruwan ya zama mai matuƙar haɗari ga masu kamun kifi. Masunta da dama sun daina fita kamun kifi gaba ɗaya, yayin da wasu suka ci gaba da fita duk da sanin cewa suna shiga yankin da ake gwabza yaƙi.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A yanzu dai an shafe makonni bayan da Iran ta amince a sake buɗe Mashigar Hormuz a wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka, wadda har yanzu ake ci gaba da tattaunawa, lamura sun fara daidata a kan ruwan, kuma masunta sun koma gudanar da sana'arsu.
Ɗaya daga cikin masuntan, Abdol Rahman, ya raka tawagar BBC zuwa mashigar domin nuna yadda rikicin ya shafi rayuwa a Bandar Abbas da yankunan da ke kewaye da ita.
Yayin da suke tafiya a cikin mashigar, an hango wasu manyan jiragen dakon kaya guda biyu da dakarun IRGC suka ƙwace a watan Afrilu, lokacin da rikicin ya yi ƙamari.
A lokacin, dakarun IRGC sun ce jiragen sun yi barazana ga tsaron teku ne saboda sun yi ƙoƙarin wucewa ba tare da amincewarta ba, tare da yin katsalandan ga na'urorin kewayawarsu.
Duk da tsagaita wutar, har yanzu ba a saki jiragen MSC Francesca mai tutar Panama da Epaminondas mai tutar Laberiya ba.
Haka kuma, BBC ta ga wasu jiragen dakon kaya da dama suna tsaye a bakin teku suna jiran izinin hukumomin Iran kafin su ratsa Mashigar Hormuz.
Lokacin da tawagar ta isa kusa da Hormuz, mai nisan kilomita takwas daga gabar Bandar Abbas, jagoransu Rahman ya nuna musu wani tsohon sansanin soja da ke kallon tekun.
An daɗe ana gwabza yaƙi kan mallakar Mashigar Hormuz. An kafa sansanin a farkon ƙarni na 16 ne, kuma har zuwa shekarar 1622 lokacin da Shah Abbas na Farisa ya fatattaki Portugal daga yankin. Shi ne aka sanya wa birnin Bandar Abbas suna.
A yanzu dai Bandar Abbas ne birni mai matuƙar muhimmanci ta fuskar tsaro. Birnin na kudancin Iran ne, kusa da Mashigar Hormuz, kuma a nan ne hedikwatar rundunar sojin ruwan Iran da kuma rundunar sojin ruwa ta IRGC take.
Kusan kashi ɗaya cikin biyar na ɗanyen mai da iskar gas da ake jigila a duniya na ratsawa ne ta wannan mashiga, abin da ya sa Bandar Abbas ke da muhimmanci ga tattalin arzikin duniya.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sha yin barazana ga Iran, inda ya gargaɗin cewa "ba za ta ci gaba da kasancewa ƙasa ba" idan ba ta sake buɗe Mashigar Hormuz ba.
Sai dai duk da waɗannan barazanar da kuma yarjejeniyar tsagaita wuta, Iran ba ta sake buɗe mashigar gaba ɗaya ba.

Lokacin da tawagar BBC ta isa birnin Bandar Abbas, alamu sun nuna cewa rayuwa na ci gaba da komawa yadda take a da.
Mutanen da suka tsere sun koma gidajensu, shaguna sun sake buɗewa, sannan tituna sun cika da ababen hawa kamar yadda aka saba.
Kasuwar birnin ita ma ta sake cika da masu saye da sayarwa. Sai dai har yanzu ana iya ganin illar yaƙin.
A titin Khushnoodi, bayan babbar jami'ar Bandar Abbas, wasu gine-gine ne da suka lalace sosai bayan harin da Isra'ila ta kai masa a ranar 26 ga Maris.
Rabin ginin ba rushe ba, yayin da ɗayan rabin ya rushe. Ana kuma iya hango ɗakuna da mutane, yayin da tutocin Iran ke lilo a jikin ginin.
Akwai wasu ofisoshi a ginin. Fatima, wata ƴar kasuwa mai shekara 40 da ke aiki a wurin, ba ta cikin ginin lokacin da aka kai harin.
"Na san mutane da yawa da ke zaune a ginin," in ji ta.
"Akwai iyaye mata da yara. Suna barci lokacin da akai kai harin. Wasu sun tsira, amma mutum uku sun mutu. Ɗaya daga cikinsu jami'in soja ne da ke zaune a ginin tare da iyalansa."

Asalin hoton, Jack Garland / BBC
Rundunar sojin Isra'ila ta ce kwamandan rundunar ruwa ta dakarun IRGC, Alireza Tangsiri ta kai wa harin. Kwana huɗu bayan harin, Iran ta tabbatar da mutuwarsa.
Kamfanin dillancin labarai na Fars ya ruwaito cewa mutum uku sun mutu, yayin da bakwai suka jikkata bayan makamai masu linzami biyu sun faɗa kan ginin.
Ƙungiyar agajin gaggawa ta Red Crescent ta ce mutum 261 da suka haɗa da fararen hula da jami'an soja ne suka mutu a lardin Hormozgan, wanda Bandar Abbas ita ce babban birninsa.
Bayanan da ƙungiyar sa ido kan rikice-rikice ta Acled ta tattara sun nuna cewa Amurka ta kai hare-hare aƙalla 96 a Bandar Abbas da kewaye tsakanin ranar 28 ga Fabrairu zuwa lokacin da tsagaita wuta ya fara aiki a ranar 8 ga Afrilu.
A cewar Acled, fiye da kashi ɗaya bisa uku na hare-haren an kai su ne a cibiyoyin soji, ciki har da sansanonin IRGC, wuraren adana makamai masu linzami, kadarorin rundunar ruwa da kuma sansanin soji da ke filin jirgin saman Bandar Abbas. Yawancin waɗannan wurare na kusa da unguwannin fararen hula.
Sai dai Acled ta ce ba ta iya tabbatar da ainihin wuraren da aka kai wa hari a sauran hare-haren ba.

Asalin hoton, Jack Garland / BBC
Hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai a lokacin yain sun yi sanadin mutuwar manyan shugabannin Iran, ciki har da Jagoran Addini, Ayatollah Ali Khamenei, tare da lalata muhimman cibiyoyin soja da na tattalin arziki, kuma sun yi mummunan tasiri ga shirin nukiliyar kasar.
Sai dai Magajin garin Bandar Abbas ya yi watsi da iƙirarin da ke cewa yaƙin ya raunana Iran.
Da yake magana da BBC, Mehdi Nobani ya ce Isra'ila da Amurka ba su cimma manufofinsu na yaki ba, ciki har da burin sauya gwamnati.
Ya kuma ce naɗin sabon Jagoran Addini, Mojtaba Khamenei—ɗan Ali Khamenei—ya ƙara haɗe kan ƙasar maimakon rarrabawa.
Ya ce idan yarjejeniyar tsagaita wuta ta rushe, Iran za ta rufe Mashigar Hormuz ba tare da ɓata lokaci ba.
A kasuwa kuma, yawancin mutanen da BBC ta yi ƙoƙarin tattaunawa da su sun ƙi yin magana. Wasu ba su bayyana dalili ba, yayin da wasu suka ce ba su yarda da yadda kafafen yaɗa labarai ke nuna Iran ba.

Asalin hoton, Jack Garland / BBC
A ƙarshe dai, wata matashiya da ta dawo daga ƙasar China ta shaida wa BBC cewa ta koma Iran ne domin kasancewa tare da an'uwanta a lokacin rikicin.
"Iranawa sun haɗa kai domin taimakon juna," in ji ta.
A kan wata ƙaramar hanyar kasuwar wata mata mai shekaru 55, Fatemeh, na sayar da lemo.
Kasuwar ta kasu kashi-kashi, inda ake samun kayayyaki iri-iri: kifaye da aka kawo daga Tekun Fasha da safe, dabino daga kudancin Iran, kayan lantarki da ake shigowa da su daga ƙasashen waje, turaruka, kayayyakin gida, da kuma tufafin gargajiya na mutanen Bandar.
Fatemeh ta ce ɗanta ya rasa aikinsa a lokacin yaƙin, yanzu kuma su na rayuwa ne da abin da take samu daga kasuwancinta.
"Ba mu son yaƙi. Idan bama-bamai suka fara sauka, muna tsoro. Trump ne ke son yaƙi. Ya kai mana hari ba tare da tsammani ba. Mu ba mu so wannan ba," in ji ta.

Asalin hoton, Jack Garland / BBC
Wata mata mai shekaru 40, Masoumeh, ta ji muna tattaunawa a gefe sai ta tsoma baki a maganar.
Ta ce: "Duk wani yaƙi yana kawo matsaloli. Yana shafar tattalin arziki da rayuwar mutane. Amma dole mu yi haƙuri."
Yayin da tattaunawa tsakanin bangarori ke ci gaba, kuma ana ci gaba da duba yiwuwar ɗorewar yarjejeniyar tsagaita wuta, ana ganin Mashigar Hormuz za ta ci gaba da zama abin da zai ci gaba da mamaye tattaunawa tsakanin Iran da Amurka.
Sai dai ga mutanen da ke rayuwa a yankin, rikicin ya fi shafar rayuwarsu ta yau da kullum—rashin aikin yi, da kwana cikin fargabar hare-hare ta sama, da kuma fatan ganin wannan tsagaita wuta ta dore.
Ƙarin rahotanni daga Jasmin Dyer
Nawal Al-Maghafi ta aiko da rahoto daga Tehran, amma an gindaya mata sharaɗin cewa ba za a buga rahoton nata a sashen BBC na Farisanci ba. Irin waɗannan takunkumi na aiki kan dukkan kafafen yaɗa labarai na ƙasashen waje da ke aiki a Iran.






