Muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni 17-23, 2025

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku sharhi da bayanai kan labarain wasanni a faɗin duniya daga ranar Asabar 17 zuwa 23 ga watan Mayun 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Yau za a kammala Bundesliga a Jamus, Bundesliga

    Kane

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a kammala wasannin mako na 34 a Bundesliga ranar Asabar, inda za a yi fafata tara a kuma lokaci ɗaya.

    Tuni Bayern Munich ta lashe kofin bana, kuma na 33 jimilla.

    Yanzu ana neman huɗun da za su wakilci kasar a Champions League a baɗi da wadda za ta Europa da kuma wadda za ta buga Conference League da waɗanda za su yi ban ƙwana da kakar bana.

    Tun a mako na 27 Bayern Munich ta samu gurbin shiga gasar zakarun Turai ta baɗi, yayin da Bayern Leverkusen ta samu nata tikitin a mako na 29.

    Waɗan da suka yi ban kwana da Bundesliga a kakar nan sun haɗa da Holstein da Bochum tun a karawar mako na 33.

    Wasannin makon karshe a Bundesliga ranar Asabar:

    • Augsburg da Union Berlin
    • Borussia Dortmund da Holstein Kiel
    • Borussia M'gladbach versus Wolfsburg
    • Freiburg da Eintracht Frankfurt
    • Heidenheim da Werder Bremen
    • Hoffenheim da Bayern Munich
    • Mainz 05 da Bayer Leverkusen
    • RB Leipzig da Stuttgart
    • St. Pauli da Bochum
  2. Labaran da jaridu kan wallafa kan cinikin ƴan wasa

    Rodrgo

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyoyi uku na Premier League wato Chelsea, Manchester City da Arsenal, sun yi nisa a tattaunawa da eja din dan wasan tsakiya na Brazil mai taka leda Real Madrid, Rodrygo mai shekara 24, wanda Bernabeu ke zawarci. (Fichajes - in Spanish)

    Aston Villa na fatan juya zaman aron da Axel Disasi a Chelsea zuwa dindindin a kakar wasa, inda kungiyar ta fara tattaunawa da dan wasan na Faransa mai shekara 27. (Footmercato - in French)

    Har wayau Chelsea, ta fitar da jerin 'yan wasan baya da ta ke son daukowa, ciki har da dan wasan Ingila meanwhile, Jarrad Branthwaite mai shekara 21, wanda ke taka leda a Everton, sai kuma na Ingila Marc Guehi, 24, da ke Crystal Palace. (Sky Sports)

  3. Southampton na fatan katse bikin da ake a Goodison

    Simon Rusk

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan riƙon ƙwarya a Southampton, Simon Rusk ya ce za su kawo karshen bikin barin Goodison Park a wasan karshe da Everton za ta yi a gida ranar Lahadi.

    Ƙungiyar ta Merseyside za ta buga wasan karshe a Goodison Park ranar Lahadi daga nan ta koma Bramley-Moore Dock daga farkon kakar baɗi.

    Amakon jiya Everton ta sanar cewar ta fasa rushe filin Goodison Park, maimakon hakan zai zama wajen da matan ƙungiyar za su ci gaba da taka leda, amma za ta rage yawan wajen zaman ƴan kallo.

    Soutahmpton ce ta karshe da za ta ziyarci Goodison Park a gasar Premier League, wadda a makon jiya ta tashi 0-0 da Manchester City mai neman gurbin Champions League a baɗi.

    ,

  4. Leicester City za ta dawo Premier League a baɗi - Van Nistelrooy

    Nistelrooy

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan Leicester, Ruud van Nistelrooy ya ce yana fatan za su shawo kan koma bayan da suka ci karo a bana, domin buga Premier League a baɗi.

    Leicester City tana daga cikin ukun da za su koma buga Championship a baɗi da ya hada da Ipswich Town da Southampton.

    A filin wasa na King Power, Leicester City za ta yi bikin barin Jamie Vardy ƙungiyar, wanda ya buga mata wasa 500 a kaka 13.

    Leicester ce ta lashe kofin Championship tare da jagorancin Enzo Maresca, wanda ya koma Chelsea da horar da tamaula.

    Sauran da suka mara mata baya sun haɗa da Ipswich Town da kuma Southampton kuma sune dai suka kara komawa Championship.

  5. Cucureira ya kai Chelsea mataki na huɗu a teburin Premier, Premier League

    Chelsea

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙyaftin ɗin Chelsea, Reece James ya yaba da ƙwazon da suka sa da ta kai suka doke Manchester United 1-0 ranar Juma'a, hakan ya sa ƙungiyar take cikin gurbin masu buga Champions League a baɗi.

    Sauran minti 20 a tashi daga wasan ne Chelsea ta ci ƙwallo ta hannun Marc Cucureira, hakan ya sa ƙungiyar Stamford t koma ta huɗun teburi.

    Idan Chelsea za ta doke Nottingham Forest a makon gobe, kenan za ta samu gurbin Champions League a karon farko tun bayan 2023.

    Manchester United ta ci karo da koma baya, wadda ta yi rashin nasara shida daga karawa takwas baya a Premier League.

    United, wadda take buga kaka mafi muna na fatan cin Aston Villa a wasan karshe, idan ba haka ba za ta kasance ta 17 a kasan teburi.

    A makon da za mu shiga ne United za ta buga wasan karshe a Europa League da Tottenham, kuma duk wadda ta yi nasara za ta samu gurbin Champions League a baɗi.

  6. Labaran da jaridu kan wallafa kan cinikin ƴan wasa

    Liverpool ta bi sahun Real Madrid da Barcelona kan dan wasan tsakiya na Ingila mai taka leda a Crystal Palace Adam Wharton, 21, kan kudi fam miliyan 60. (Daily Mail - subscription required)

    Watakil Liverpool din ta dauko mai kai hari na Faransa da ke taka leda a Nkunku, 27, a kaka mai zuwa. (Footmercato - in French)

    Wolves na ci gaba da zage damtse domin dauko dan wasan tsakiya na Ingila mai taka leda a Liverpool, Harvey Elliott, 22. (GiveMesport)

  7. Labarai da dumi-dumi, Huijsen zai koma Real Madrid daga ranar 1 ga watan Yuni, Real Madrid

    Huijsen

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai tsaron bayan Bournemouth, Dean Huijsen zai koma Real Madrid da taka leda daga ranar 1 ga watan Yunin 2025, kamar yadda ƙungiyoyin suka sanar ranar Asabar.

    Tuni matashin ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta kare a karshen kakar 2030, kuma yana da damar buga wa Real Club Worl Cup da za a yi a Amurka a kakar nan.

    Bournemouth mai buga Premier League ta sanar cewar Real Madrid ta biya ƙunshin ƙwantiragin mai tsaron bayan da ya kai ($66.36 million), hakan ya sa ta ɗauki mai shekara 20 da zai taka mata leda kaka biyar.

    Real Madrid ta riga manyan ƙungiyoyin da ke son sayen matashin, sakamakon rawar da yake takawa a Bournemouth, wanda yake buga Premier League tun da ya koma can daga Juventus.

    Matashin ya buga karawa 34 a dukkan fafatawa a Bournmouth da cin ƙwallo uku.

    Ɗan wasan tawagar Sifaniya, wanda aka haifa a Netherlands ya fara yi wa Sifaniya a karawar da ta yi da Netherlands a cikin watan Maris a Nations League Cup.

  8. Barkan mu da saduwa

    Jama'a barkan mu da wannan lokacin na sharhi da bayanai kan labarin wasanni kai-tsaye da ni Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tudun Wada zan gabatar a rana irin ta Asabar.

    Za ku iya bayar da gudunmawa ko tafka muhawara kai-tsaye a BBC Hausa ko kuma ta X.