Muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni 17-23, 2025

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku sharhi da bayanai kan labarain wasanni a faɗin duniya daga ranar Asabar 17 zuwa 23 ga watan Mayun 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Nottingham Forest na fatan samun gurbin Champions League, Premier League

    Forest

    Asalin hoton, Getty Images

    Nottingham Forest ta samu damar kammala kakar bana cikin ƴan biyar ɗin farko a Premier League, sakamakon da ta je ta doke West Ham United 2-1 a wasan mako na 37 ranar Lahadi.

    Da wannan sakamakon Forest tana mataki na bakwai da maki 65, iri ɗaya da na Manchester City ta shida, mai ƙwantan wasa, wadda Crystal Palace ta ci 1-0 ta lashe FA Cup ranar Asabar a Wembley.

    Forest za ta karɓi bakuncin Chelsea a wasan karshe ranar Lahadi, wadda za ta yi kokarin cin wasan daga nan ta yi fatan wasu sakamakon wasannin su ba ta damar shiga ƴan biyar ɗin farko a Premier League a bana.

    Chelsea tana mataki na huɗu da maki 66, iri ɗaya da na Aston Villa ta biyar.

  2. Di Maria ya gama wasa a Benfica daga karshen kakar nan, Benfica

    Angel Di Maria

    Asalin hoton, Getty Images

    Angel di Maria ya gama wasa a Benfica daga karshen kakar nan, kamar yadda ɗan kasar Argentina ya sanar, bayan da ƙungiyar ta kasa lashe babban kofin tamaula na Portugal.

    Ranar Asabar suka tashi 1-1 da Braga, hakan ya sa Sporting ta ɗauki kofin da tazarar maki biyu tsakani da Benfica.

    Mai shekara 37, wanda ya yi ritaya daga buga wa Argentina tamaula a bara, bayan yi mata karawa 145, ya yi kaka biyar a Benfica, wadda ya yi mata wasa karo biyu.

    Ya koma Benfica a 2023, bayan takaleda a Real Madrid da Manchester United da Paris St Germain da kuma Juventus.

    Benfica za ta kece raini da Sporting a Portuguese Cup ranar 25 ga watan Mayu, daga nan ta je gasar Club World Cup daga 16 ga watan Yuni a Amurka.

    Di Maria, wanda ƙwantiraginsa zai kare a karshen watan Yuni, bai fayyace ko zai buga Club World Cup ba.

  3. Verstappen ya lashe Emilia-Romagna Grand Prix a Imola

    Formula 1

    Asalin hoton, Getty Images

    Direban motar RRed Bull, Max Verstappen shi ne ya lashe tseren motocin Formula One a Emilia-Romagna Grand Prix at Imola

    Matukin motar McLaren, Lando Norris shi ne na biyu, yayin da Oscar Piastri ya kare a mataki na uku da kuma direban Ferrari, Lewis Hamilton a matsayi na huɗu.

  4. Chelsea ta mata ta lashe FA Cup bayan cin Man United ranar Lahadi, Chelsea 3-0 Man United

    FA Cup

    Asalin hoton, Reuters

  5. Ƴan Real Madrid huɗu na fuskantar hukuncin dakatarwa

    Real Madrid

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan wasan Real Madrid huɗu na fuskantar dakatarwa a wasan da za ta kara a gidan Sevilla ranar Lahadi a La Liga.

    Ƴan ƙwallon sun haɗa da Dani Ceballos da Federico Valverde da Lucas Vazquez da kuma Jude Bellingham.

    Dukkan ƴan wasan suna cikin koshin lafiya, amma duk wanda aka sa a wasan Sevilla yana da ƙyau ya yi taka tsantan, idan ba haka ba, ba zai yi karawar karshe ba a La Liga.

    Kuma duk wanda aka bai wa katin gargaɗi a wasan na Sevilla, ba zai buga wa Real wasan karshe da za ta yi da Real Sociedad ba.

    A dokar La Liga, duk ɗan wasan da ya karɓi karin gargaɗi biyar jimilla, zai yi hutun karawa ɗaya.

  6. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin ƴan ƙwallo, Aston Villa

    Marcus Rashford

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan wasan gaba na Ingila mai taka leda a Manchester United, Marcus Rashford, 27, da ke zaman aro a Aston Villa, ya amince a rage ma sa albashi domin ya samu komawa taka leda kungiyar Barcelona a kaka mai zuwa. (Mundo Deportivo - in Spanish)

    Tun da fari Barcelona na son daukar Rashford a matsayin aro daga Manchester United, amma ta na fatan sayan dan wasan nan gaba kadan idan ciniki ya kaya. (Sport - in Spanish)

    Mai tsaron baya na Poland kuma dan wasan Arsenal, Jakub Kiwior, 25, na samun zawarawa ciki har da Napoli, sai dai kulub din na Serie A na son Gunners su sassauta farashin fam miliyan 30 da suka sanya kan dan wasan. (Calciomercato - in Italian)

  7. Sporting Lisbon ce ta lashe Primeira Liga na Portugal na bana

    Sporting Lisbon

    Asalin hoton, Getty Images

    Sporting Lisbon ta lashe kofin Primeira Liga na Portugal na bana, bayan cin Vitoria Guimaraes 2-0 ranar Asabar 17 ga watan Mayu.

    Ƙungiyar ta yi bikin ɗaukar kofin kakar nan a Marques de Pombao, inda ko ina ganin launin kore kake yi.

    Sporting ta yi ta ɗaya a kan teburin bana da maki 82 da tazarar maki biyu tsakani da Benfica ta biyu, wadda ta tashi 1-1 da Sporting Braga.

    Sporting, wadda ta lashe kofin babbar gasar tamaula ta Portugal karo na 21 jimilla, ta ɗauki kofin a karo na biyu a jere a karon farko tun bayan da ta haɗa huɗu a jere daga 1951-54.

    A farkon watan Nuwamba, kociyan Sporting, Ruben Amorim ya bar ungiyar ya koma Manchester United, wanda ya maye gurbin Erik ten Hag.

    A makon da za mu shiga ne United za ta buga wasan karshe a Europa League da Tottenham.

  8. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin ƴan ƙwallo

    Florian Wirtz

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester City na shirin kashe fam miliyan 180 kan kwantiragi biyu na dan wasan Jamus da ke taka leda Bayer Leverkusen, Florian Wirtz, 22, da dan wasan tsakiya na Netherlands mai taka leda a AC Milan Tijjani Reijnders, 26. (Mirror)

    Manchester United ba za ta kori manaja Ruben Amorim, ko da kuwa ba su kai bantensu a wasan karshe na cin kofin Nahiyar Turai da za su kara da kungiyar Tottenham. (Mirror)

    AC Milan ta yi watsi da tayin sama da fam miliyan 50 da Manchester City kan dan wasanta Reijnders. (Teamtalk)

  9. Wasannin mako na 37 a La Liga ranar Lahadi 18 ga watan Mayu:, La Liga mako na 37

    • Atlético Madrid da Real Betis
    • Barcelona da Villarreal
    • Celta Vigo da Rayo Vallecano
    • Las Palmas da Leganés
    • Mallorca da Getafe
    • Osasuna da Espanyol
    • Real Sociedad da Girona
    • Real Valladolid da Deportivo Alavés
    • Sevilla da Real Madrid
    • Valencia da Athletic Club
  10. Ben Mee zai bar Brentford da zarar an kammala kakar bana, Premier League

    Ben Mee

    Asalin hoton, Getty Images

    Ben Mee ya sanar cewar zai bar Brentford a karshen kakar nan.

    Tsohon ɗan wasan tawagar Ingila ta matasa ƴan kasa da shekara 21 ya koma Brentford a yulin 2022, bayan kaka 11 a Burnley.

    Ya buga wa Brentford karawa 67 da ci mata ƙwallo biyar a matakin mai tsaron baya.

    To sai dai wasa biyu aka fara da shi a bana a Premier League da kuma biyar da ya shiga canjin ɗan ƙwallo, hakan ya sa mai shekara 35 ya yanke hukuncin yin gaba daga 30 ga watan Yunin 2025.

  11. Ƴan Real Madrid da za su fafata da Sevilla, La Liga mako na 37

    Mbappe

    Asalin hoton, Getty Images

    Real Madrid za ta je Sevilla, domin buga wasan mako na 37 a La Liga ranar Lahadi a filin wasa na Ramon Sanchez-Pizjuan.

    Real Madrid wadda take ta biyu a teburin La Liga ta doke Sevilla 4-2 a wasan farko a bana a Santiago Barnabeu ranar 22 ga watan Disambar 2024.

    Ƴan wasan Real Madrid:Masu tsare raga: Courtois, Lunin da Sergio Mestre.Masu tsare baya: Lucas Vázquez, Vallejo, Fran García, Youssef, Jacobo da Mario Rivas.Masu buga tsakiya: Bellingham, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler, Ceballos da Chema.Masu cin ƙwallaye: Mbappé, Endrick, Gonzalo da Víctor Muñoz.

  12. Ƴan Barca da za su kara da Villareal a La Liga ranar Lahadi

    Barca

    Asalin hoton, Getty Images

    Wadda ta lashe La Liga na bana, Barcelona za ta kara da Villareal a wasan mako na 37 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya ranar Lahadi a filin wasa na Estadi Olímpic Lluís Companys.

    Tuni Hansi Flick ya bayyana ƴan wasa 23 da zai fuskanci Villareal daga nan saura karawa ɗaya a karkare kakar bana.

    Ƴan wasan Barcelona 23:

    Ter Stegen, Cubarsí, Balde, I. Martinez, Gavi, Pedri, Lewandowski, Ansu Fati, Raphinha, Iñaki Peña, Pablo Torre, Christensen, Fermín, M. Casadó, Pau Víctor, Lamine Yamal, Olmo, F. De Jong, Eric, Szczęsny, H. Fort, Gerard Martín da kuma S. Domínguez.

    Wasannin mako na 37 a Spanish La Liga ranar Lahadi 18 ga watan Mayu:

    • Atlético Madrid da Real Betis
    • Barcelona da Villarreal
    • Celta Vigo da Rayo Vallecano
    • Las Palmas da Leganés
    • Mallorca da Getafe
    • Osasuna da Espanyol
    • Real Sociedad da Girona
    • Real Valladolid da Deportivo Alavés
    • Sevilla da Real Madrid
    • Valencia da Athletic Club
  13. Everton ta ci wasan karshe a filin Goodison Park

    Goodison Park

    Asalin hoton, Getty Images

    Everton ta ci wasan karshe a filin Goodison Park, bayan shekara 133 tana taka leda a ciki.

    Ƙungiyar da David Moyes ke jan ragama ta doke Southampton 2-0 a gasar Premier League karawar mako na 37 ranar Asabar.

    Iliman Ndiaye ne ya ci mata ƙwallyen, yayin da Everton za ta koma taka leda a Bramley-Moore Dock a farkon kakar baɗi.

    Everton tana ta 13 da maki 45 a Premier League, ita kuwa Southampton, wadda take ta karshen teburi, wadda za ta koma buga Championship a baɗi tana da maki 12 a karawa 37.

    Wasannin mako na 38 a Premier League ranar 25 ga watan Mayu:

    • Bournemouth da Leicester City
    • Fulham da Manchester City
    • Ipswich Town da West Ham United
    • Liverpool da Crystal Palace
    • Manchester United da Aston Villa
    • Newcastle United da Everton
    • Nottingham Forest da Chelsea
    • Southampton da Arsenal
    • Tottenham da Brighton & Hove Albion
    • Wolverhampton Wanderers da Brentford
  14. Za mu ɗauki Champions League - Araujo

    Barca

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai tsaron bayan Barcelona, Ronald Araujo ya ce yana da tabbaci, bayan da suka lashe La Liga da Copa del Rey da Spanish Super Cup, za su ɗauki Champions League nan gaba.

    Dubban magoya bayan Barcelona sun taya ƙungiyar bikin lashe kofi uku a bana da ta yi ranar Juma'a, kwana ɗaya da ta ɗauki La Liga a gidan Espanyol da ta doke 2-0.

    ''Muna cike da murna, kuma mun cancanta. Ba wanda ya sa tsammanin za muyi wani abin kirki a bana, sai gashi mun lashe kofi uku a Sifaniya.''

    ''Mutane suna alfahari da Barcelona darawar da muka taka, domin muna da fitattun ƴan ƙwallo.''

    ''An fitar da mu a Champions League, amma za mu ɗauki kofin nan gaba.''

    Inter Milan ce ta yi waje da Barcelona a zagayen daf da karshe a Champions League, kofin da rabon ta da shi tun 2015.

  15. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin ƴan ƙwallo

    Frimpong

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan wasan Netherlands mai taka leda a Bayer Leverkusen, Jeremie Frimpong, 24, inda suka amince da kwantiragin shekara 5 da Liverpool. (Talksport)

    Dan wasan Jamus Leroy Sane, 29, ya yi watsi da tayin kwantiragin da Bayern Munich daidai lokacin da ake rade-radin kungiyoyin Premier League da La Liga, na zawarcinsa. ( Sky Germany - in German)

    Da alama mai tsaron ragar Aston Villa, Emiliano Martinez, zai bar kulub din sakamakon yadda dan wasan na Argentina mai shekara 32 ke samun goron gayyata daga kungiyoyi da dama ciki har da kulub din Saudiyya da kuma wasu biyu na Turai. (Mundo Albiceleste - in Spanish)

    Martinez da iyalansa sun samu matsuguni a Birmingham, amma ya na bukatar yin gaba idan har ya na son daukar karin kofuna.(Ole - in Spanish)

  16. Za a fafata tsakanin Arsenal da Newcastle a Premier

    Tonali

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal, wadda take ta biyun teburin Premier League za ta karɓi bakuncin Newcastle United a Emirates a wasan mako na 37 ranar Lahadi.

    Arsenal tana da maki 68, ita kuwa Newcatle maki 66 take da shi, kuma dukkansu suna neman gurbin Champions League a baɗi.

    Arsenal ta ci wasa 18 a Premier League da canjaras 14 aka doke ta karawa huɗu, ita kuwa Newcastle ta yi nasara 20 da canjaras shida da rashin nasara 10.

    To sai dai Newcastle tana da maki 66 iri ɗaqya da na Chelsea ta huɗu da kuma Aston Villa ta biyar.

    Newcastle ta yi nasara uku a kan Arsenal, kuma Alexander Isak na fatan zura ƙwallo na uku a ragar Arsenal a kakar nan a dukkan fafatawa.

    Yanzu haka Isak ya ci ƙwallo 23 a Premier League, inda Salah ne ke gabansa mai 28 a raga.

  17. Will Still ya bar aikin horar da Lens mai buga Ligue 1, Ligue 1

    Will Still

    Asalin hoton, Getty Images

    Will Still ya bar aikin horar da RC Lens Mai buga Ligue 1, domin zai koma cikin iayalansa a Burtaniya, kamar yadda ya sanar ranar Asabar.,

    Mai shekara 32, wanda ya horar da Reims a baya, ya koma Lens a bara daga watan Yuni kan yarjejeniyar kaka uku, wanda ya kai ƙungiyar mataki na takwas a teburin Ligue 1 a bana.

    ''Ba zan ci gaba da aiki da Lens ba a kaka mai zuwa. Wannan ita ce rana ta karshe a ƙungiyar nan'', kamar yadda Stll ya sanar da manema labaran wasanni, bayan da Lens ta doke Monaco 4-0.

  18. Jama'a barkan mu da wannan lokacin

    Sunana Mohammed Abdu ke muku barka da shiga shirin sharhi da bayanai kan labaran wasanni a ranar Lahadi 18 ga watan Mayun 2025.

    Za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko a X kai tsaye.

  19. Nan muka kawo karshen shirin

    Nan na kawo karshen shirin sharhi da bayanai kan labarin wasanni a ranar Asabar da fatan kun ji dadin shirin za kuma ku sake tarawa ranar Lahadi daga 12:00 na rana agogon Najeriya da Nijer.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tudun Wada ke muku fatan alheri.

  20. Barcelona ta cancanci lashe La Liga - Ancelotti, Real Madrid

    Barcelona ta cancanci lashe La Liga, kamar yadda Hansi Flick ya dora ƙungiyar da nasarorin da ta yi ta samu da salon taka leda da take yi in ji Carlo Anclotti.

    Ancelotti ya sanar da hakan a shirin da Real Madrid ke yi na zuwa gidan Sevilla a La Liga, wadda take ta 14 a kasan teburi.

    Bayan da Barcelona ta doke Real Madrid ta lashe La Liga da Copa del Rey da kuma Spanish Super Cup a kakar nan, yanzu Club World Cup ne ya rage da ƙungiyar ke fatan ɗauka kenan.

    Barcelona ta yi nasara a wasa huɗun da suka yi a kakar nan a dukkan karawa, yayin da Barcelona ta zura ƙwallo 97 a wasa 36 a lik a bana.

    A karshen kakar nan Carlo Ancelotti zai bar Real Madrid zai koma horar da Brazil.

    Kociyan ɗan kasar Italiya ya lashe kofi 15 a kaka biyu da ya yi a ƙungiyar Santiago Bernabeu.

    Ge

    Asalin hoton, Getty Images