Everton ta yi ban kwana da Goodison Park, Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Magoya bayan Everton sun yi ban kwana da filin Goodison Park, bayan shekara 133 suna taka leda a ciki.
Ƙungiyar ta Mersyside za ta koma buga tamaula a Bramley-Moore Dock a kaka mai zuwa.
To amma Everton za ta bai wa matan ƙungiyar filin Goodison Park, domin ci gaba da wasanni a ciki, amma za ta rage yawan kujerun zaman ƴan kallo.















