Ko Man United za ta lashe Europa League?, Wasan karshe a Europa League

Asalin hoton, Getty Images
Za a buga wasan karshe a Europa League ranar Laraba tsakanin Tottenham da Manchester United.
Duk wadda ta yi nasara za ta wakilci Ingila a Champions League a kaka mai zuwa.
Wannan shi ne karo na huɗu da za su kece raini a bana:
Kakar 2024/2025
Premier League ranar Lahadi 16 ga watan Fabrairun 2025
- Tottenham 1 - 0 Man Utd
English League Cup ranar Alhamis 19 ga watan Disambar 2024
- Tottenham 4 - 3 Man Utd
Premier League ranar Lahadi 29 ga watan Satumbar 2024
- Man Utd 0 - 3 Tottenham
Ƙungiyoyin ba sa kokari a kakar nan a Premier League, inda United take ta 16 da maki 39 da tazarar maki ɗaya tsakani da Tottenham ta 17.
















