Muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni 17-23, 2025

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku sharhi da bayanai kan labarain wasanni a faɗin duniya daga ranar Asabar 17 zuwa 23 ga watan Mayun 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. An ɗaure mutum biyar da suka yi wa Vinicius Jr kalaman wariya, Real Madrid

    Vinicius

    Asalin hoton, Getty Images

    An yanke hukuncin ɗauri ga mutum biyar da aka samu da laifin yi wa Vinicius Jr kalaman wariya lokacin gasar La Liga ta Sifaniya.

    A cikin watan Disambar 2022 aka ci zarafin ɗan wasan tawagar Brazil a wasan da Real Madrid ta doke Real Valladolid 2-0 a lokacin da aka sauya ɗan wasan a filin wasa na Jose Zorilla.

    Kotun da take Valladolid ta yanke hukuncin shekara ɗaya ga kowanne mutum da cin tara da ta kai Yuro 1,080 zuwa 1,620.

    To sai dai an jingine hukuncin ɗaurin da cewr har idan ba a sake samunsu da laifi irin wanda suka aikata, kuma ba za su sake shiga kallon tamaula a sitadiya shekara ukun.

  2. Za a zaɓi sabon shugabn hukumar ƙwallon Brazil ranar Lahadi, Brazil

    Brazil

    Asalin hoton, Getty Images

    Tubabben shugaban hukumar kwallon kafar Brazil, Ednaldo Rodrigues ya janye daga ɗaukaka kakar da ya shigar, bayan da wata kotu a Rio de Janeiro ta sauke shi a makon jiya.

    A wata sanarwa da aka fitar daga tsagin tsohon shugaban ta ce – ya yanke wannan hukuncin ne domin a samu kwanciyar hankali da natsuwa a hukumar ƙwallon kafar Brazil, domin kasar ta samu ci gaba a fannin taka leda.

    Tuni an tsara yin zaben sabon shugaba ranar Lahadi da mai rikon kwarya zai gudanar, Fernando Sarney, ɗaya daga mataimakin da ya bukaci a tube Rodrigues.

    Tsohon shugaban ya sanar ta hannun lauyansa cewar ba zai yi takara ba, kuma ba zai goyi da bayan duk wani mai neman mukami a hukumar kwallon kafar Brazil ba.

  3. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin ƴan wasa, Daga jaridu

    Darwin Nunez

    Asalin hoton, Getty Images

    Brighton ta amince da yarjejeniyar daukar dan wasan bayan Faransa Olivier Boscagli mai shekaru 27a kyauta daga PSV Eindhoven. (Sky Sports)

    Manchester City za ta fafata da Liverpool don siyan dan wasan Bournemouth mai shekara 21 da kuma dan bayan Hungary Milos Kerkez. (i paper)

    Liverpool ta karbi tayi daga kungiyoyin Saudiyya kan dan wasan gaban Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 25, dan wasan Portugal Diogo Jota da dan wasan Colombia Luis Diaz, dukkansu 28. (Sky Germany)

  4. De Bruyne ba zai buga Club World Cup ba, Manchester City

    De Bruyne

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Manchester City, Kevin De Bruyne ya ce da kyar ne idan zai buga wasa a Club World Cup, saboda kada ya ji rauni, wanda zai bar Etihad a karshen kakar nan.

    Mai shekara 33 zai bar kungiyar bayan kaka 10 da lashe kofin Premier League shida da Champions League da kuma Club World Cup a 2023.

    Yarjejeniyar Ƙyaftin ɗin tawagar Belgium za ta kare a karshen watan Yuni a City,

    Kenan yana da damar buga wasa uku a gasar, sai dai ya ce ba zai yi kasassa ɓa ba, saboda kada ya ji rauni, domin wa zai kula da lafiyarsa, sannan yana fatan neman wata kungiyar a badi.

    Za a fara Club World Cup a Amurka daga 14 ga watan gobe zuwa 13 ga watan Yuli.

  5. Labaran da jaridu ke wallafa kan cinikin ƴan ƙwallo, Daga jaridu

    RRaphinha

    Asalin hoton, Getty Images

    Barcelona ta cimma yarjejeniya da dan wasan Brazil Raphinha kan sabuwar yarjejeniyar ci gaba da zama a kulob din har zuwa watan Yunin 2028. (Fabrizio Romano)

    Kocin Nottingham Forest Nuno Espirito Santo na iya barin kungiyar a karshen kakar wasa ta bana saboda rikicin cikin gida a kungiyar. (Footmercato)

    Leicester City na shirin korar kocinta Ruud van Nistelrooy kuma tana ci gaba da tattaunawa domin nada tsohon kocin Southampton Russell Martin. (Football Insider)

  6. Wa zai lashe Europa League tsakanin Tottenham da Man United?

    Europa LEAGU

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a buga wasan karshe a Europa League tsakanin kungiyoyin Ingila, wato Tottenham da Manchester United da za a yi tata burza a birnin Bilbao a Sifaniya ranar Laraba.

    Wannan shi ne karo na huɗu da za su fafata a tsakaninsu a bana, inda Tottenham ta yi nasara a wasa uku hae da biyu a Premier, sannan ta fitar da United a League Cup.

    To sai dai kungiyoyin biyu sun fuskanci kalubale a kakar nan a babbar gasar tamaula ta Ingila,

    Inda United take mataki na 16 da maki 39 da tazarar maki daya tsakani da Tottenham ta 17, wadda rabonta da wani kofi ya yi daidai da matakin da take a teburi

    Wannan wasan yana da fa'ida ga dukkan kungiyoyin biyu, domin duk wadda ta ci kofin za ta je Champions League a badi.

    Ita kuwa United idan har ba ta ci kofin ba, zai zama karon farko da za ta kasa halartar gasar zakarun Turai tun bayan 2014/15 - kenan ZA ta kare kakar bana mafi muni a tarihi tun 1973/74.

  7. Mummunan tarihin da Man United da Tottenham suka kafa a Premier ta bana, Premier League

    Europa League

    Asalin hoton, Getty Images

    Tottenham da Manchester United za su kara a wasan karshe a Europa League ranar Laraba.

    Manchester United tana mataki na 16 da maki 39 a teburin Premier League da tazarar maki ɗaya tsakani da Tottenham ta 17.

  8. Dan Evans ya kai zagaye na biyu a wasan share fagen shiga US Open, Ƙwallon tennis

    Dan Evans ya yi nasara a kan Billy Harris a wasan zagayen farko a neman gurbin shiga French Open.

    Evans ya yi kasa zuwa mataki na 215 a jerin masu buga tennis a duniya a karon farko - yana buga wasan na neman shiga gasar bana a karon farko tun 2014.

    Harris ya yi rashin nasarar a hannun Evans da cin 7-5 6-3.

  9. 'Ba za a fara farkon kaka da Bellingham ba saboda jinyar kafaɗa'

    Jude Bellingham

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan tsakiyar Real Madrid, Jude Bellingham ba zai buga aƙalla mako shida na farkon kakar wasa mai zuwa ba, saboda za a yi masa tiyatar kafaɗa bayan ƙare gasar Kofin Duniya ta Ƙungiyoyi.

    Ƙungiyar ta shirya yi wa ɗan wasan na Ingila tiyata a Amurka, bayan kammala gasar, domin magance matsalar ciwon kafaɗa da yake fama da ita tun 2023.

    Ɗan wasan mai shekara 21 ya riƙa ɗaure kafaɗar tasa a wasu wasannin da ya buga wa Ingila da Real.

    Za fara gasar cin Kofin Duniya na Ƙungiyoyi da aka faɗaɗa zuwa ƙungiyoyi 32 a Amurka tsakanin 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuni.

    Ana sa ran ɗan wasan ba zai buga duka wasannin sada zumunta da ƙungiyoyi ke bugawa gabanin sabuwar kaka da kuma wasan Ingila ne neman gurbin Gasar Kofin Duniya da za ta buga da Andorra da kuma Serbia a watan Satumba

  10. Zan bar City idan ta ɗauki ƴanwasa da yawa - Guardiola

    Pep Guardiola

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya shaida wa masu ƙungiyar cewa ba ya buƙatar ɗaukar ƴanwasa masu yawa a kakar wasa mai zuwa.

    Kocin ɗan asalin Sifaniya ya ce ba ye idan har mamallakan ƙungiyar ba su amince da buƙatar tasa ba yana barin ƙungiyar, saboda a cewarsa ba ya son yanayin da zai riƙa ajiye ƴanwasa masu yawa a benci, a cewar Sky Sports.

    Ƙunciya City za ta fita kasuwa domin neman ƴanwasa a ƙoƙarin sake gina ƙungiyar, yayin da manyan ƴanwasan ƙungiyar za su bar ƙungiyar a kaka.

    Tuni dai kaftin ɗin ƙungiyar Kevin De Bruyne ya yi wasansa na ƙarshe a Etihad ranar Talata, yayin da ƙungiyar ta samu nasara da ci 3-1.

    Manchester City dai ta gamu da cikas a kakar wasa ta bana, bayan da ta ƙare kakar ba tare da daukar kofi ba, karo na farko cikin shekaru.

  11. 'Arsenal na dab da ɗaukar ɗan wasan gaba Viktor Gyokeres'

    Viktor Gyokeres

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Arsenal na shirin ɗaukar ɗan wasan gaban Sporting CP, Viktor Gyokeres kamar yadda jaridar wasanni ta football365 ta ruwaito.

    Arsenal ta fuskanci matsalolin ƴanwasan gaba a kakar wasan da ke dab da ƙarewa, yayin da ƙungiyar da gaza lashe kowane irin kofi.

    Bayan ƙarewa a mataki na biyu a Gasar Premier da samun gurbin zuwa Gasar Zakarun Turai ta baɗi a yanzu hankalin ƙungiyar ya karkata kan samun ɗan wasan gaba, domin sake gina kanta.

    A ƙarshen kakar wasa da muke ciki ne Gyokeres ɗan asalin Sweden zai bar ƙungiyar Sporting bayan ƙarewar kwantiraginsa, kamar yadda Fabrizio Romano fitaccen ɗanjaridar wasanni ya bayyana a shafinsa na X.

  12. Za mu sa ƙwazo mu lashe Europa League - Maguire, Wasan karshe a Europa League

    Harry Maguire

    Asalin hoton, Getty Images

    Harry Maguire ya ce za su yi iya yi, domin faranta ran magoya bayan Manchester United wajen lashe Europa League na bana.

    Za a kece raini tsakanin Tottenham da Manchester United ranar Laraba a birnin Bilbao, kuma duk wadda ta yi nasara za ta wakilci Ingila a Champions League a badi.

    United da Tottenham sun fuskanci kalubale a kakar nan a Premier League, inda United take mataki na 16 da maki 39 da tazarar maki daya tsakani da Tottenham ta 17.

    Idan har United ba ta lashe kofin ba, zai zama karon farko rabon da ta halarci wasannin zakarun Turai tun bayan 2014/15 - kenan kaka mafi muni tun 1973/74.

  13. Jorgensen ne zai tsare ragar Chelsea a Europa League, Europa League

    Filip Jorgensen

    Asalin hoton, Getty Images

    Filip Jorgensen ne zai tsare ragar Chelsea a wasan karshe a Conference League da za su kara da Real Betis, in ji koci, Enzo Maresca kamar yadda ya sanar ranar Talata.

    Wasa ɗaya ne kacal golan bai yi ba a gasar, yayin da Chelsea ke amfani da mai tsare mata raga da ɗan kasar Sifaniya Robert Sanchez a Premier League, wanda ya yi wasa 31.

    Maresca ya ce ba adalci bane a ce ba a saka Jorgensen ranar wasan ba, sakamakon rawar da ya taka a gasar ta Conference League ta bana.

    To sai dai ana tantama kan koshin lafiyar Christopher Nkunku da kuma Marc Guiu a wasan karshe da za a yi a Poland a birnin Wroclaw ranar 28 ga watan Mayu, sakamakon jinya.

  14. Doucoure zai bar Everton a karshen kakar nan, Everton

    Abdoulaye Doucoure

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan wasan Everton, Abdoulaye Doucoure ya sanar zai bar ƙungiyar a karshen kakar bana, kamar yadda mai shekara 32 ya sanar a kafarsa ta sada zumunta a Instagram ranar Talata.

    Ya sanar cewar daga kakar nan ya kammala shekara biyar da ya yi a Everton.

    Doucoure, wanda ya buga wasa 165 a Everton tun bayan da ya koma ƙungiyar daga Watford a 2020, an sa ran zai tsawaita zamansa kan yarjejeniyar kaka daya tun farko.

    An canja shi a wasan karshe da Everton ta yi a Goodisson Park ranar Lahadi a gasar Premier League da suka doke Southampton 2-0 a karawar mako na 37.

  15. Shagon Ramadan ya sumar da Bagobiri, Damben gargajiya

    An buga damben gargajiya a jiya a gidan wasa da ke Ado Bayero Square a Kano, Nigeria.

    An tashi canjaras tsakanin Buhari da Shagon Reza Bunza

    da na Shagon Babba da Bahagon biyu

    Yayin da Shagon Biyun Sama'aila ya buge Bille

    Da wanda Shagon Ramadan ya sumar da Bagobiri

  16. Guardiola ya ce kakar bana ya fuskanci kalubale, Manchester City

    Pep Guardiola

    Asalin hoton, Getty Images

    Pep Guardiola ya kwatanta kakar bana mai muni mai dan karen kalubale a shirin da yake na neman gurbin Champions League ruwa a jallo a baɗi.

    City ta karasa kakar nan ba tare da lashe kofi koda na shayi ba, sakamakon rashin nasara 1-0 a hannun Crystal Palace a Wembley a wasan karshe a FA Cup.

    Sai dai idan har City ta ci wasa biyu da ya rage mata da Bournemouth da za ta yi a ranar Talata da kuma da Fulham ranar Lahadi, tabbas za ta wakilci Ingila a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai.

    Kungiyar Etihad ta fara kakar bana da fatan lashe Premier League na biyar a jere, amma sai aka yi ta ragargazarta a dukkan fafatawa.

    Ba wanda zai ce maka City za ta shiga cikin masu rige rigen neman gurbin Champions League a bana.

  17. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin ƴan ƙwallo, Daga jarida

    Frimpong

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan wasan gaba na Wolves, Matheus Cunha zai koma taka leda a ƙungiyar Manchester United a ƙarshen kaka mai zuwa, inda ake sa ran darajar ɗan wasan na Brazil mai shekara 25 ta kai sama da fam miliyan 62. (Sky Sports)

    Manchester United ta tattauna da ɗan wasan Ingila da ke taka leda a Ipswich Town Liam Delap, 22. (The Athletic)

    A ranar Litinin ne ɗan wasan baya na Bayer Leverkusen, Jeremie Frimpong, 24, ya kammala gwajin lafiya da Liverpool, bayan nan ne mai tsaron gida na Netherlands zai koma Birtaniya a ranar Lahadi mai zuwa. (Sky Sports)

  18. Reina zai yi ritaya daga taka leda a karshen kakar nan

    Reina

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon ɗan wasan tawagar Sifaniya da Liverpool, Pepe Reina zai yi ritaya a karshen kakar nan, kamar yadda mai shekara 42 ya sanar.

    Reina, wanda ya fara taka leda daga makarantar Barcelona, ya yi kaka takwas a Liverpool, wajen da ya ɗauki FA Cup da League Cup da Premier League da lashe safar hannu ta zinare a matakin wanda ƙwallo da yawa bai shiga ragarsa ba.

    Ya kuma taka leda a Bayern Munich da Napoli da kuma AC Milan, daga nan ya koma Como a watan Yuli a bara, inda ya yi wasa 11 a gasar Serie A ta kakar nan.

    Reina, zai buga wasan karshe da Como da za ta yi ranar Juma'a da Inter Milan a Serie A.

    Mai tsaron ragar, wanda a baya ya ce yana son yin aikin horar da tamaula, ya buga wa tawagar Sifaniya wasa 36, yana cikin ƴan wasan da suka lashe kofin duniya a 2010 da kuma European Championship a 2008 da kuma 2012.

  19. Watakila Ajax ta bai wa Erik ten Hag aikin kociyanta

    Ten Hag

    Asalin hoton, Getty Images

    Watakila tsohon kociyan Manchester United, Erik ten Hag ya sake karɓar aikin horar da Ajax Amsterdam a baɗi.

    Ten Hag baya aiki tun bayan da United ta kore shi a cikin watan Oktoba, wanda ake sa ran zai maye gurbin Francesco Farioli, wanda ya yi ritaya ranar Litinin.

    Tsohon wanda ya horar da United ya je kallon wasan karshe na Ajax da FC Twente ranar Lahadi.

    Ajax ce ta yi nasarar cin 2-0, sai dai PSV Eindhoven ce ta lashe kofin bana ranar Lahadi da tazarar maki ɗaya da Ajax.

    Ten Ha, mai shekara 55 ya horar da Ajax daga 2018 zuwa 2022 da lashe kofi uku da kai ƙungiyar zagayen daf da karshe a Champions League a 2019.

  20. Wasa biyu da za a buga a Premier League ranar Talata, Premier League

    Palace

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a buga wasa biyu da suka rage a mako na 37 a Premier League ranar Talata.

    An samu kwantan wasannin ne, sakamakon karawar karshe a FA Cup da aka yi tsakanin Manchester City da Crystal Palace a Wembley ranar Asabar.

    Palace ce ta lashe kofin da cin 1-0, kuma karon farko a tarihinta da ta ɗauki wani babban kofi a fannin tamaula.

    City ta kammala kakar nan ba tare da ɗaukar kofi ba, amma tana neman gurbin Champions League, sannan za ta buga Club World Cup nan gaba a Amurka.

    • Manchester City da Bournemouth
    • Crystal Palace da Wolverhampton