Donald Trump zai yi kome a matsayin shugaban Amurka na 47

Wannan shafi na kawo muku rahotanni da bayanai kan zaɓen ƙasar Amurka da aka gudanar a ranar Talata 5 ga watan Nuwamban 2024.

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Mohammed, Usman Minjibir, Umar Mikail, Ibrahim Muhammad da Abdullahi Bello Diginza, Rabiatu Kabir Runka

  1. Jami'an tsaro na jiran ko-ta-kwana a Washington DC da wasu jihohi

    Amurka

    Asalin hoton, Reuters

    A birnin Washington DC, ƴankasuwa da dama sun rufe gilasan shagunansu da katakai domin ƙara kariya saboda fargabar aukuwar tarzoma a sanadiyar zaɓen.

    Haka kuma an jigbe ɗaruruwan jami'an tsaro a babban birnin ƙasar, da wasu jihohi irin su Alabama da Arizona da Delaware da Iowa da Illinois da North Carolina da New Mexico.

    Tun farkon watan Oktoba ne aka fara gina katangar ƙarfe a kusa da fadar gwamnati.

    Masu shaguna

    Asalin hoton, Reuters

  2. Democrats ta samu ƙuri'u a karon farko a New Hampshire

    Amurka

    Asalin hoton, Reuters

    Dazun mun kawo labarin cewa mutum shida sun kaɗa ƙuri'a a New Hampshire na Dixville Notch, inda wurin ne aka fitar da sakamakon zaɓen Amurka na farko a tsakar dare. Trump ya samu ƙuri'a uku, Kamala ta samu uku.

    Wakilin BBC ya zanta da wani wanda ya zaɓi Democrats a karon farko a yankin mai suna Les Otten, inda ya ce ya zaɓi Harris ne saboda ta san ƙokarin mutane, kuma ta yarda akwai rawar da mutane za su taka a gwamnatin.

    "Idan wanda aka zaɓa ya fahimta tare da aminta cewa dukkanmu muna da rawar da za mu taka a gwamnati, ai wannan ya fi muhimmanci."

  3. Hukumomin leƙen asirin Amurka sun zargi Rasha da yunƙurin haifar da tarzoma a zaɓen ƙasar

    A daidai lokacin da ake dakon fara ƙuri'a, shugaban hukumar tattara bayanan sirrin Amurka ya yi gargaɗin cewa wasu "ƙasashen waje" - ciki har da Rasha - na yunƙurin yin wasu "abubuwa da za ɓata nagartar zaɓen na Amurka, da jawo rabuwar kai a tsakanin ƴan Amurka."

    A wata sanarwa da ofishin darakta na hukumar tattara bayanan sirrin, da FBI da sauran hukuman leƙen asirin ƙasar, sun zargi ƙungiyoyi da suke da alaƙa da Rasha suna ƙoƙarin tayar da tarzoma da sake dawo da batun zargin maguɗin zaɓe.

    Hukumomin sun bayyana a sanarwar cewa, "wasu ƙungiyoyi masu alaƙa da Rasha sun wallafa wasu rubuce-rubuce cewa jami'an zaɓe a wasu manyan jihohi suna ƙoƙarin yin maguɗi. Sanarwar ta kuma zargi Iran da zama "wata barazana" ga zaɓen na Amurka.

    Tuni dai Rasha da Iran sun musanta waɗannan zarge-zarge.

  4. Taƙaitaccen tarihin Donald Trump

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton dake sama domin kallon bidiyon

    An haifi Trump a Queens da ke birnin New York a shekara 1946. Ya taso ne cikin kasuwancin gidaje da ya gada daga mahaifinsa Fred Trump.

    Bayan ya kammala makarantar soji, sai Trump ya shiga harkokin kasuwancin mahaifinsa, inda ya karɓi ragamar kasuwancin tare da faɗaɗa shi.

    Filayen wasan golf da manyan otel-otel da sauran wuraren nishaɗinsu suna nuna alamomin arziki da isa. Amma shi Trump burinsa ya wuce kasuwancin.

    A shekarar 2004, ya fara gabatar da shirin talabijin mai suna ‘The Apprentice’.

  5. Nawa ne albashin shugaban ƙasar Amurka?

    Joe Biden
    Bayanan hoto, Daga wannan kakar zaɓen za a ƙara albashin shugaban ƙasar Amurka

    Mutane kan yi tunanin cewa shugaban ƙasar Amurka na samun maƙudan kuɗaɗe a matsayin albashi da alawus-alawus.

    Babu kuskure a wannan tunanin saboda shugaban Amurka jagora ne na ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya girma, kuma mafiya ƙarfin iko a duniya.

    Amma fa ba haka abin yake ba kwatakwata.

    Dalili shi ne an tsara duk shugaban da ke mulkin Amurka zai zama ma'aikacin gwamnati ne, akan biya su albashi ne da harajin da sauran 'yan ƙasa ke biya.

    Shugaba Joe Biden da ke mulki a yanzu na karɓar dala 400,000 a shekara.

    Amma kuma ba shi ne kuɗin da sabon shugaba mai zuwa - Kamala ko Trump - zai karɓa ba.

    Wannan ba abin mamaki ba ne saboda an ɗauki tsawon lokaci ba a sauya albashin shugaban ƙasa ba.

    Idan Kamala Harris ta yi nasara, bayanai sun nuna cewa za a ƙara mata dala 235,100 kan albashinta na mataimakiyar shugaban ƙasa.

    Shekara huɗu da ya yi a kan mulki, Donald Trump bai karɓi albashin shugaban ƙasa ba. Maimakon haka, ya dinga karkatar da shi zuwa wasu ma'aikatun gwamnati duk wata uku.

    A cewar sakataren kula da ayyukan gwamnati, Trump ya ba da umarnin zuba kuɗin a fannin kula da harkokin lafiya da yaƙi da annobar cutar korona a 2020.

  6. Me ya sa jihohin Pennsylvania da Michigan suke da muhimmanci a zaɓen?

    Kamala Haris ta ƙarƙare yaƙin zaɓenta ne a Pennsylvania, shi kuma Trump a Michigan, amma me ya sa haka?

    A taƙaice, jihohi biyu ne a cikin jihohin bakwai da ake kira da raba gardama, waɗanda za su iya sauya sakamakon zaɓen.

    Pennsylvania wadda ke da wakilan zaɓe da ake kira electoral college guda 19 tana cikin jihohin da dukkan ƴan takarar suka yi ta zirya - kasancewar ita ce jiha wadda ta fi kowace jiha yawan wakilan zaɓe. Wannan ya sa lashe jihar zai taimaka wa ɗantakara ya samu nasara.

    A zaɓen 2020, Joe Biden wanda ɗan jihar ne, ya lashe jihar.

    Ita kuma jihar Michigan, tana da wakilan zaɓe 15, kuma jiha ce da ƴantakarar suke so, duk da cewa jiha ce da jam'iyyar Democrats ke yawan samun nasara a zaɓukan shugaban ƙasa.

    Sai dai Trump ya karya wannan lagon a zaɓen 2016, amma Biden ya sake karɓewa a zaɓen 2020.

  7. Wane ne mijin Kamala Harris?

    KAMALA HARRIS

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Kamala rungume da mijinta Doug Emhoff a wajen babban taron jam'iyyar Democratic na 2024 a Chicago

    A shekarar 2014, Harris lokacin tana sanata ne ta auri Doug Emhoff wanda lauya ne, inda ta ci gaba da riƙe yaransa biyu Cole and Ella.

    Ta rubuta wata maƙala a mujallar Elle a sherara 2019, inda a ciki ta bayyana yadda ta zama mai kula da ƴaƴan.

    "Da muka yi aure da Doug, sai ni da Cole da Ella muka amince cewa za su daina kirana da 'kishiyar uwa ba'. Sai suka fara kira na da 'Momala."

    An ga Cole da Ella da mahaifinsu duka a babban taron jam'iyyar democrats a 2024, inda aka riƙa kiran su da "iyalai masu zaman aminci."

    Ƙanwarta, Maya da ƴaruwarta, Meena ma duk sun zo babban taron.

    Nadia Brown, ƙaramar farfesan nazarin siyasa a jami'ar Purdue ta shaida wa BBC cewa Kamala Harris na bin sahun Fannie Lou Hamer da Ella Baker da Septima Clark ne da sauran su.

  8. Bidiyon yadda ake kiran sunan 'Kamala' - Kamar yadda ƴan uwanta suka bayyana

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton dake sama domin kallon bidiyon
  9. Wace ce Kamala Harris?

    Kamala Harris

    Asalin hoton, Kamala Harris

    Bayanan hoto, Kamala tana karama da ƙanwarta Maya tare da mahaifiyarsu

    An haifa Harris ne a Oakland a jihar California. Mahaifiyarta ƴar asalin India ce, mahaifinta kuma ɗan asalin Jamaica ne.

    Iyayenta sun rabu tana da shekara biyar, inda mahaifiyarta mai suna Shyamala Gopalan Harris ta ci gaba da kula da ita

    Ms Harris ta taso ne tana cuɗanya da al'adun India, kasancewar tana yawan bin mahaifiyarta zuwa ƙasar.

    "Mahaifiyata ta san cewa ƴaƴanta biyu mata ne kuma baƙaƙe. Ta san cewa ƙasar da take zaune za su riƙa kallon ƴaƴanta a matsayin baƙaƙen fata ne, wanda hakan ya sa ta ƙuduri aniyar ƙarfafa mana gwiwa."

    Amma rayuwarta a jami'ar Howard, wadda ɗaya ce daga cikin manyan makarantu da baƙaƙen fata suke karatu ya sauya rayuwarta, inda ita ma ta ce zuwanta jami'ar ya matuƙar sauya mata rayuwa da tunani.

  10. An kaɗa ƙuri'a da tsakar dare a New Hampshire

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mutum shida ne suka kaɗa ƙuri'a a ɗan ƙaramin garin

    A daidai lokacin da Trump ke ƙarƙare yaƙin zaɓensa ne kuma ake kaɗa ƙuri'a a wani yankin.

    An kaɗa ƙuri'ar ne a tsakar dare a wani ƙaramin gari mai suna New Hampshire da ke yankin Dixville Notch, inda su asali dama da tsakar dare suke yin zaɓensu.

    Mutum shida ne suka kaɗa ƙuri'ar, inda Kamala ta samu ƙuri'a uku, Trump ya samu uku.

    Sai dai za a ci gaba da kaɗa ƙuri'a a New Hampshire idan gari ya waye.

  11. Zaɓe ne na kankankan

    Har yanzu dai duk da ƙuri'un jin ra'ayoyi da aka yi da sauran hasashe-hasashe da aka riƙa yi game da zaɓen, har yanzu babu haƙiƙanin alƙaluman da za su nuna yadda zaɓen zai kaya.

    Wannan ya sa har yanzu babu wanda zai iya cewa ga ɗantakarar da zai lashe zaɓen na yau.

    Sai dai idan zaɓe ya yi nisa, za a iya samun yin hasashen, musamman ganin jihohi masu raba gardama za su tara wa ɗantakara ɗaya, musamman saboda an san yadda suka saba.

  12. Trump ya caccaki Harris a jawabinsa na ƙarƙare yaƙin zaɓe

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shi ma Donald Trump ya ƙarƙare nasa yaƙin zaɓen a jihar Michigan, inda magoya bayansa suka ɗauki kusan sa'a biyu ana jiransa.

    Sai dai ba kamar Kamala Haris ba, wadda ta ƙarƙare yaƙin zaɓen nata ba tare da ta ambaci sunansa, shi Trump sai da ya caccake ta, tare da kiranta da "mara hankali"

    Ya bayyana wa magoya bayansa cewa zai lashe zaɓen na yau, inda ya ce, "wannan ranar ce za ta zama ranar nasara mafi girma a tarihin siyasar ƙasarmu."

  13. Harris ta ƙarƙare yaƙin zaɓe da kira na musamman ga matasa

    Kamala

    Asalin hoton, Reuters

    Kamala Haris ta ƙarƙare yaƙin zaɓenta a jihar Philadelphia, bayan makonni tana fafutikar jawo hankalin masu kaɗa ƙuri'a kan su zaɓe ta.

    Ta ce tana "tare da mutane da dama daga kowane lungu da saƙo na ƙasar."

    Ta ƙara da cewa, "mu muna fafutika ne domin wasu abubuwa, ba wai fafutikar banza ba. Yau mun kammala yaƙin zaɓenmu cikin ƙarfin gwiwa da fatan nasara."

    Sai ta yi kira ta musamman zuwa ga matasa masu zaɓe, inda ta ce, "zuwa ga matasa, na san abin da za ku iya yi, kuma in alfahari da ku."

    Kamala ta yi kiran ne kasancewar ta san tana matuƙar buƙatar ƙuri'un matasan domin lashe zaɓen.

  14. Yau take zaɓe a ƙasar Amurka

    Jama'a assalamu alaikum, barkanmu da wannan safiyar taTalata daga nan sashen Hausa na BBC. A yau ne Amurka za su kaɗa ƙuri'a domin zaɓen shugaban ƙasar, wanda zai maye gurbin Joe Biden.

    Ku kasance tare da mu a wannan shafin, inda za mu riƙa kawo muku labaran wainar da ake toyawa a zaɓen mai zafi tsakanin Donald Trump da Kamala Haris.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin kallon wasu hotunan da bidiyo.