Akwai yiwuwar Trump ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Bisa ga dukkan alamu, Donald Trump ya riga ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Amurka, inda ya yi kome a fadar shugaban ƙasar, bayan Joe Biden ya kayar kayar da shi shekara huɗu da suka gabata, kamar yadda wakilin BBC, Anthony Zurcher ya bayyana a sharhinsa.
Tun tuni Trump ya yi wa magoya bayansa jawabi, inda a ciki ya bayyana cewa ya samu gagarumar nasara a zaɓen.
Trump ya fi mayar da akalar yaƙin zaɓensa ne kan farfaɗo da tattalin arziki da yaƙi da kwararowar baƙin haure.

















