Amsar tambayoyi 10 da ya kamata ku sani kan zaɓen Amurka

a
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Amurkawa na shirin fita rumfunan zaɓe domin zaɓar mutumin da suke fatan ya zama shugaban ƙasar na gaba.

Yaƙin neman zaɓen 'yan takara ya haifar da zazzafar muhawara a shafukan intanet kan abubuwa da dama kama daga amfani da hanyoyin zamani kan sauya kalaman Kamala Harris zuwa labaran ƙarairayi kan yuƙurin kisan Donald Trump.

Shafuka sada zumunta sun yi matuƙar tsii a yaƙin neman zaɓen, yayin da shafin TikTok ya ce a makon da aka harbi Donald Trump, adadin saƙonnin da aka wallafa a kansa a shafin sun ƙaru da kashi kusan 800, yayin da kallon bidiyo a shafin ya tashi daga miliyan guda zuwa biliyan shida.

Baya ga kanun labarai a shafukan intanet, mutane kan yi amfani da shafukan sada zumunta domin fahimtar haƙiƙanin yadda tsarin siyasar Amurka yake gudana. La'akari da haka ga wasu tambayoyi da aka fi yawan neman amsoshinsu game da zaɓen.

Yaushe ake gudanar da zaɓe Amurka?

A ranar 5 ga watan Nuwamba ne za a gudanar da zaben shugaban ƙasar Amurka. Akan gudanar da zaɓen ne duk bayan shekara huɗu, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.

Kundin tsarin mulki - wanda shi ne ya tanadi duka dokokin ƙasar - ya tanadi cewa wa'adin shugabancin ƙasar ya taƙaita wa shugaban ƙasar wa'adin mulki biyu na shekara hurhuɗu.

Kafin yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima a 1951, shugaban ƙasa a Amurka ba shi da wani wa'adi, yana da damar da zai yi ta tsayawa takara muddin ana zaɓarsa.

Su wane ne 'yan takarar shugabancin ƙasar?

Tsohon shugaban ƙasar Donald Trump, wanda a watan Janairun 2017, aka rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasar na 45, shi ke fafatawa da mataimakiyar shugaban ƙasar Kamala Harris.

Kamala Harris ce jam'iyyar Dimokrats ta tsayar takarar bayan da a cikin watan Yuli shugaban ƙasar na yanzu Joe Biden ya bayyana cewa ba zai yi takara ba.

Waɗanne ne manyan jam'iyyun siyasar Amurka?

Manyan jam'iyyun siyasar Amurka su ne Democrats, wadda Kamala Harris ke takara a ƙarƙashinta, sai kuma jam'iyyar Republican, da Donald Trump ke takara a ƙarƙashinta.

A zaɓen Amurka, 'yan takarar shugaban ƙasa kan yi kokawar neman magoya baya a yankunan ƙasar daban-daban da ƙungiyoyi, kuma kowace jam'iyya na ƙunshe da ruunin mutane daban-daban.

Yaya jam'iyyun ke zaɓar 'yan takararsu?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Duka jam'iyyun biyu, kan tsayar da 'yan takara ta hanyar gudanar da zaɓukan fitar da gwani daga manyan wakilan jam'iyyar, inda a nan ne jam'iyyun ke fitar da wanda zai yi musu takarar shugaban ƙasa.

Zaɓukar fitar da gwani, zaɓe ne da jam'iyyun siyasa ke zaɓar mutanen da za su yi musu takarar shugabancin ƙasa, kuma akan gudanar da irin waɗanann zaɓuka a jihohi watanni shida zuwa tara kafin babban zaɓen. Masu zaɓen kan zaɓi mutanen da suke so ta hanyar kaɗa ƙuri'a.

A jihohi da dama akan gudanar da zaɓen fitar da gwanin, waɗanda taruka ne inda 'yan takarar shugaban ƙasa kan halarci wuraren tarukan domin bayyana manyan ƙudurorinsu . Bayan haka sai mambobin jam'iyyar su zaɓi mutumin da suka fi nustuwa da ƙudurorinsa.

Bayan da Joe Biden ya bayyana haƙura da takara a watan Yuli, sai ya goyi bayan mataimakiyarsa, Kamal Harris. Ba a samu mutanen da suka ƙalubalance ta ba, don haka cikin sauƙi ta tara magoya baya a cikin jam'iyyar, inda kuma aka amince da ita a matsayin 'yar takara.

Ta yaya ake zaɓar shugaban ƙasa a Amurka?

Manyan 'yan takarar biyu kan yi gogayya domin lashe zaɓen a jihohin ƙasar 50 da Washington, babban birnin ƙasar.

Akwai wasu ƙuri'un wakilan masu zaɓe 530 a faɗin ƙasar, kuma duk wanda zai yi nasara a zaɓen dole ne ya samu ƙuri'un wakilan masu zaɓen aƙalla 270 zuwa sama.

Wane ne ke da damar kaɗa ƙuri'a a zaɓen Amurka?

Mafi yawan Amurkawa masu shekara 18 zuwa sama na da damar kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasar.

Haka su ma Amurkawan da ke zaune a ƙasashen waje za su iya yin rajistar zaɓen, sannan su buƙaci a ba su damar kaɗa ƙuri'a a ƙasashen da sauke zaune.

Yaushe za mu san sakamakon zaɓen Amurka?

Galibi akan sanar da wanda ya yi nasara a cikin daren da aka kammala zaɓen, amma a zaɓen 2020 an ɗauki kwanaki ana ƙirga ƙuri'un.

Idan aka samu sauyin shugaba, to lokacin da ya biyo bayan zaɓen ana kiransa da lokacin shirin miƙa mulki.

Hakan na bai wa sabuwar gwamnati damar naɗa manyan sakatarori tare da gudanar da shirin kafa sabuwar gwamnati.

Yaushe ake rantsar da sabon shugaban ƙasa a hukumance?

Ana rantsar da sabon shugaban ƙasa a watan Janairu a wani ƙasaitaccen biki da ake gudanarwa a harabar majalisar dokokin ƙasar da ke birnin Washington DC.

Yaushe za a gudanar zaɓen Amurka na gaba?

Wanda ya lashe zaɓen zai yi shekara huɗu a fadar gwamntin ƙasar da ake kira 'White House', don haka zaɓen shugaban ƙasar na gaba zai gudana cikin watan Nuwamban 2028.

Wane ne shugaban Amurka na farko?

George Washington ne mutum na farko da aka fara zaɓa a matsayin shugaban Amurka a shekarar 1789.