Zaɓen Amurka: Zuwa yaushe za mu san wanda ya yi nasara tsakanin Harris da Trump?

Hoton fadar White House da tutar Amurka
    • Marubuci, Sam Cabral
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Washington
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Amurka na kaɗa ƙuri'ar zaɓen shugaban ƙasarsu na gaba wanda za a kammala ranar Talata 5 ga watan Nuwamba.

Da zarar an kammala kaɗa ƙuri'a, ya danganta ga yadda fafatawar ta kasance, zai iya kasancewa ba za iya sanin wanda ya kama hanyar nasara ba tsawon sa'o'i ko kwanaki ko ma makonni. Ga abin da ya kamata ku sani.

Yaushe ake sa ran bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasar na 2024?

Mataimakiyar shugaban Amurka ta yanzu kuma 'yar takarar jam'iyyar Democrat Kamala Harris, da kuma tsohon shugaban ƙasar kuma ɗan takarar jam'iyyar Republican Donald Trump, na ta kan-kan-kan a farin jini wajen masu zaɓe tsawon makonni.

Bambancin da za a samu na nasara a wasu wuraren da dama zai kasance ba shi da yawa, wanda hakan zai buƙaci a sake ƙirga ƙuri'u.

Haka kuma akwai yuwuwar sakamakon zai kasance yana zuwa a hankali ba cikin sauri ba a wannan shekarar saboda sauyin da aka samu a wasu jihohin kan yadda suke zaɓen.

Ta ɗaya ɓangaren kuma an samu cigaba wajen ƙirga ƙuri'u a jihohi kamar Michigan, kuma a wannan karon ƙuri'un da za a jefa ta wasiƙa kaɗan ne ba kamar lokacin annobar Korona ba.

Wannan na nufin kenan akwai yuwuwar bayyana wanda ya yi nasara a daren da aka kammala zaɓe, ko da safe ko bayan 'yan kwanaki ko kuma makonni.

Yaushe muka samu sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2020?

An yi zaɓen 2020 ne ranar Talata 3 ga watan Nuwamba, to amma tashoshin talabijin na Amurka ba su bayyana Biden a matsayin wanda ya yi nasara ba har sai ranar 7 ga watan Nuwamba.

A daren da aka kammala kaɗa ƙuri'a, magoya bayan Trump suna cike da ƙwarin gwiwa cewa gwaninsu ne zai yi nasara. Hasali ma dai dukkanin 'yan takarar na cike da ƙwarin gwiwa domin kowanne yana dab da samun ƙuri'u 270 na wakilan masu zaɓe da ake buƙata kafin mutum ya yi nasarar zama shugaban Amurka.

Duk da cewa jihohi da dama sun kammala zaɓen da bayyana sakamakon cikin sa'a 24 wasu jihohin mafiya muhimmanci 'yan kaɗan da suka haɗa da Pennsylvania da Nevada ba su bayyana ba.

Pennsylvania, wadda take da ƙuri'ar wakilan masu zaɓe 19 ta fara karkata ga jam'iyyar Democrat. To amma a ranar Asabar da safe wasu ƙuri'u da aka sake ƙirgawa a jihar sun bai wa kafofin yaɗa labarai, (CNN, ce ta farko) ƙwarin gwiwar cewa Biden ne zai iya nasara a can.

Ma'akaciyar zaɓe a Georgia a 2020

Asalin hoton, Getty Images

Da yaushe aka saba bayyana sakamakon zaɓe?

Bisa al'ada jama'a sun saɓa tafiya bacci a daren da aka kammala kaɗa ƙuri'a da hasashen wanda zai zama sabon shugaban ƙasar ko kuma aƙalla idan gari ya waye.

Misali a 2016, lokacin da Trump ya ci zaɓe, an bayyana shi ne da ƙarfe 03:00 (08:00 GMT) na dare, kwana ɗaya bayan ranar zaɓe.

A 2012 lokacin da Barack Obama ya ci zaɓe na biyu, an yi hasashen nasarar tasa tun kafin ƙarfe 12 na dare a ranar zaɓe.

To amma zaɓen da ya bambanta da si ne na 2000 tsakanin George W Bush da Al Gore.

An yi ta gwagwagwa a tsakanin ɓangarorin ƴantakarar biyu a kan sakamakon Florida, inda sai a ranar 12 ga watan Disamba Kotun Ƙolin Amurka ta kawo ƙarshen dambarwar, ta sa aka kawo ƙarshen sake ƙirag ƙuri'ar jihar, inda ta tabbatar da Bush a matsayin wanda ya yi nasara.

Waɗanne muhimman jihohi ne za a sa ido a kansu?

A faɗin ƙasar za a kammala kaɗa ƙuri'a da ƙarfe 6:00 EST (2200 GMT) ranar Talata da yamma, sannan za a dakatar da zaɓen ƙuri'a ta ƙarshe da ƙarfe 1:00 EST na dare (0500 GMT) kafin wayewar garin Laraba.

Amma a ƙarshe ana sa ran sakamakon zaɓen jihohi bakwai na raba-gardama wato Arizona, da Georgia, da Michigan, da Nevada, da North Carolina, da Pennsylvania da kuma Wisconsin.

Yaya ake ƙirga ƙuri'un?

A bisa al'ada ana fara ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa ne a ranar zaɓe sai kuma waɗanda aka yi na zaɓen wuri sannan na zaɓen da aka yi ta wasiƙa.

Masu biy bayan waɗannan kuma a ƙirgin su ne waɗanda aka ƙalubalanta sai na ƙasashen waje sai kuma a arshe na sojoji.

Jami'an jiha ne wani lokaci waɗanda aka naɗa wani lokacin kuma waɗanda aka zaɓa suke yi aikin ƙirgen ƙuri'un ɗaiɗai-da-ɗaiɗai.

Duk ƙuri'ra da aka ƙirga ana kuma ɗaukar hotonta inda na'ura za ta irga ta.

Akwai kuma matakan da ake bi wajen tantance ƙuri'u masu kyau da waɗanda suka ɓaci.

Wasu tarin ƙuri'u kenan da ake taƙaddama a kansu, inda za a tantance su a California

Asalin hoton, Getty Images

Me zai iya jinkirta sakamakon zaɓen shugaban ƙasar?

Idan sakamakon ya kasance kusa da kusa wannan zai sa kafofin yaɗa labarai su jinkirta hasashen wanda suke ganin zai yi nasara, to amma kuma zai sa su bijiro da batun sake ƙirge da kuma batutuwa na shari'a.

A jihar Pennsylvania, misali za a sake ƙirga ƙuri'u ne gaba ɗaya idan aka samu bambancin rabi cikin ɗari a tsakanin wanda ya yi nasara da wanda aka kayar.

A 2020, bambancin shi ne sama da maki 1.1 bisa ɗari.

Yanzu ma dai tuni 'yan jam'iyyar Republican sun riga sun shigar da ƙararraki sama da ɗari na zaɓen a faɗin ƙasar, waɗanda suka hada da cancantar mai zaɓe da sauransu.

Me zai faru idan aka ƙalubalanci sakamakon zaɓen?

Da zarar an ƙirga kowace ƙuri'a aka sanya ta a cikin sakamako na ƙarshe, bayan bin duk wasu matakai na tantancewa - wannan sakamako ya tabbata kenan - farko a yankin sannan kuma a matakin jiha.

Daga nan gwamnan jiha zai sanya hannu a kan wata takarda ta jerin sunayen waɗanda za su wakilci jihar a ƙuri'ar wakilan masu zaɓe.

Waɗannan masu zaɓe su ne za su haɗu a jihohinsu ranar 17 ga watan Disamba su jefa ƙuri'arsu sannan su aika Washington.

Ranar 6 ga watan Janairu sabuwar majalisar dokoki - ta dattawa da ta wakilai- za ta yi taron haɗin gwiwa bisa shugabancin wanda ke mataimakin shugaban ƙasa mai ci ( a wannan karon Kamala Harris kenan) ta ƙirga ƙuri'ar wakilan masu zaɓe.

A 2020 Trump ya ƙi yarda da shan kaye kuma ya angiza magoya bayansa suka kai farmaki suka mamaye majalisar, lokacin da majalisar ke taro domin tabbatar da nasarar Biden.

Magoya bayan Trump da suka taru a 2020

Asalin hoton, Getty Images

Trump ya yi kira ga mataimakinsa a lokacin, Mike Pence, da ya yi watsi da sakamakon to amma Pence ya ƙi.

Har bayan tarzomar ta mamaye ginin majalisa, bayan da 'yan majalisar suka sake taruwa domin tabbatar da nasarar ta Biden 'yan Republican 147 sun kaɗa kuri'ar sauya wannan sakamako to amma ba su yi nasara ba.

Tun daga wannan lokaci sauye-sauyen dokokin zaɓe da aka yi a Amurkar, sun sa da wuya 'yan majalisar dokoki su ƙi amincewa da tabbataccen sakamakon da aka aika musu daga jiha. Haka kuma an zartar cewamataimakin shugaban ƙasa ba shi da iko shi kaɗai ya ƙi amincewa da ƙuri'ar wakilan masu zaɓe.

To sai dai duk da waɗannan matakai ana hasashen samun jinkirin tabbatar da sakamakon zaɓen na 2024, a yankuna da kuma jihohi.

Tuni daman Trump da mataimakinsa JD Vance da manyan 'yan majalisar dokoki na ƙasar 'yan Republican suke ta nuna cewa ba za su amince da sakamakon ba idan Trump ya faɗi.

Yaushe za a rantsar da shugaban ƙasa?

Za a rantsar da sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ne a ranar Litinin 20 ga watan Janairu 2025 a harabar ginin majalisar dokoki.

Taron zai kasance na 60 na ƙaddamar da shugaban ƙasa a tarihin Amurka.