Mutane kan yi tunanin cewa shugaban ƙasar Amurka na samun maƙudan kuɗaɗe a matsayin albashi da alawus-alawus.
Babu kuskure a wannan tunanin saboda shugaban Amurka jagora ne na ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya girma, kuma mafiya ƙarfin iko a duniya.
Amma fa ba haka abin yake ba kwatakwata.
Dalili shi ne an tsara duk shugaban da ke mulkin Amurka zai zama ma'aikacin gwamnati ne, akan biya su albashi ne da harajin da sauran 'yan ƙasa ke biya.
Shugaba Joe Biden da ke mulki a yanzu na karɓar dala 400,000 a shekara.
Amma kuma ba shi ne kuɗin da sabon shugaba mai zuwa - Kamala ko Trump - zai karɓa ba.
Wannan ba abin mamaki ba ne saboda an ɗauki tsawon lokaci ba a sauya albashin shugaban ƙasa ba.
Idan Kamala Harris ta yi nasara, bayanai sun nuna cewa za a ƙara mata dala 235,100 kan albashinta na mataimakiyar shugaban ƙasa.
Shekara huɗu da ya yi a kan mulki, Donald Trump bai karɓi albashin shugaban ƙasa ba. Maimakon haka, ya dinga karkatar da shi zuwa wasu ma'aikatun gwamnati duk wata uku.
A cewar sakataren kula da ayyukan gwamnati, Trump ya ba da umarnin zuba kuɗin a fannin kula da harkokin lafiya da yaƙi da annobar cutar korona a 2020.