Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaɓen Amurka: Ra'ayoyin ƴan Afirka kan zaɓen
Zaɓen Amurka: Ra'ayoyin ƴan Afirka kan zaɓen
An wallafa
Adaidai lokacin da ƴan sa'o'i suka rage a kammala yaƙin neman zaɓe a Amurka, wasu daga cikin mazauna ƙasar wadanda ƴan Afirka ne sun bayyana wa BBC ra'ayinsu kan zaɓen.
A ranar Talata ne dai ta 5 ga watan Nuwamba miliyoyin Amurkawan za su fita rumfunan zaɓe domin kaɗa ƙuri'arsu.
Duk da cewa akwai wasu ƴantakara na daban, amman takarar ta fi zafi tsakanin, Donald Trump tsohon shugaban ƙasar da kuma Kamala Harris, mataimakiyar shugaba Biden na Amurka.