Yadda Amurkawa ke kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa
Yayin da ake gab da kammala kaɗa ƙuri’u a zaɓen shugaban ƙasar Amurka, wakilinmu Haruna Ibrahim Kakangi zai nuna muku yadda Amurkawa ke jefa ƙuri’un nasu dalla-dalla a birnin Minneapolis.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku rahotanni da bayanai kan zaɓen ƙasar Amurka da aka gudanar a ranar Talata 5 ga watan Nuwamban 2024.
Isiyaku Mohammed, Usman Minjibir, Umar Mikail, Ibrahim Muhammad da Abdullahi Bello Diginza, Rabiatu Kabir Runka
Yayin da ake gab da kammala kaɗa ƙuri’u a zaɓen shugaban ƙasar Amurka, wakilinmu Haruna Ibrahim Kakangi zai nuna muku yadda Amurkawa ke jefa ƙuri’un nasu dalla-dalla a birnin Minneapolis.
An rufe rumfunan farko a zaɓen shugaban ƙasar Amurka a jihohin Indiana da Kentucky.
Za mu kawo muku ƙarin bayani kan duka sakamakon da muka samu.
Ku ci gaba da kasancewa da mu a wannan shafi...
Yayin da cigaban dimokraɗiyya da tattalin arziki ke kan gaba a batutuwan da masu zaɓe ke la'akari da shi, ƙuri'ar jin ra'ayi ta nuna yadda magoya bayan manyan 'yan takarar suka karkata.
Daga cikin waɗanda suka zaɓi Kamala Harris:
Daga cikin waɗanda suka zaɓi Donald Trump:
Kafofin yaɗa labaran Amurka sun ambato babban sakataren jihar Nevada na bayyana damuwarsa kan yawan ƙuri'un da aka ƙi amincewa da su saboda rashin daidaiton sa-hannun masu zaɓe a gundumomin Clark da Washoe.
Akan kwatanta sa-hannun da ke kan ƙuri'un da aka kaɗa ta Email da sa-hannun da ke kan rajistar masu zaɓe.
Duk ƙuri'ar da aka samu saɓanin sa-hannun da ke kanta da wanda ke kan rajistar masu zaɓe to tana buƙatar ''keɓe'' ta domin sake tantanceta da wanda ya kaɗa ta..
Jaridar New York Times ta ruwaito cewa fiye da ƙuri'u 11,300 aka gano suna da wanna matsala, waɗanda kuma suke buƙatar ƙarin tantancewa a gundumar Clark, yayin da aka samu fiye da ƙuri'a 1,800 a gundumar Washoe.
Kafar yaɗa labarai ta CNN ta ruwaito babban sakataren jihar, Francisco Aguilar, na aika saƙonnin waya ga mutanen da suka kaɗa ƙuri'a da ake buƙatar a sake tantance sa-hannunsu kafin a ƙidaya ƙuri'un nasu.
Duka kafofin yaɗa labaran sun ce an samu matsalar rashin daidaito a galibin ƙuri'un matasan masu zaɓe.
'Yar takarar Sanatan Republican ta jihar Arizona, da a baya ta sha watsi da sakamakon zaɓe, a yanzu ta ce za ta amince da sakamakon zaɓen.
Yayin da take jawabi ga manema labarai, Kari Lake ta ce tana da 'damuwa' amma an yi abin da ya dace domin magance matsalolin.
Lake ta jima tana goyon bayan Ikirarin Donald Trump maras hujja cewa bai faɗin zaɓen 2020 ba.
Haka kuma ba ta amince da sakamakon tsakiyar wa'adi, a lokacin da ta yi rashin nasara a takarar gwamnan jihar a hannun Katie Hobbs ta Dimokrats.
Yayin da ake jiran ƙarin bayani daga rundunar 'yansanda kan kama wani mutum da ke warin man fetur ɗauke da wata babbar bindigar harba hayaƙi a kusa da wani gini.
Haka kuma 'yansandan sun kama wasu mutane a faɗin ƙasar da ake zargi da aikata wasu laifuka masu alaƙa da karya dokokin zaɓe a wannan rana da ake kaɗa ƙuri'a.
Ga wasu bayanai game da kamen da ka yi a yau.
An tsawaita lokacin zabe da mintuna 90 a gundumar Luzerne da ke jihar Pennsylvania, sakamakon jinkirin da aka samu wajen buɗe rumfunan zaɓe a gundumar, kamar yadda wani jami'in zaɓen ya bayyana
A yanzu za a rufe rumfar zaɓen Laflin Borough zuwa ƙarfe 9:30 na dare agogon ƙasar, wato ƙarfe 2:30 agogon GMT.
Tun da farko an tsawaita zaɓe a gudumar Cobb da ke jihar Georgia, sakamakon jinƙirin buɗe rumfuna a gundumar.
Za dai a rufe rumfunan zaɓen a bambantan lokuta a faɗin Amurka, inda za a fara rufe rumfar zaɓe da misalin ƙarfe 11:00 na dare, sannan a rufe rumfunan ƙarfe da ƙarfe 06:00 na safiyar Laraba agogon na GMT.
Rundunar ƴan sandan majalisar dokokin Amurka ta ce ta kama wani mutum da bindiga harba hayaƙi a cibiyar saukar baƙi ta ginin majalisar da ke birnin Washington DC.
A wani sako da ta wallafa a shafinta na X, rundunar ta ce jami'anta sun tsaida da mutumin ne a lokacin da ake aikin tantance shi a cibiyar. "Mutumin yana warin man fetur, kuma yana ɗauke da bindigar harba hayaƙi," in ji sakon.
Sanarwar ta ƙara da cewa an rufe cibiyar ga masu rangadi a yau yayin da 'ƴan sanda ke gudanar da bincike.
Rundunar ƴan sandan ta ce za ta bayar da ƙarin bayani idan ta samu.
A zaɓen shugaban ƙasa, jihohi da dama sukan zaɓi jam'iyya ɗaya ce a kowane zaɓe.
Wannan ya bar wasu tsirarun jihohi - waɗanda aka sani da "marasa tabbas" - inda kowane ɗan takara zai iya yin nasara.
Uku daga cikin jihohi bakwai a wannan zaɓen sun kasance a wani yanki da ake kira 'Rust Belt', tsohuwar cibiyar masana'antar ƙere-ƙere ta Amurka.
Pennsylvania da Michigan da Wisconsin suna da kamanceceniya a yanayin masu jefa ƙuri'ar da ke jihohinsu kuma dukansu sun zaɓi jam'iyya ɗaya ne tun 1992.
Idan suka yi zaɓe kaman yadda ake hasashe, Kamala Harris sai ta nemi cikon ƙuri'un wakilan masu zaɓe 44 kafin ta kai adadin 270 da ta ke buƙata, yayin da shi kuma Trump zai nemi cikin ƙuri'u 51 kafin ya sami adadin 270 da yake buƙata.
Ana ta tafka ruwan sama tun da sanyin safiyar yau a yammacin jihar North Carolina, amma masu kaɗa ƙuri'a na ci gaba da fitowa rumfunan zaɓe.
An kafa tantuna da ake amfani da su don maye gurbin rumfunan zaɓen da suka lalace a gundumar Burke, kuma darektan zaɓen ya shaida wa BBC cewa mutane na ta kwararowa fiye da yadda ake tsammani.
"Mun samu mutum 94 da suka kaɗa ƙuri'a kawo yanzu," in ji Richard Coleman.
Adadin ba mai girma ba ne duba da cewa an shafe sa'o'i shida da buɗe rumfunan zaɓe, amma yankin karkara ce kuma da yawan masu kaɗa ƙuri'a a yankin sun riga sun kaɗa ƙuri'unsu kafin ranar zaɓe.
Alama ce mai kyau ga ƴan Republican. Wannan yanki da gundumar Burke sun cika da magoya bayan Trump wanda zai buƙaci mutane su fito da yawa domin su zaɓe shi.
Mun dai ji ta bakin abokin takarar Kamala Harris Tim Walz, wanda ke ganawa da masu kaɗa ƙuri’a a Pennsylvania.
Da yake magana da manema labarai kafin ya hau jirgi zuwa Washington DC, ya ce "muna jin daɗin yadda abubuwa ke gudana".
Gwamnan na jihar Minnesota ya ci gaba da dagewa kan cewa yaƙin neman zaɓe ta hanyar nuna bambanci tsakanin yakin neman zaɓen Harris - wanda ya ce ya samo asali ne bisa haɗin kai - da sakon Trump wanda ya ce babu abin da yake tallatawa illa rarraba kawunan jama'a.
Ya ba da tabbacin cewa yana da kwarin gwiwa kan tasirin tsarin dimokuradiya, yana mai cewa Amurka na gudanar da zaɓuka masu inganci da aminci.
Ya ƙara da cewa yana iya ɗaukar ɗan lokaci kafin a samu sakamako.
Walz ya yi zagaye na ƙarshe na hirarrakin gidajen rediyo da safiyar yau.
Ya zaburar da masu sauraro a Detroit da Milwaukee da North Carolina da Atlanta da Philadelphia don su fito rumfunan zaɓe kuma su zaɓi Harris.
Miliyoyin mutane ne ke kaɗa kuri'unsu a rumfunan zabe a faɗin Amurka a yau Talata.
Sai dai ba za a bayyana sakamakon zaɓen da zai tabbatar da wanda zai zama shugaban ƙasa a hukumance ba har sai an ƙirga ƙuri'un tare da tantance duka ƙuri'un da aka kaɗa, wanda ka iya ɗaukar kwanaki kafin a kai ga kammalawa.
Za a fara rufe rumfunan zaɓe da misalin ƙarfe 18:00 EST (23:00 agogon GMT) a wasu ƙananan hukumomi a ranar Talata, amma za a ci gaba da ƙidayar kuri'un na tsawon sa'o'i da dama bayan haka a yawancin jihohin ƙasar.
Misali, a cikin jihohi masu muhimmanci - Pennsylvania da Wisconsin - ma'aikatan zaɓe ba a yarda su fara taɓa kuri'un da aka aiko ta gidan waya ba sai ranar zaɓe.
Yana da mahimmanci a lura da cewa kafafen yaɗa labarai na amfani da sakamakon da ba na hukuma ba lokacin da suke sanar da waɗanda suka yi nasara a daren zaɓe, maimakon jiran ƙidayar ƙarshe.
Wasu gundumomi suna zira takardar zaɓen na cikin na'urorin ɗaukar hoto wanɗanda ke tattarawa su kuma tantance kafin kuma a sake ƙirga su da hannu har sau biyu kafin a sanar.
An umarci jihohin Texas da Missouri da su ƙyale masu sa ido kan zaɓe daga ma'aikatar shari'a (DOJ) su sanya ido a rumfunan zaɓen bayan da alƙalai suka ƙi amincewa da yunƙurin da suka yi na hana jami'an shiga rumfunan zaɓen.
Don sanya ido kan bin ƙa'idojin zaɓe, DOJ ta sanar da cewa za ta tura lauyoyi don duba rumfunan zaɓe a yankuna 86 na jihohi 27, ciki har da wasu a Texas da Missouri.
Al'ada ce ta DOJ ta tura ma'aikata don sanya ido a wuraren zaɓe a lokacin zaɓukan ƙasa.
Texas da Missouri sun nemi daƙile wannan lamari a wasu ƙararraki daban-daban da suka shigar, amma kotuna guda biyu sun yi watsi da ƙararrakin.
Jami’an hukumar binciken manyan laifuka ta FBI sun kama wasu mutum biyu a jihar Michigan da laifin yin barazana ga gudanar da zaɓe, kamar yadda The Detroit News ta ruwaito.
Wata kafar yaɗa labarai da ke Michigan ta ce wani mutum da ake zargi yana da alaƙa da wani yunƙurin kisa kan Donald Trump.
Mutumin, Isaac Sissel, da ake zargin ya buga a shafinsa na Reddit da sunan mai amfani da "ShootUpTrumpRally" kuma tun a lokacin ya shaida wa masu binciken cewa ya yi imanin "komai zai yi kyau idan Trump ya mutu".
A wani ɓangaren kuma, ana zargin Christopher Clay Pierce mai shekaru 46 na Jackson da yin barazana ga wani kwamitin siyasa da ba a tabbatar da sunansa ba mai alaƙa da jam'iyyar Democrat cikin shekaru biyu da suka gabata.
Sakataren harkokin wajen Geogia Brad Raffensperger ya ce barazanar bam da aka yi a rumfunan zaɓe da dama a safiyar yau ba na ƙwarai ba ne.
Da yake magana a wani taron manema labarai, Raffensperger ya ce barazanar ta samo asali ne daga kasar Rasha.
"Muna kama su a kowane lokaci," in ji shi - kuma ya ce "manufarsu" ita ce ƙoƙarin "hargitsa Amurka".
Tun da farko, mun ba da rahoton cewa an yi barazana daban-daban biyar a wuraren kaɗa ƙuri'a a gundumar Fulton. An kwashe mutane daga rumfuna biyu, amma duk an sake buɗe su kuma ana ci gaba da kaɗa ƙuri'a.
Ofishin babban mai shigar da ƙara na gundumar Philadelphia ya ƙaddamar da wani kwamiti da ya ƙunshi lauyoyi kusan 60 domin gudanar da bincike kan duk wani korafi game da tsarin zaɓe a cikin birnin.
A wani takaitaccen taron manema labarai da jami'ai suka yi sun ce kawo yanzu rundunar ta samu rahotanni da dama, musamman kan mutanen da suka hana shiga wuraren zaɓe da gangan.
Babban mai shigar da ƙara na gundumar, Larry Krasner, ya ce halin da ake ciki ƴan matsalolin da aka samu sun ɗan fi na zaɓukan baya, kodayake ya zuwa yanzu an warware matsalolin ba tare da wani tashin hankali ba.
Jami'ai na kuma binciken shafukan sada zumunta waɗanda ke nuna mu'amala da ma'aikata a rumfunan zaɓe wanda hakan na iya keta dokokin zaɓe.
Krasner ya ce hukumomi a shirye suke domin tunkarar duk wani yunƙurin kawo barazana ga yadda ake gudanar da zaɓe a gundumar.
An samu barazanar bam har biyar amma na ƙarya a wuraren kaɗa ƙuri'a a gundumar Fulton da ke jihar Georgia a safiyar yau.
Nadine Williams, shugabar sashen rajista da zabe na gundumar, ta ce barazanar ta kai ga kwashe mutane na wucin gadi a wasu wurare biyu na kusan mintuna 30.
A halin yanzu mahukunta a yankin, wanda ya haɗa da birnin Atlanta, suna aiki don samun umarnin kotu domin tsawaita lokacin zaɓe a wuraren biyu da abin ya shafa har zuwa karfe 00:30 GMT.
Mun ruwaito a baya cewa tangarɗar na'ura a gundumar Cambria ta jihar Pennsylvania ta hana wasu masu kaɗa ƙuri’a tantance kuri’unsu, kuma jami’an zaɓe a jihar sun miƙa buƙatar tsawaita lokacin kaɗa ƙuri’a.
Donald Trump yana magana da manema labarai a Palm Beach, Florida, yayin da yake kaɗa ƙuri'a a zaɓen tare da matarsa, Melania.
Sanye da jar hular sa, yana magana da manema labarai yanzu, inda ya ce "Ina da ƙwarin gwiwa… kuma da alama ƴan Republican sun nuna jajircewa," in ji shi.
Trump ya ce an karrama shi don ganin cewa layukan zaɓen sun yi tsayi sosai. "Mun dawo cikin daren jiya," in ji shi, yayin da yake magana kan gangamin yaƙin neman zabensa a Michigan a daren jiya. "Na ji cewa muna taka rawar gani."
Mataimakiyar shugaban ƙasa Harris ta shaida wa manema labarai cewa ta riga ta kaɗa ƙuri'arta ta gidan waya tun makon da ya gabata.
Ana ci gaba da kaɗa ƙuri'a a duka jihohi bakwai da ba su da tabbas a zaɓen shugaban ƙasa, amma har yanzu babu wata tazarar kirki a sakamakon ƙuri'un jin ra'ayin jama'a da ake ci gaba da gudanarwa a waɗannan jihohin.
Sai dai ƙuri’u na nuna cewa Harris ce ke kan gaba a babbar jihar Pennsylvania, inda a baya ƴantakarar suka yi kunnen doki.
Masana na yi wa jihar kallon mai matuƙar muhimmanci a wannan zaɓen, kuma Harris da Trump sun sadaukar da lokaci mai yawa wurin gudanar da yaƙin neman zaɓe a sassan jihar.
Har yanzu Trump yana kan gaba da 'yar tazara a Nevada, da Georgia, da North Carolina, da kuma Arizona, inda ita ma Harris ta ba shi 'yar tazara a jihohin Winsconsin, da Michigan.
Yayin da ake ci gaba da kaɗa ƙuri'a a rumfunan zaɓe daban-daban a faɗin Amurka, kallo ya koma kan jihohin da ake sa ran za su ne za su yi muhimmin tasiri a sakamakon zaɓen.
A zaɓen shugaban ƙasa, jihohin da ke da mutane da yawa sun fi yawan ƙuri'un wakilan masu zaɓe.
A duk faɗin Amurka akwai jimillar ƙuri'un wakilan masu zaɓe 538. Ɗan takara na buƙatar ya lashe ƙuri'u 270 ko fiye da haka kafin ya iya lashe zaɓen baki ɗaya.
Jihohin bakwai da ake ganin su ne ke da matuƙar mahimmanci a wannan zaɓen na da ƙuri'u 93 na wakilan masu zaɓe a tsakanin su.